Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne waɗanda aka kama da zargin kitsa sace ɗaliban Oyo?
Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutum da ta ce tan zargin su ne suka kitsa tare da jagorantar ƙaddamar da hari a makarantar jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar tare da sace ɗalibai.
A makon jiya ne rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto dukkan ɗalibai da malamai su 44 da aka sace kimanin wata biyu da suka gabata daga makarantu a jihar Oyo da ke, sannan ta ce an kama wasu daga cikin masu garkuwar.
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin sojojinta sun rasa rayukansu yayin gudanar da aikin ceton.
Sace ɗaliban na Oyo ya matuƙar ɗaukar hankali, inda har fitaccen mawaƙin Najeriya Davido ya isar da batun zuwa duniya bayan ya taka rawa a raƙashewar share fagen Gasar Kofin Duniya sanye da riga mai ɗauke da sunan ɗaliban.
Matakin nasa ne ya haifar da zazzafar muhawara tsakaninsa da fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara a kafofin sadarawa.
Su wane ne ake zargi?
Waɗanda hukumomin suka kama tare da zarginsu da hannu a sace ɗaliban makarantun su ne:
- Abu Khalifa/Abu Khalid
- Bin Musa
- Abu Itisar
Dukanzu mazauna ƙaramar hukumar Suleja ta Jihar Neja ne, kuma ana zarginsu da cewa sun haɗa baki da wasu mutum ukun daban a tsakanin watan Janairu da Mayu na shekarar 2026 domin yin garkuwa da ɗalibai da malamai a Jihar Oyo, wanda hukumomi suka ce ya saɓa wa Sashe na 26(1) na Dokar Hana da Takaita Ta'addanci ta shekarar 2022.
Haka kuma ana zargin sun taimaka wajen sace ɗaliban da malamai, sannan suka ɓoye bayanai game da waɗanda ake zargin su ne suka shirya harin duk da cewa suna da masaniya a kai. An ce hakan ya saɓa wa Sashe na 26(2) da Sashe na 16(1) na dokar.
Bugu da ƙari, ƙarar ta ce a ranar 2 ga Yuni, 2026, mutanen ukun sun bayyana kansu a matsayin mambobin Darul Salam, wata ƙungiya da ake zargin tana da alaƙa da Ansaru (Jama'atu Ansarul Musulmina Fi Biladis Sudan), wadda gwamnatin Najeriya ta haramta saboda ayyukan ta'addanci. Ana zargin hakan ya saɓa wa Sashe na 25(1) na Dokar Ta'addanci.
A wasu tuhume-tuhume na daban, ana zargin ɗaya daga cikin su da horas da ƴanta'adda ta hanyar buɗe zauren WhatsApp mai suna "The Oneness of Allah is the Foundation of Peace", da kuma tunzura mambobinta su aikata ayyukan ta'addanci. An ce waɗannan laifuka sun saɓa wa Sashe na 15 da Sashe na 2(2)(g) na Dokar Ta'addanci ta 2022, da kuma Sashe na 18 na Dokar Laifukan Yanar Gizo (Cybercrime Act) ta shekarar 2015.
Tuhuma ta goma kuma ta zargi ɗaya daga ciki da haƙar zinari ba tare da izini ba a ramukan yankin Chaza da ke ƙaramar hukumar Suleja tsakanin shekarun 2024 da 2026.
Yadda aka sace ɗaliban
A ranar 15 ga Mayun 2026 ce wasu mahara masu ɗauke da makamai suka kai hari makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Oriire a jihar Oyo, inda suka yi garkuwa da ɗalibai, malamai da ƙaramin yaro.
Maharan sun isa yankin ne a kan babura, inda suka kai hare-hare lokaci guda kan makarantu uku a Yawota da Ahoro-Esinele.
Makarantun da aka kai wa hari su ne
- Baptist Nursery and Primary School, Yawota;
- Community High School, Ahoro-Esinele;
- L.A. Primary School, Ahoro-Esinele
Sun isa makarantun ne ana tsaka da karatu, inda suka riƙa harbe-harbe kafin su kutsa cikin ajujuwa. Wani malami ya shaida wa BBC cewa yara sun riga sun zauna a cikin aji lokacin da harin ya fara, kuma maharan suka tafi da su ba tare da wata turjiya ba.
Masu garkuwar sun sace yara ƙanana har masu shekaru biyu, tare da malamai da kuma wani ƙaramin yaro wanda yake tare da ɗaya daga cikin malaman da aka sace.
A yayin harin, mutane biyu sun mutu: wani mutum da aka harbe bayan maharan sun yi zargin yana binsu, da kuma wani malami da aka kashe nan take a wurin harin.
Sace ɗalibai daga makarantu ya fara zama ruwan-dare a Najeriya ne tun bayan sace ƴan matan makarantar Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014, inda aka sace ɗalibai mata kusan 276.
Lamarin ya faru ne ƙasa da shekara guda bayan wasu manyan hare-haren sace ɗalibai, ciki har da sace kusan yara 100 daga wata makarantar Katolika a jihar Neja a ƙarshen shekarar 2025, da kuma sace ƴan mata 25 daga makarantar mata ta Government Girls Comprehensive Secondary School a jihar Kebbi.