Muna ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bunguɗu - Sojojin Najeriya
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce jami'anta na bibiya tare da yunƙurin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, bayan wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da shi daga gidansa, sannan ta ƙara da cewa an ceto wasu daga cikin iyalansa.
A cewar rundunar, maharan sun yi nasarar yin awon gaba da shugaban karamar hukumar bayan sun yi galaba a kan jami'an ƴansanda da masu sintiri da ke ba shi kariya.
Sanarwar ta ce bayan sojoji sun ji harbe-harbe ne suka garzaya wurin tare da bin sawun maharan, inda suka yi musayar wuta.
Rundunar ta ce matsin lambar da dakarunta suka yi ya sa maharan ne ya sa suka bar mutum biyar daga cikin iyalan shugaban ƙaramar hukumar, waɗanda suka haɗa da 'ya'yansa biyu da mahaifiyarsa da matarsa da wani ɗan'uwansa, kafin su tsere da shi cikin daji.
Rundunar ta tabbatar da mutuwar jami'an tsaronsa uku, ciki har da ƴansanda biyu da dan sintiri guda daya. Haka kuma wani ɗan babu ruwan ya rasu, sannan wani Alhaji Bello Umar, ya ji raunuka.
Rundunar ta ce ta ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa tare da ƴansanda da DSS da ƴan sa-kai domin gano inda maharan suke tare da kuɓutar da shugaban ƙaramar hukumar cikin ƙoshin lafiya.