Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 30/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Rufe mashigar Hormuz ya maƙure tattalin arziƙin duniya - Guteres

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce rufe mashigar Hormuz na taɗiye tattalin arzikin duniya.

    Antonio Guterres kenan ya ce a gaggauta buɗe masigar Hormuz, a bada dama ga dukkanin jiragen ruwa su wuce, a bar tattalin arzikin duniya ya numfasa.

    Ya ce ko a yanzu aka janye takunkumin, harkar samar da kayayyaki za ta dauki watanni kafin ta farfado, lamarin da zai haifar da raguwar samar da kayayyaki da kuma tashin farashi.

    Ya bayyana hakan ne yayin da dakarun juyin juya halin Iran sukai gargadi cewa, za su kaddamar da zafafan hare-hare masu dogon zango kan Amurka, idan Washington ta sake kai wa Iran hari.

    Tun bayan da rahotannin suka ce Shugaba Donald Trump na samun bayanai kan yiwuwar ɗaukar matakin soja a kan Iran, farashin ɗanyan mai yayi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya.

  2. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutane da dama a Lebanon

    Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla mutum 9, ciki har da yara 2 da mata 5, sun mutu a hare-haren da Israel ta kai kudancin ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan sojojin Israel sun fitar da sabon gargaɗin ficewa ga mazauna garuruwa 9 na yankin kudanci ƙasar da Israel ta mamaye.

    A sabon jawabin sa da yayi, Shugaban Lebanon, Joseph Aoun ya yi Allah-wadai da abin da ya kira ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta daga Isra'ila, yana mai kira ga kasashen duniya da su matsa lamba a daina da kai hare-hare kan fararen hula da jami’an agaji.

    Israel ta ce hare-haren nata na da nufin kawar da barazanar Hezbollah.

  3. 'Za mu ƙaddamar da zafafan hare-hare kan Amurka idan ta ƙara kai mana hari'

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundinar juyin juya halin Iran ta yi gargaɗin cewa za su ƙaddamar da zafafan hare-hare masu dogon zango kan Amurka, idan Washington ta sake kai wa Iran hari.

    Rahotannin sun ce ana gabatar wa Shugaban Amurka Donald Trump bayani, kan yiwuwar ɗaukar matakin soji a kan Iran, wani batu da ya haddasa gagarumin tashin farashin mai.

    Wakilin BBC ya ce ana amfani da Ɗanyen Mai da dangoginsa a masana'antu da dama da kuma fannin sufuri, lamarin da ya zama gagarumar barazana ga al'umma.

    Shi ma Man nau'in Brent yayi gagarumin tashin da ba'a taɓa gani ba cikin shekaru 4, inda ya kai dala 126 kan kowace ganga kafin daga bisani ya sauko.

    A wata sanarwa da aka fitar da sunan jagoran addini Iran Mojtaba Khamenei, ta yi ƙarin haske kan sabon tsarin tafiyar da mashigar Hormuz.

  4. Shugaban matasan ADC ɓangaren Nafiu Bala ya yi murabus

    Sultan Ahmed Bello

    Asalin hoton, @sultanbellojr/X

    Shugaban matasan jam'iyyar adawa ta ADC ɓangaren Nafiu Bala Gombe, Hon. Sultan Ahmed Bello ya sanar da ajiye muƙaminsa.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Hon. Sultan ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda yake fuskantar barazana da kuma "shan tsinuwa" daga wajenal'umma saboda abin da ya ke faruwa da kuma goyon bayan Nafiu Bala da ya ke yi.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

    Sai dai matashin ya tabbatar wa BBC cewa ba wannan ne dalilin da ya sa ya ɗauki matakin ba kamar yadda wasu ke tunani.

    "Abin da ya tayar min da hankali shi ne yadda ake min munanan addu'o'i da fatan in yi ƙarshe irin na fir'auna," in ji shi.

    Nafiu Bala Gombe dai shi ne mutumin da ake rikicin shugabancin jam'iyyar hamayya ta ADC da shi a Najeriya.

  5. Kotun Ƙoli ta tabbatar da shugabancin David Mark na ADC

    ADC

    Asalin hoton, Muhammeed M Abdulhameed/FB

    Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

    A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari'a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da ake yi.

    Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake da cire sunan shugabancin ADC ɓangaren David Mark daga shafin INEC.

  6. Tinubu ya naɗa sabon ministan Lantarki na Najeriya

    Tinubu

    Asalin hoton, @aonanuga1956/X

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mr Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin sabon ministan wutar lantarkin ƙasar.

    A sanarwar da kakakin shugaban Bayo Onanuga ya fitar, ya ce an tura sunan Tegbe zuwa majalisar dattawa domin amincewa kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada.

    Wannan na zuwa ne bayan murabus ɗin da Adebayo Adelabu ya yi daga muƙamin domin shiga takara a zaɓen 2027.

  7. Abin da muka sani game da mutumin da ake zargi da kai hari da wuƙa a Landan

    L

    Asalin hoton, Supplied

    An kama wani mutum mai kimanin shekaru 45 bisa zargin kisan kai bayan da ya soki wasu Yahudawa biyu da wuƙa a Golders Green da ke birnin Landan a ranar Laraba.

    Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Shabana Mahmood ta shaida wa BBC a safiyar Alhamis cewa, wanda ake zargin cikakken ɗan ƙasa ne a Birtaniya amma haifaffen ƙasar Somalia, inda ya shiga ƙasar tun yana ƙarami ta halastacciyar hanya.

    Kwamishin ƴansandan birnin Mark Rowley, ya ce mutumin yana da matsalar taɓin hankali kuma yana da son rikici.

    ƴansandan sun kuma ce suna binciken wani rikici da ya faru a kusa da yankin da ya kai harin a kudu maso gabashin Landan a ranar Laraba, inda ake zargin mutumin da tayar da hatsaniyar.

    BBC ta gano cewa sunan mutumin Essa Suleiman, daga kudu maso gabashin Landan.

    Mr. Rowley ya ce bayan kama mutumin, jami'ai sun yi zargin yana ɗauke da wasu abubuwan fashewa a jikinsa, inda suka yi amfani da na'urori wajen kashe su duk da ya ci gaba da farmakar su da wuƙa.

    Ana ci gaba da tsare mutumin wajen ƴansanda bayan yi masa magani a asibiti.

  8. Isra'ila ta kama jiragen ruwa fiye da 50 ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza

    B

    Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

    Rundunar sojin ruwan Isra'ila ta kama wasu jiragen ruwa fiye da 50 ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza, a gaɓar kogin Kireet dake Girka.

    Ma’aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce an kama kusan ƴan fafutuka 175, a kan jiragen ruwan sama da 20.

    Masu shirya tawagar jiragen ruwan sun yi Allah-wadai da matakin, inda suka kira abin da fashin teku, kuma jiragen na nesa da Gaza da daruruwan kilomitoci, da dakarun Isra'ila su kai wa ƙawanya.

    Wani mai magana da yawun gwamnatin Girka ya ce ba a tuntuɓe su ba kafin gudanar da samamen.

  9. Kotun ƙoli ta kori ƙarar PDP ɓangaren Tanimu Turaki

    Tanimu Turaki

    Asalin hoton, PDP/FACEBOOK

    Kotun ƙolin Najeriya ta kori ƙarar da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki ya shigar, inda yake ƙalubalantar matakin rushe taron zaɓen shugabanninsu da aka yi a Ibadan.

    Yayin da yake sanar da matsayar alƙalan, mai shari'a Stepehen Adah ya bayyana cewa taron da suka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa'a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari'a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron jam'iyyar.

    Kotun ƙolin ta kuma soki ɓangaren Turaki game da zuwa kotun da ba ta da hurumi, a madadin zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

    Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar da ta yanke na haramta taron PDPn a jihar Oyo.

    Uku daga cikin alƙalai biyar ne suka amince da wannan hukuncin.

  10. Majalisar Amurka ta buƙaci a daina tallafa wa Najeriya har sai an daina kashe kiristoci

    Riley Moore

    Asalin hoton, RileyMoore/House.gov

    Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dokokin Amurka ya gabatar da wani ƙudirin doka da ya gindaya wasu sharuɗɗan dakatar da tallafin kuɗi ga Najeriya har sai gwamnatin ƙasar ta magance matsalar hare-hare a sassan kasar.

    Ƙudirin ya mayar da hankali ne kan tallafin da Amurka ke bayarwa don tsaron ƙasa, da shirye-shirye masu alaƙa na kasafin kuɗin shekara da zai ƙare 30 ga watan Satumba, 2027.

    Da ya ke magana a kan ƙudirin a shafinsa na X, ɗanmajalisa Riley Moore ya ce: "Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ta kashe miliyoyi wajen roƙon majalisar, amma ta kasa magance matasalar kashe kiristoci a ƙasar".

    Moore ya ƙara da cewa ba za su rufe idanunsu suna kallo "ana yi wa ƴan'uwansu kiristoci kisan ƙare dangi ba."

    Ƙudirin da aka gabatar ya tanadi cewa aƙalla kashi 15 na dala biliyan 6.89 da aka ware, za su tafi ne wajen taimaka wa tsaro a Afirka, inda da aka ware dala miliyan 870 domin yaƙi da ta'addanci.

    A ƙudirin da aka gabatar, ya bayyana cewa ba za a iya fitar da kashi 50 na kudaden da aka ware wa Najeriya ba har sai sakataren harkokin wajen ƙasar ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya "ta ɗauki ƙwararan matakai na hana tashe-tashen hankula da kuma daukar matakin hukunta masu laifi".

    Sai dai ba a bayyana ainihin kuɗaden da aka ware wa Najeriya a cikin ƙudirin dokar ba.

  11. Hukumomin lafiya a Gaza sun ce an kashe mutum 2 da jikkata 8 cikin awa 24

    Hukumomin lafiyar Gaza da ke da alaƙa da Hamas, sun ce an kashe mutum 2 da jikkata wasu 8 a hare-haren da Isra'ila ta kai cikin awanni 24.

    Gidan Talabijin na Al Jazeera ya ruwaito cewa daga watan Oktobar bara da aka fara tsagaita buɗe wuta a Gaza, an kashe mutum 824 da jikkata 2,316.

    Hukumomin lafiyar a Gaza sun ce an kashe mutum 72,601 da jikkata 172,419 tun a watan Oktobar 2023 da aka fara yaƙi a yankin.

  12. Ƙungiyar JNIM ta yi barazanar toshe hanyoyin shiga Bamako

    Shugaban mulkin soja na ƙasar Mali Assimi Goita

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban mulkin soja na ƙasar Mali Assimi Goita

    Ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da Al Qaeda ta fara wani abin da ta bayyana a matsayin toshe hanyoyin shiga Bamako babban birnin kasar Mali baki ɗaya.

    JNIM ta yi barazanar toshe duk wata hanya ta shiga birnin, bayan hare-haren da ta kai babban birnin da ma wasu sassan ƙasar a ƙarshen mako.

    Matakin dai wani ƙarin barazana ne ga gwamnatin mulkin sojan kasar ta Mali, wadda ta yi iƙirarin ƙarfafa tsaro, bayan shafe kwanaki ana tashe tashen hankula, inda har aka kashe ministan tsaron ƙasar.

    JNIM ita ce babbar ƙungiyar da ke da alhakin yawaitar hare-haren da ke ci gaba da mamaye wasu ƙasashen yammacin Afirka, musamman Burkina Faso, Mali da Nijar.

  13. Mutum 9 sun mutu a wasu hare-haren Isra'ila kan Lebanon

    Lebanon

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe aƙalla mutane tara a wasu hare-haren da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon a safiyar yau Alhamis.

    A cewar kamfanin dillancin labaran Lebanon, harin da Isra'ila ta kai a yankin Jabshit, ya lalata wani gini, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku da jikkata 7.

    A birnin Toul ma, wani hari da ta kai kan wasu gidaje ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu tare da jikkata wasu 6, sai a birnin Haruf, inda aka kashe mutane biyu a wani harin da ya lalata wani gida.

  14. Rundunar ƴansandan Najeriya ta kori jami'inta da ya kashe matashi a Delta

    NIGERIA POLICE

    Asalin hoton, NIGERIA POLICE

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta kori wani jami'inta da ke da hannu a kisan wani matashi Mene Ogidi a yankin Effurun da ke jihar Delta a Kudu Maso Kudancin ƙasar.

    Rundunar ƴansandan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ta ce an sallami jami'in mai suna ASP Nuhu Usman bayan kammala bincikenta kamar yadda babban sufetan hukumar Tunji Disu ya ba da umarni.

    A wata sanarwa a ranar Laraba mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DCP Anthony Placid, ta ce an kama Ogidi mai shekaru 28 ne a lokacin da yake yunkurin aika wani saƙo da ake zargin bindiga ce da harsashi hudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar shi.

    Hukumar ta ce bayan samun waɗannan rahotannin ne, aka dauƙi matakin mayar da binciken zuwa hedikwatarta da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    "Bincike ya nuna cewa cewa, jami'i ASP Nuhu Usman ya aikata laifin da ya ci karo da dokokin hukumar na 237 da kuma amfani da makami ba bisa ƙa'ida ba," in ji sanarwar.

    "Abin da ya aikata, rashin ƙwarewa ne da kuma cin amanar rantsuwar da ya yi na kare rayuwar al'umma da dokokin ƙasa".

    Rundunar ta ƙara da cewa bayan kammala matakan da suka dace, za a miƙa jami’an da abin ya shafa ga hukumomin shari’a da suka dace domin gurfanar da su.

  15. Tinubu ya ɗaga darajar Bianca Ojukwu zuwa ministar harkokin wajen Najeriya

    Bianca Ojukwu

    Asalin hoton, Bianca Ojukwu/Insta

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin ministar harkokin wajen ƙasar, bayan murabus ɗin Yusuf Tuggar, wanda ya ajiye mukaminsa domin shiga takara a zaɓen 2027.

    Bianca ita ce ƙaramar minista a ma'aikatar kafin wannan sabon matsayin.

    Kamar yadda wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ta bayyana, an kuma naɗa Sola Enikanolaiye a matsayin ƙaramin minista a ma'aikatar, inda za a jira amicewar majalisar dattawa.

    Kafin a naɗa shi muƙamin, Enikanolaiye wanda haifaffen jihar Kogi ne, shi ne babban mataimaki na musamman ga shugaba Tinubu kan harkokin ƙasashen waje.

  16. Yau kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

    ADC

    Asalin hoton, ADC

    Nan gaba a yau Alhamis ne ake sa ran kotun ƙolin kasar za ta yanke hukunci kan shari'ar rikicin shugabancin jam'iyyar hamayya ta ADC.

    Hukuncin dai zai fayyace makomar jam'iyyar musamman hamayyar shugabanci tsakanin bangaren Sanata David Mark da kuma bangaren Nafiu Bala Gombe.

    Tun da fari dai jam'iyyar hamayya ta ADC ta fara neman a gaggauta yanke hukunci kan saɓanin da take ciki kan sahihancin shugabancinta, lamarin da za a iya cewa ya tsayar da harkokin jam'iyyar cak.

    Ana dai ganin jam'iyyar ADC ce babbar wadda za ta yi hamayya da jam'iyya mai mulki ta APC, musamman ganin irin manyan ƴansiyasar da ke cikin jam'iyyar da kuma tarihin su.

    Wani abu da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne yadda ADC da PDP da wasu jam'iyyun hamayya suka haɗu, suka tattauna tare da ayyana ƙudurinsu na tsayar da ɗantakara ɗaya da zai fafata da Bola Tinubu a zaɓen na 2027.

    Sai dai ADC na ta fama da rikicin gida, inda yanzu haka ake Kotun Ƙoli, inda ake sauraron hukuncin da za ta yanke.

  17. Farashin ɗanyen mai ya yi tashin da bai taɓa yi tun daga 2022

    Fetur

    Asalin hoton, Costfoto/NurPhoto via Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya ci gaba da tashin gwauron zabi ba ƙaƙƙautawa - inda ya kai matakin da bai taɓa kaiwa ba na ƙoli- tun bayan da aka fara yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran a ƙarshen watan Fabarairu.

    Samfurin Brent - wanda shi ke zaman ma'auni ya ɗan haura dala 126 a kan duk ganga ɗaya, yayin da ake nuna damuwa kan tsawon lokacin da yakin zai ƙare.

    Wannan ya biyo bayan bayanan da aka samu ne cewa Shugaba Trump na tattaunawa da shugabannin harkar makamashi, kan yuwuwar tsawaita, rufe tasoshin jiragen ruwa na Iran da zirga-zirgar jiragen - tsawon watanni.

    Iran ta hana wucewar jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz - wadda ta nan ne kusan kashi daya bisa biyar na yawan mai da iskar gas da ake amfani da su a duniya ke bi.

  18. Amurka na tuhumar gwamna a Mexico da safarar miyagun ƙwayoyi

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce ta tuhumi gwamnan jihar Sinaloa na kasar Mexico, mai ci - da laifin zargin hada baki da shugabannin kungiyar Sinaloa mai safarar miyagun kwayoyi, domin safarar tarin kwayoyi.

    Baya ga Rúben Rocha Moya, akwai kuma wasu jami'an na Mexico su tara - wadanda suke rike da mukamai a yanzu da kuma wadanda suka sauka, da su ma aka tuhuma.

    Wakilin BBC ya ce a tsakiyar wannan tuhuma ta gwamnatin Trump, shi ne zargin cewa Mista Rocha na amfani da wani bangare da kungiyar ta Sinaloa domin a zabe shi Wannan, wata babbar tuhuma ce da Amurka ta yi a kan safarar miyagun kwayoyi, wadda za ta iya kara tsamin dangantaka tsakaninta da Mexico.

    Shi dai gwamnan da wannan tuhuma ta shafa - Mr Rocha,wanda dan jam'iyyar Shugaba Claudia Sheinbaum ne, Morena, ya musanta tuhumar.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Juma'a. Da fatan za mu samu albarkacin da ke cikin wannan rana. Allah ya sa hakan.

    Kamar kullum yau ma mun sake dawo muku da shafin BBC Hausa na kai tsaye inda muke kawo muku labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a yaƙin Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.