Wane tasiri sababbin harajin Trump za su yi ga tattalin arziƙin Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Amurka ta ƙaƙaba sabbin harajin kan manyan ƙasashe 60 da take hulɗa da su a fannin kasuwanci, bayan wa'adin wani harajin wucin-gadi na duniya ya ƙare.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Ƙolin Amurka ta yanke hukunci a watan Fabrairu cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump ba ta bi ƙa'ida ba wajen ƙaƙaba wasu haraje da ta gabatar a baya.

Sabbin harajin sun kai tsakanin kashi 10 zuwa 12.5 cikin ɗari, kuma suna shafar mafi yawan kayayyakin da Amurka ke shigowa da su daga ƙasashen waje. Daga cikin ƙasashen da abin ya shafa akwai Birtaniya, China, Tarayyar Turai (EU), Canada, Japan da Indiya.

Wannan mataki shi ne sabon salo na yaƙin kasuwanci da Shugaba Donald Trump, wanda shugaban ya sake farfaɗowa bayan komawarsa mulki a bara.

Kotun Ƙolin Amurka ta yanke hukunci a farkon shekarar nan cewa wasu daga cikin harajin da gwamnatin Trump ta ƙaƙaba a ƙarƙashin dokokin cikin gaggawa ba su yi daidai da doka ba.

A watan da ya gabata ne Fadar White House ta gabatar da shawarar ƙaƙaba harajin kashi 10 zuwa 12.5 cikin ɗari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashe da dama, bisa zargin cewa ba sa yin isasshen ƙoƙari wajen hana amfani da aikin tilas wajen samar da kayayyaki.

A ranar Alhamis, Wakilin Kasuwancin Amurka, Jamieson Greer, wanda ya ce yana aiwatar da umarnin Shugaba Trump, ya sanar da cewa sabbin harajin za su fara aiki nan take.

Me hakan ke nufi?

Greer ya ce: "Matakin yau zai taimaka wajen gyara abin da muke gani a matsayin take haƙƙin ɗan Adam da kuma wata hanyar kasuwanci da ke cutar da gasa, domin inganta walwalar ma'aikata a ko'ina."

Ya ce an ɗauki matakin ne bisa Sashe na 301 na Dokar Kasuwanci ta shekarar 1974, wadda ke bai wa Amurka damar ɗaukar matakan kariya idan ta yi zargin cewa wasu ƙasashe na yin kasuwancin da ke cutar da tattalin arzikinta.

A farkon makon nan kuma gwamnatin Trump ta yi amfani da wata doka dabam, Sashe na 338 na Dokar Haraji ta 1930, wajen ƙaƙaba harajin kashi 50 cikin ɗari kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Canada.

Ofishin Wakilin Kasuwancin Amurka ya ce an ɗora sabbin harajin ne kan ƙasashen da ba su kafa ko aiwatar da dokokin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole ko aikin wahala ba.

A cewarsa, sabbin harajin sun shafi manyan abokan kasuwancin Amurka 60, waɗanda ke wakiltar kusan kashi 99.4 cikin ɗari na duk kayayyakin da Amurka ke shigowa da su daga ƙasashen waje.

Ofishin ya kuma ce Shugaba Trump ya mayar da hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas wani muhimmin sharadi a yarjejeniyoyin kasuwanci da Amurka ke yi da sauran ƙasashe.

Ya ce zuwa yanzu ƙasashe 10 sun amince su kafa irin wannan doka a yarjejeniyoyinsu da Amurka, yayin da wasu kuma suka fara aiwatar da dokar bayan binciken da Amurka ta gudanar.

Saboda haka, ƙasashen da suka amince da kafa da kuma aiwatar da dokar za su fuskanci harajin kashi 10 cikin ɗari, yayin da waɗanda ba su yi hakan ba za su biya kashi 12.5 cikin ɗari.

Greer ya ce yana farin ciki da yadda wasu ƙasashe suka yi gaggawar ɗaukar waɗannan matakai, kuma yana fatan za su tabbatar da aiwatar da dokokin yadda ya kamata.

Masaniyar manufofin kasuwanci daga Hinrich Foundation, Deborah Elms, ta ce wannan mataki ya nuna gwamnatin Trump ta kuduri aniyar ci gaba da amfani da haraji a matsayin makamin siyasar kasuwanci.

Ta kuma ce da wuya ƙasashen da abin ya shafa su iya tabbatar wa Amurka cewa suna da isassun matakan hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas.

Ita kuwa Wendy Cutler daga Asia Society Policy Institute ta ce sabbin harajin za su ƙara tsadar kayayyaki ga kamfanoni da masu saye, ko da yake hakan na iya raguwa saboda akwai wasu kayayyaki da aka ware daga harajin.

Ta ƙara da cewa yawancin ƙasashen da abin ya shafa za su yi takaici, kuma mai yiwuwa su ƙara neman hanyoyin rage dogaro da kasuwar Amurka ta hanyar ƙulla sabbin yarjejeniyoyin kasuwanci da wasu ƙasashe.

Shugaban British Chambers of Commerce (BCC), William Bain, ya shaida wa shirin Today na BBC cewa sabbin harajin sun sa Birtaniya ta rasa wata fa'ida da take da ita idan aka kwatanta da Tarayyar Turai.

Shin zai shafi Najeriya?

Shuaibu Idris mai sharhi ne kan harkokin tattalin arziki da al'amuran yau da kullum a Najeriya, ya ce yana tunanin babu wata babbar illa matakin zai yi ga tattalin arzikin Najeriya ba.

Masanin harkokin tattalin arzikin ya ce irin takunkuman da Donald Trump ke ƙaƙabawa "matsaloli, kuma nan gaba al'ummar duniya za su ƙara fahimtar illolin hakan."

Shuaibu Idris ya ƙara da cewa akwai yarjejeniyar kasuwanci ta duniya da ƙasashe suka shiga domin inganta harkokin cinikayya, amma ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce Trump na mata karan-tsaye.

"Akwai yarjejeniyar da ake kira "Genaral trade and tariffs agreement wato GTTA da ƙasashen duniya suka tsara tare da rattaba hannu a tsakaninsu. Wannan yarjejeniyar ce ta haifar da assasa Hukumar cinikayya ta duniya wato WT."

Masanin ya ce ƙasashen duniya ciki har da Amurka ne suka amince da amfani da tsarin domi tsara yadda za a riga gudanar da kasuwanci a duniya.

Sai dai ya ce abin takaici, "a koma gefe ana ƙaƙaaba wasu takunkuman da suka saɓa da doka. Idan akwai matsala kamata ya yi a koma zauren taro a tattauna," in ji shi.

A game da yadda lamarin zai shafi Najeriya, Shuaibu Idris ya ce dole ba ne lamarin ya shafi Najeriya kai-tsaye.

"Ba kasafai muke fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba. A Najeriya kayayyakin da muke shigarwa, kusan ita ce za ta wahala ba mu ba. Misali idan ta saya ɗanyen mai ko ikar gas, idan ta saka wannan harajin saboda man ya yi tsada, su ƴan Amurka ɗin ne za su wahala."

Ya ƙara da cewa idan ma kayayyakin sun yi tsada, sai aka samu ragowar yadda ake saya a Amurka, Najeriya za ta iya kai kayayyakinta wasu ƙasashen saboda ana buƙata.

A masa jawabin, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, mai sharhi kan harkokin tattalin arziki ne ya ce matakin zai sa kayayyakin ake fitarwa daga Najeriya su tsada. "Hakan kuma zai sa masu saya su duba wasu kasashen masu sauki."

Ya ce matakin zai yi illa ga tattalin arzikin Najeriya saboda a cewarsa zai rage yawan dalar Amurka da ke shigowa kasar, "kuma tattalin arzikin Najeriya ya dogara sosai da dalar Amurka."

Ya kara da cewa hakan zai sa kayayyakin cikin Najeriya su kara tsada, har ya shafi masu zuba hannun jaro.

Daga cikin kayayyakin Najeriya da ake fitarwa zuwa Amurka akwai:

  • Ɗanyen mai
  • Iskar gas
  • Coacoa
  • Gyaɗar cashew