ICC ta tsige mai gabatar da ƙara da jagoranci bayar da sammacin kama Netanyahu

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen da ke mambobin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) sun kaɗa kuri'ar amincewa da tsige babban mai gabatar da ƙara na kotun, Karim Khan.
Ana zargin lauyan ɗan Birtaniya mai shekara 56 da dabi'ar da ba ta dace ba - a kan wata karamar ma'aikaciyar kotun - zargin da ya musanta.
Wakiliyar BBC ta ce wannan zargi ya fara bayyana ne a shekara ta 2024, cewa ya ci zarafi ta lalata na karamar abokiyar aikinsa.
Karim Khan ya jagoranci kotun tsawon shekara biyar, wanda a cikin wannan lokaci, kotun ta bayar da sammacin kama mutane da dama da suka haɗa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da wasu jami'an ƙungiyar Hamas, da Shugaban Rasha Vladimir Putin, da tsohon shugaban Philippines Rodrigo Duterte.
Tsige Khan na zuwa ne a wani lokaci da kotun ta duniya ke fuskantar ƙalubale, sakamakon matakan Amurka na neman raunana ikonta.




















