Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Litinin 5 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. An bayar ba belin malamar jinyar Ghana da ake zargi da alaƙa da wani mai sukar gwamnati

    An bada belin malamar jinyar nan ƴar Ghana bayan shafe makonni uku a kulle, kan zargin alaƙa da wani shafin sada zumunta na TikTok da ya yi fice wajen sukar shugaba Jihn Dramani Mahama da maidakinsa Lordina Mahama.

    Malamar jinyar mai shekara 40 ta musanta zargin da ake ma ta na hannu a kan yada labaran ƙarya kan shugaban ƙasar da maidakinsa ba.

    Salomey Awiti Baffoe ta shafe makonni 3 a daure, amma yanzu an ba da belin ta kan kudi dala 8,500 sannan za ta dinga zuwa ofishin 'ƴansanda a duk bayan mako biyu.

    Masu shigar da ƙara sun zarge ta da haɗa kai da mai shafin sada zumuntar da ba a san mamallakinsa ba baya ga sunan ''Ghana Jallof'', da ya yi ƙaurin suna a sukar gwamnati maimulkin ƙasar, tare da bai wa wasu hore su ma su na zukar gwamnati a mabanbantan shafukan sada zumunta.

    A watan da ya gabata ne jami'an tsaro suka cafke ta, ko da ya ke daga bisani sun musanta tsare ta. Masu sukar lamari sun yi gargadi kan cin zarafin ƴan ƙasa da take hakkinsu da ƴancin fadin albarkacin baki, musamman ashafukan sada zumunta.

    Wasu na ganin bai kamata hakan ta faru ba, a daidai lokacin da shugaba Mahama ke kiraye-kiraye 'yan ƙasa su guji yaɗa kalaman ƙiyayya musamman a shafukan sada zumunta.

  2. Babu hujjar cewa Iran na da hannu a lamarin jirgin Flydubai - Amurka

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce babu wata hujja da ke nuna hannun Iran a lamarin jirgin Flydubai da matuƙansa suka yi faɗa a sararin samaniya.

    JD Vance ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai kafin ya tashi zuwa jihar Alaska.

    A makon da ya gabata ne wani jirgin saman Emirates da ya taso daga Dubai zuwa Tel Aviv ya aika da saƙon gaggawa daga sararin samaniyar Jordan kusan sa'o'i biyu bayan tashinsa.

    Daga nan jirgin ya sauya hanya kafin daga bisani ya sauka a filin jirgin sama na Tabuk da ke Saudiyya.

    Tun da farko, Babban Lauyan Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ya ce mataimakin matuƙin jirgin Flydubai ya yi niyyar aikata abin da ya kira "aikin ta'addanci."

    Wannan ne karon farko da hukumomin UAE suka bayyana lamarin a hukumance a matsayin "ta'addanci.''

  3. Duka mutane 32 da ke cikin jirgin sojin Najeriya da ya faɗi sun mutu

    Jirgin sojin Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan fasinjoji da ma'aikata 7 da suka rasu sanadin hatsarin jirgin sojin saman ƙasar a jihar Ondo da ke kudu maso gabashinƙasar.

    Hukumomi sun ce Jirgin sojin sama na Najeriyar mai lamba ATR-42 ya yi hatsarin ne da safiyar yau Litinin bayan tasowa da Benin zuwa Lagos.

    A sanarwar da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya kaɗu da labarin hatsarin jirgin da ya yi ajalin dukkan mutum 32 da ke ciki da suka hada da fasinjoji 25 da ma'aikata 7.

    Ya mika sakon ta'aziyya ga Babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Marshal Sunday Kelvin Aneke da dukkan ma'aikatan maza da mata na rundunar sojin sama ta Najeriya.

    Tinubu ya ce wannan ranar baƙin ciki ce ba ga sojoji ba har ga ƴan Najeriya baki ɗaya, ya ce sojoji na sadaukar da rayukansu domin kare ƴan ƙasa, dan haka sadaukarwar ba za ta bi rariya ba.

    Ya kuma bada umarnin gudanar da binciken gaggawa kan musabbabin haɗarin jirgin, da lalubo hanyar magance aukuwar hakan nan gaba.

    Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya yabawa rundunar sojin sama ta Najeriya kan aikin ceton da suka kaddamar cikin gaggawa, da martanin gaggawar da gwamnatin jihar Onbdo ta yi n girke jami'ai inda jirgin ya faɗi.

    Sai dai ita ma fadar shugaban Najeriyar bata bayyana sunayen wadanda suka rasu a hatsarin jirgin ko wadanda suka jikkata ba.

  4. Amurka ta amince da sayar wa UAE makamai na dala biliya ɗaya

    Makamai

    Amurka ta amince da sayar wa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) makamai da darajarsu ta kai dala biliyan ɗaya.

    A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce, “Wannan yarjejeniyar sayar da makaman za ta ƙarfafa ikon Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wajen tunkarar barazanar da take fuskanta a yanzu da kuma waɗanda ka iya tasowa nan gaba, tare da inganta haɗin gwiwar soji tsakaninta da Amurka.”

    Sanarwar ta kuma ce sayar da makaman “za ta taimaka wajen aiwatar da manufofin harkokin wajen Amurka da kuma manufofinta na tsaron ƙasa ta hanyar ƙarfafa tsaron ɗaya daga cikin manyan ƙawayenta a fannin tsaro.”

    A watannin baya-bayan nan, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta fuskanci zumunci mai cike da ƙalubale da wasu maƙwabtanta, ciki har da Saudiyya da Iran.

    Bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran a lokaci guda, UAE na daga cikin ƙasashen da Iran ta ce ta mayar wa da martani, bayan hare-haren makamai masu linzami da Amurka ta kai mata.

  5. Harin sojin Myanmar ya hallaka 'yan gudun hijira 8 a jihar Rakhine

    Ƙungiyar ƴan tawaye a Myanmar sun ce sojoji sun kai hari ta sama a sansanin ƴan gudun hijira a jihar Rakhine tare da hallaka mutum taƙwas cikin ƙwanaki biyu da suka gabata.

    Sun ce an kuma jikkata mutum 11 a wani sansanin da ke garin Ponnagyun a ranar Lahadi.

    Harin na zuwa ne bayan wani da aka kai a jihar da ya hallaka mutum 50. Kawo yanzu babu martanin da gwamnatin Burma ta yi kan iƙirarin ƙungiyar, amma a baya sun sha nanata su na kaucewa duk wani hari da ka iya fadawa kan farar hula.

    Harwayau, babu wata kafar yada labarai mai zaman kan ta da ta tabbatar da iƙirarin ƙungiyar.

    Jihar Rakhine dai ta kasance sansanin yaƙin da dakarun ƙungiyar ƴan tawayen Arakan ke iko da shi da ke kusa da gaɓar teku, ya yin da sojin gwamnati ke kokarin karɓe iko amma lamarin ya ci tura.

  6. Ƴansanda a Kano sun gayyaci Warkal kan zargin harbin bindiga

    Rundunar ƴansanda jihar Kano ta gayyaci fitaccen ɗan siyasar jihar Aminu Abdullahi Warkal domin amsa tambayoyi kan zargin fito da babbar bindiga a wani taron siyasa.

    Ƴansandan sun ce an gayyace shi ne bayan ɓullar wani bidiyo a shafukan sada zumunta, da ya nuna Warkal rike da bindigar.

    Sanarwar da kakain ƴansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce ƙwamishinan ƴansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fitar da bindiga a bainar jama'a a kuma wurin taron soyasa ya saɓawa dokakin mallakar bindiga.

    Rundunar ƴansandan ta ce hakan ka iya ɗarsa fargaba a zukatan jama'a da barazana ga tsaro da tada husuma.

    Sanarwar ta ƙarƙare da cewa rundunar ƴansanda ba za ta zuba ido mutane su dinga abin da suka ga dama ba, da fidda makamai da sauransu.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki ke kiraye-kirayen ayi taka tsantsan a gangamin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni da aka kaddamar a zaben shekara mai zuwa.

    Zaɓukan da kan zo da tashin hankali da ake zargin ƴandaba magoya bayan ƴan siyasa da haddasawa.

  7. Shettima ya je ta'aziyya ga iyalan masu haƙar ma'adinai a jihar Neja

    Kashhima Shettima da gwamna Bago
    Bayanan hoto, An gudanar da zanga-zanga kan mutuwar masu haƙar ma'adinan a jihar Neja.

    Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya ga jihar Neja, ga iyalan masu haƙar ma'adinan nan 37 da suka rasu a hannun jami'an hukumar NCDC bayan kama su kan zargin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

    Ya ja jantawa iyayen mamatan da gwamnatin jihar Neja, da isar da sakon gwamnatin tarayya zata bada tallafin kuɗi ga iyayen mamatan 37 da suka kai naira miliyan 250.

    Tun da fari hukumar NSCDC ta ce jami'anta sun kama mutanen ne a ranakun Talata da Laraba a a watan Satumba a wasu sassan jihar Neja, bisa zargin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

    An ce an kama su ne a kusa da Borgu, wani yanki da ake gudanar da ayyukan haƙar ma'adanai.

    Sai dai hukumar ta ce mutanen sun rasu ne a ranar Alhamis yayin da suke tsare.

    Da farko, jami'an sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwarsu, amma bayanan da suka fito daga waɗanda suka tsira sun yi zargin an fesa musu wani magani da cunkusa su a ƙaramin ɗaki ba tare da wadatacciyar iska ba.

    Lamarin dai ya kai ga gwamnatin Najeriya kafa ƙwamitin mutum 10 da aka ba su makonni biyu su gudanar da binciken ainahin abin da faru, kuma a cikin makonnan ne wa'adin zai kammala.

  8. Bayanai na ƙara fitowa kan jirgin sojin Najeriya da ya fadi a Ondo

    Jirgin sojin Najeriya

    Bayanai na kara fitowa kan hatsarin jirgin sojin Najeriya da ya faru a kudancin ƙasar.

    Rundunar sojin sama ta ƙasar ta kaddamar da aikin ceto ba ƙaƙƙautawa domin gano wadanda hatsarin jirginta mai lamba ATR-42 da ya fadi a yankin Igbokoda a jihar Ondo da ke kudancin ƙasar.

    Hatsarin jirgin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da ya ke gudanar da aikin da ya saba tsakanin Benin zuwa Lagas.

    A sanarwar da Daraktan yada labarai na shalkwatar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce ana ci gaba aikin ceto kan jiki kan ƙarfi.

    Ya ƙara da cewa rudunar za tai duk mai yiwuwa domin ganin an gudanar da aikin cikin gaggawa, ai dai babu karin bayani kan abin da ya haddasa hatsarin da wadanda ya rutsa da su da muƙamansu.

    Sun ce za ai hakan bayan samun karin haske da kammala aikin ceton.

    Mazauna yankin sun shaidawa BBC jirgin ya faɗi ne a wani kurmi da ke kusa da sansanin sojin sama. Wani ganau ya ce an yi amfani da kwale-kwalen shi a aikin ceton, an kuma gano takalma da tufafin fasinjojin kuma sun mika su ga hukumomi.

    Shi ma wani na daban ya ce mutane sun ji kara mai ƙarfin gaske, da harke a sararin samaniya sun ɗauka saboda ruwan sama da ake yi ne, amma daga bisani sai hayaƙi ya tashi sama daga inda jirgin ya faɗi.

    Tuni rundunar sojin sama da jami'an tsaro suka cika wurin, domin ci gaba da aikin ceton.

    Tun da farko, hukumomi a Najeriyar ne suka fara tabbatar da afkuwar hadarin jirgi mai saukar ungulu na sojin kasar a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Hukumomi sun ce jirgin na ɗauke ne da mutane 32, kuma 25 fasinjoji ne sai ma'aikata 7 a lokacin da ya fadi a sansanin sojin sama da ke yankin Igbokoda, an gano tarkacen jirgin kuma ana ci gaba da aikin ceto.

  9. Amurka da Isra'ila sun ce an yi shirin kifar da jirgin Flydubai a Tel Aviv

    Jirgin Flydubai
    Bayanan hoto, Jirgin ya yi saukar gaggawa a kasar Saudiyya dauke da fasinjoji 170

    Amurka da Isra'ila sun ce ta yiwu mataimakin matukin jirgin Flydubai da akai zargi da kokarin karbe iko dashi, ya yi shirin kifar da shi a filin jirgin sama na Ben Gurion da ke birnin Tel Aviv.

    Rahotanni sun ce mutumin dan asalin Oman na da tsattsauran ra'ayi.

    Shi ma babban lauyan gwamnatin Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ya ce, mutumin ya yi ƙoƙarin kai harin ta'addanci da jirgin mai lamba FZ1073 da ya taso daga birnin Dubai zuwa Tel Aviv a ranar larabar makon da ya wuce.

    Firai ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu, ya ce matuƙin jirgin da fasinjojin da ke ciki da ma'aikatansa sun yi ƙoƙarin ganin ba a maimaita abin da ya faru na 9/11 a Amurka ba, lokacin da ƙungiyar Al-Qa'ida ta kai mummunan hari a ƙasar.

    Ya dai jikkata babban matukin jirgin inda ya caka masa wuka, kafin daga bisani fasinjoji da ma'aikata sukai nasarar balla kofar da daure shi, akai kuma nasarar saukar jirgin a kasar Saudiyya.

  10. Magoya bayan Imran Khan na zanga-zangar buƙatar a sake shi

    Dubban masu zanga-zanga a titunan Pakistan

    Dubban magoya bayan tsohon firai ministan Pakistan Imran Khan da ake tsare da shi a gidan kaso sun fara maci daga arewa maso gabashin kasar da kiran hukumomi su sake shi.

    Tun a watan da ya gabata ake nuna damuwa kan tabarbarewar lafiyar tsohon firai ministan mai shekaru 74 a duniya. Iyalansa yi ikirarin ya na fama da raunin gani, bayan hukumomi sun ki daukar matakin da ya dace na duba lafiyar idon shi.

    Fitaccen mai wasan Kurket da ya rikiɗe ɗan siyasa, na fuskantar shari'a kan ƙararraki sama 100, an kuma yanke masa zaman kason shekaru 17, sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ya ce bita da ƙullin siyasa ne.

    Duk da cewa ana tsare da shi a gidan kaso, amma Mista Khan ya kasance a sahun gaba a faggen siyasar Pakistan, kuma ya na ƙara samun magoya baya da ke zanga-zangar kiran a sake shi, wadda lokuta da dama ta ke rikiɗewa tahin hankali.

    A ranar Asabar din ƙarshen mako be aka fara macin daga birnin Lakki Marwat mai nistan kilomita 275 daga birnin Islamabad, ana kuma saran a ci gaba da ita a ɗaukacin kasar a makon nan.

  11. Gurneti ya cirewa ɗalibi hannu a zanga-zangar da suke yi a Faransa

    Wani ɗalibi mai shekaru 15 a Faransa ya rasa hannunsa sakamakon fashewar wani gurneti, yayin zanga-zangar adawa da rashin ingancin tsarin ilimi.

    Wani jami’in yankin Lens ya ce yaron ya ɗauki gurnetin ne da ’yan sanda ke amfani da shi wajen tarwatsa tarzoma.

    Daruruwan makarantu a faɗin Faransa sun rufe gaba ɗaya ko kuma na wani lokaci, saboda zanga-zangar da ta fara a watan da ya gabata.

    A birnin Paris kuwa, gobara ta tashi sau uku a wurare daban-daban a wata makarantar sakandare, lamarin da ya tilasta kwashe ɗalibai kusan ɗari daga makarantar.

    Zanga-zangar, wadda aka fara saboda ƙarancin malamai da kuma rashin isassun kayan aiki a makarantu, ta fara ne a ƙarshen watan Satumba a wata makaranta da ke Paris kafin daga bisani ta bazu zuwa sassan ƙasar baki ɗaya.

  12. Sojojin Yemen sun kai farmakin ƙwace birnin Sanaa

    Sojojin gwamnatin Yemen sun ce sun fara kai wani farmaki kan babban birnin ƙasar, Sanaa, da nufin ƙwace birnin daga hannun mayakan ƙungiyar Houthi da Iran ke marawa baya.

    Wata tashar talabijin mai ala alaƙa da 'yan Houthin ta ruwaito cewa Saudiyya ta kai hari kan birnin na Sanaa.

    Wannan na zuwa ne bayan da ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya ce ya kai hare-hare kan daruruwan wurare, a ƙoƙarinsa na dakile dannawar da mayakan Houthi suka yi a watan da ya gabata.

    Jami’an Yemen sun ce dakarunsu sun ƙwace muhimman wurare a mashigar ruwa ta Bab el-Mandeb, bayan sun fatattaki mayaƙan Houthi din daga wannan muhimmiyar hanyar ruwa da ke bakin ƙofar shiga Tekun Bahar Maliya.

    Sun ce samun iko da waɗannan wurare na da matuƙar muhimmanci ga tsaro da kuma zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Tashin hankali na ƙaruwa tsakanin Saudiyya da 'yan Houthi na Yemen, a baya-bayan nan an zarge su da kai hari biranen Makka da Madina, da ƙasashen duniya sukai allawadai da shi, amma mayakan Houthi sun musanta kai hare-haren.

  13. Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

    ..

    Kusan shekara 70 ke nan da Najeriya ta gano ɗanyen mai na kasuwanci. Amma duk da wannan tsawon lokacin da ƙasar ta kasance tana fitar da miliyoyin ganga na ɗanyen, tambayar da ake yi ita ce: me wannan arziki ya kawo wa Najeriya, kuma me ƙasar ta rasa saboda dogaro da shi?

    A wani rahoto da ma'aikatar man fetur ta Najeriya ta wallafa kan tarihin ɗanyen mai a Najeriya, ta ce a shekara ta 1956, kamfanin Shell-BP ya gano ɗanyen mai na kasuwanci a Oloibiri, a jihar Bayelsa ta yanzu.

    Rahoton ya ƙara da cewa shekara biyu bayan, wato a 1958, Najeriya ta fara fitar da ɗanyen mai zuwa kasuwannin duniya, wanda shi ne ya buɗe wani sabon babi a tattalin arzikin ƙasar.

    A wani binciken da babban bankin Najeriya CBN ya yi, ya gano cewa kafin gano mai, noma shi ne babban tushen arzikin ƙasar, wanda ke samar da kuɗaɗen shiga na gwamnati, amma daga baya kuɗaɗen da Najeriya ke samu daga fitar da mai suka zama ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar.

    Ga ƙarin bayani kan wannan labarin idan kuka latsa nan.

  14. Al'ummar Taiz na fama da ƙarancin gas

    Taiz da wasu lardunan Yemen na fama da matsalar ƙarancin gas na girki, inda jama'a da dama ke dandazo a gidajen sayar da gas.

    Lamarin na nuna irin wahalar da jama'a ke fuskanta a kullum sakamakon ƙarancin gas ɗin.

    Jama'a na yin dogayen layuka domin samun gas, inda wasu ke kafa layi tun da sanyin safiya.

    Ana kuma samun turmutsitsi sakamakon yawan mutanen da ke neman gas.

    ..
    ..
    ..
  15. Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo

    jirgi mai saukar ungulu

    Ministan sufurin jiragen sama na ƙasar, Festus Keyamo ya tabbatar da cewa jirgin sojin ƙasdar mai saukar ungulu ya faɗi a Igbokoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Ilaje ta jihar Ondo.

    Keyamo ya ce jirgin na ɗauke da mutum 32, da suka haɗa da fasinjoji 25 da ma'aikatan jirgin bakwai.

    Hatsarin ya haifar da firgici a yankin da ke gabar teku, yayin da aka tura jami’an agajin gaggawa da na tsaro zuwa yankin.

    Wani mazaunin yankin, Olorunlola Oluwafemi, ya shaida wa BBC cewa ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya lokacin da mutanen yankin suka ji “ƙara mai ƙarfi kamar tsawa.”

    Ya ce bayan sun fahimci cewa ba tsawa ba ce, “mun fita waje inda muka gano cewa kamar jirgin sama ne.”

    Ya ƙara da cewa hayaki na tashi daga wurin da jirgin ya faɗi.

    A cewar Oluwafemi, jirgin ya yi hatsarin ne kusa da wani daji da ke makwabtaka da sansanin rundunar sojin ruwan Najeriya na FOB a Igbokoda.

    Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun tura jami’ai zuwa yankin, inda ake ci gaba da aikin nema da ceto.

    Jirgi mai saukar ungulu
  16. Yemen ta ƙaddamar da hari don ƙwato Sana'a daga hannun Houthi

    ..

    Dakarun gwamnatin Yemen sun ce sun fara ƙaddamar da gagarumin farmaki kan babban birnin ƙasar, Sanaa, da nufin ƙwato birnin daga hannun ƙungiyar Houthi da Iran ke marawa baya.

    Wani gidan talabijin mai alaƙa da Houthi ya ruwaito cewa Saudiyya ta kai hari kan Sanaa.

    Hakan na zuwa ne bayan gamayyar ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ta kai hare-hare kan ɗaruruwan wurare , a wani yunƙuri na dakile mayaƙan Houthi daga ci gaba da nausawa wasu yankunan.

    Jami'an Yemen sun ce dakarunsu sun ƙwace wasu muhimman wurare a mashigar Bab el-Mandeb, bayan sun fatattaki mayaƙan Houthi daga wannan muhimmiyar mashigar ruwa da ke tekun Maliya.

  17. An kashe aƙalla mutum 28 duk da dokar hana fita a Filato

    An kashe aƙalla mutum 28 a sabbin hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomi uku na jihar Filato, duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta ƙaƙaba a ranar 21 ga Satumba domin dawo da zaman lafiya da hana ci gaba da asarar rayuka.

    Yankunan da abin ya shafa ciki har da Mangu, Bokkos da Barkin Ladi, sun fuskanci hare-hare akai-akai a 'yan makonnin nan.

    Lamarin ya jefa dubban mazauna cikin fargaba, ya kuma kawo cikas ga ayyukan noma da kiwo, tare da tilasta wa mutane da dama barin harkokin samun abincinsu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a sabon harin da aka kai jiya, an kashe mutum biyu tare da jikkata wasu shida bayan an kai hari kan makiyaya da ke cikin motar ɗaukar kaya a kusa da wani gidan mai da ke Bukuru, a ƙaramar hukumar Jos South ta jihar Filato.

    Harin ya faru ne ƙasa da makonni biyu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan makiyaya a kusa da garin Kassa da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata mutum ɗaya.

    Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos, ya ce 'yan bindigar sun kai wa motar hari ne da misalin ƙarfe 5:30 yayin da mutanen ke dawowa daga kasuwar shanu zuwa ƙaramar hukumar Bassa.

    Shugaban ya yi allah-wadai da harin, tare da kira ga jami'an tsaro su gano waɗanda suka aikata shi tare da gurfanar da su a gaban shari'a.

  18. Yadda Kanawa ke murnar dawowar ruwan famfo

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don ganin yadda Kanawa ke murnar dawowar ruwan famfo

    Wasu al’ummun jihar Kano na murnar samun ruwan famfo a karon farko bayan fiye da shekara 10 wanda gwamnati ta kashe kimanin naira biliyan 22 don samarwa.

    Wasu daga cikin mutanen da ke murna sun bayyana mana farin cikinsu.

  19. An rufe makarantu kusan 500 kan zanga-zangar ɗalibai a Faransa

    ..

    Faransa na fara wani sabon makon karatu yayin da aka rufe makarantu kusan 500 sakamakon ci gaba da zanga-zangar da dalibai ke yi.

    Ministan Ilimi ya bayyana cewa an dauki matakin rufe makarantun ne saboda dalilai na tsaro, inda ya kara da cewa an kona ko kuma an yi mummunar barna a makarantu ashirin da hudu a cikin makonni uku na zanga-zangar.

    Daliban na cewa rashin malamai, da tsawon lokacin karatu a makaranta, da kuma rashin kayan aiki masu inganci na kawo cikas ga karatunsu.

    Wannan yunkuri ya samo asali ne daga wata makaranta a birnin Paris kafin daga bisani ya bazu zuwa sassan kasar baki daya.

  20. Ƴansanda sun gano sansanin da ake tsare da ƴan NYSC da aka sace

    ..

    Yan sanda a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun gano wani sansani da ake tsare da aƙalla matasa 19 masu yi wa ƙasa hidima da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan.

    Kwamishinan ’yan sandan jihar, Audu Bosso, ya ce jirage marasa matuƙa sun taimaka wajen gano sansanin, amma jami’an tsaro ba su kai ga isa wajen ba saboda ana kyautata zaton an dasa abubuwan fashewa a zagayen wajen.

    Da yake magana da manema labarai ranar Asabar, Bosso ya ce: “Jiya mun shiga daji, mun bi sawunsu har zuwa wani wuri. Amma a lokacin ba mu iya kutsawa zuwa wurin da bayananmu suka nuna mana cewa suna can ba.”

    Ya ce binciken da aka yi da jirgi marar matuƙi ya tabbatar da inda sansanin yake.

    “Jirgin marar matuƙin ya nuna mana ainihin inda suke. Amma matsalar da muke fuskanta ita ce, bisa bayanan sirrin da muke da su, an dasa abubuwan fashewa a sansanin,” in ji Bosso.

    Ya ce ana tura motocin katapila da motocin yaƙi masu sulke yayin da ’yan sanda ke shirin gudanar da aikin ceto mutanen.

    Omotosho Adewale, wanda ɗansa ke cikin waɗanda aka sace, ya shaida wa BBC cewa kuɗin fansar da masu garkuwar ke nema sun fi ƙarfinsa.

    Ya ce “Naira miliyan 50 suke nema,”.

    Ya ƙara da cewa “Don Allah, duk abin da gwamnati za ta iya yi ta taimaka mani... Na samu damar rainon yaron nan ne kawai saboda taimako da goyon bayan da na samu daga kowa,”.

    Biyan kuɗin fansa abu ne da ya saɓawa doka a Najeriya, kuma hukumomi sun sha gargaɗin iyalan waɗanda aka sace kada su biya. Sai dai iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kan fuskanci matsin lamba na biyan kuɗi domin a sako ’yan uwansu.

    Ba a bayyana takamaiman wurin da sansanin yake ba, kuma ’yan sanda ba su bayyana waɗanda ke da alhakin sace mutanen ba.

    Satar mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da kasancewa babbar matsalar tsaro a Najeriya.

    A kudu maso gabashin ƙasar, an danganta wasu sace-sacen da aka yi a baya da ƙungiyoyin ƴan aware, ciki har da IPOB. Sai dai hukumomi ba su danganta wannan satar da wata ƙungiya ba.

    Lamarin ya jawo damuwa sosai, kasancewar sace mutane da yawa lokaci guda ba kasafai ake samun irin sa a kudancin Najeriya ba kamar yadda ake samu a wasu sassan arewacin ƙasar.

    Waɗanda aka sace sun taso ne daga Ibadan zuwa sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin Abia da Akwa Ibom, lokacin da ’yan bindiga suka kai wa motocin bas ɗinsu hari kusa da Umunoha a jihar Imo a ranar Alhamis da ta gabata.