NDC ta kafa kwamitin sulhu bayan ɓarkewar rikicin cikin gida
Jam’iyyar NDC ta sanar da ɗaukar wasu muhimman matakai da nufin karfafa dimokuradiyya a cikin jam’iyyar da tabbatar da ladabtarwa da kuma gina ta a matsayin babbar kafa ta siyasa gabanin zaɓuka masu zuwa.
An cimma waɗannan matsaya ne a taro na biyu na kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar, kamar yadda take ƙunshe cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Osa Director, ya fitar a ranar Asabar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa duk gwamnatocin da aka zaɓa karkashin tutarta za su riƙa tuntubar tsare-tsaren jam’iyya kafin yanke manyan shawarwari na manufofi da naɗa muƙamai da aiwatar da shirye-shirye, ban da naɗe-naɗen ma’aikatan ofisoshin masu riƙe da muƙamai.
NDC ta jaddada cewa jam’iyyar ta fi fifita muradun daidaikun mutane, tana mai kira ga mambobinta da su daidaita burinsu da ayyukansu da manufofi da akidar jam’iyyar.