Mun lalata jiragen yaƙin Amurka ƙirar F-35 guda uku a Jordan - Iran

Asalin hoton, EPA
Dakarun juyin-juya-halin Iran wato IRGC sun ce sun lalata gaba ɗaya jiragen yaƙin Amurka kirar F-35 guda uku, sannan ta yi wa wasu guda uku mummunar ɓarna a wani harin makamai masu linzami da ta kai kan sansanin sojin sama na Al-Azraq da ke Jordan.
Sai dai har zuwa yanzu, Amurka ko Jordan, ko kuma wasu majiyoyi masu zaman kansu, ba su tabbatar da wannan ikirari ba.
Sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya bayyana cewa harin martani ne ga hare-haren sama da Amurka ta kai kan gidaje biyu a tsibirin Qeshm, inda ta ce mutane uku na gida, ciki har da wani yaro, suka mutu, yayin da wasu yara biyu suka jikkata.
IRGC ta kuma yi ikirarin cewa wasu jami'an sojin Amurka da ma'aikatan fasaha sun mutu a harin da aka kai kan rumfar da ake ajiye da gyaran jiragen yaƙi a sansanin Al-Azraq, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka mutu ba.
A baya, sojojin Jordan sun sanar da cewa tsarin kariyar sararin samaniyarsu ya tare tare da lalata makamai masu linzami guda biyar da aka harba daga Iran, kuma sun ce harin bai yi sanadin asarar rayuka ba.
Har zuwa yanzu, Amurka ba ta fitar da wani rahoto da ke tabbatar da lalata jiragen yaƙin F-35 ko kuma asarar rayukan sojojinta a wannan harin ba.






















