Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Laraba 16/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Badriyya Ƙalarawi

  1. Amurka ta ƙara kuɗin ruwa domin daƙile hauhawar farashi

    Babban bankin Amurka, ya ƙara kuɗin ruwa a karo na farko cikin sama da shekara uku domin daƙile hauhawar farashin kayayyaki.

    Bankin ya ɗaga kuɗin ruwansa da kaso ɗaya cikin huɗu, inda ya kai tsakanin kashi 3.75 zuwa 4 cikin 100.

    Wannan shi ne matakin farko na sabon shugaban bankin, Kevin Warsh.

    Hakan na zuwa ne duk da kiraye-kirayen Shugaba Donald Trump na a rage kuɗin aro.

    Hauhawar farashin kayayyaki ya karu sakamakon tashin farashin mai da yakin Iran ya haddasa, abin da ke kara wa masu amfani da kayayyaki matsin lamba gabanin zabukan rabin wa’adi a Amurka.

  2. Canada ta yi maraba da ƙulla ƙawance da Turai

    Firaministan Kanada, Mark Carney, ya yi maraba da ƙulla dangantaka ta ƙut-da-ƙut da Tarayyar Turai (EU) bayan shugabar hukumar gudanarwar EU ta gabatar da tunanin bai wa ƙasarsa matsayin abokiyar hulɗa ta musamman.

    Sai dai bayaninsa bai yi ƙarin haske kan yadda wannan tsari zai kasance ba.

    Majalisar Tarayyar Turai na cewa akwai buƙatar ƙasashe da ke bin tsarin dimokuradiyya su sake fasalta haɗin gwiwarsu tare da gina sabbin kawance cikin gaggawa, a daidai lokacin da tsarin dokokin duniya ke fuskantar ƙalubale.

    A makon da ya gabata, Firaminista Carney ya yi magana kan neman wata “kawance ta musamman” da Tarayyar Turai, yayin da dangantakar ƙasarsa da Amurka ƙarƙashin Donald Trump ke ƙara tsami.

  3. Sojojin Najeriya sun kuɓutar waɗanda ƴan bindiga suka sace

    Sojojin Najeriya

    A Najeriya, rundunar Fansar Yamma da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin arewa maso yammacin kasar, ta ce ta sami nasarar ƙubutar da mutum fiye da 30 da ƴan bindiga suka sace, kuma suke garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi. Rundunar ta kuma damƙe wasu mutane da take zargin ƴan ta'adda ne.

    Sai dai yayin da rundunar ke bayyana waɗannan nasarori, wasu masana harkar tsaro na ganin akwai buƙatar dakarun Najeriyar su kara matsa ƙaimi, wajen bin masu aikata miyagun laifuka har cikin daji, domin su daƙile su.

    Wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Aliyu Ɗanja ya aikewa manema labarai, ta ce dakarun rundunar hadin gwiwar sun aiwatar da ayyukan tsaro a jihohin Katsina da Kebbi, a ranakun Litinin da Talata da suka gabata. Inda suka kuɓutar da mutum talatin da ɗaya daga hannun ƴan bindiga.

    Kana suka ƙwato alburusai da sauran ababen ƙaddamar da hari, da babur, da kayan sarki, da dai sauransu. Duk da yake dai sanarwar ba ta bayyana yadda lamarin ya kasance ba, ta ce a jihar Katsina, dakarun sun kuɓutar da mutum goma, da suka haɗa da maza uku da mata bakwai, daga hannun ƴan bindiga, bayan samun wani kiran neman ɗaukin gaggawa, game da sace mutanen a ƙauykan Unguwar Daudu da Unguwar Ci-ɓauna na yankin karamar hukumar Funtuwa.

    A jihar Kebbi ma, bayan samun wasu ingantattun bayanan sirri, dakarun sun ƙaddamar da wani sintiri irin na fito-na-fito, a ƙauyukan Fafala da Dadikwa na yankin karamar hukumar Kangiwa.

    Inda ɓarin wutar da jami'an tsaron suka yi ya tilasta wa ƴan ta'addan tserewa, aka kuma ƙubutar da mutum ashirin da daya, kamar yadda sanarwar rundunar Fansan Yamman ta bayyana.

    A wani namijin ƙokarin da dakarun Najeriyan suka yi kuma, sun sami nasarar damke wasu 'yan ta'adda biyu a bangaren ƴantumaki na yankin karamar hukumar ɗan Musa ta jihar Katsina, wadanda binciken farko ya nuna cewa, suna da alaka da wani gawurtaccen ɗan ta'adda mai suna Mannori, a cewar sanarwar.

  4. Cutar Ebola na kara yaɗuwa a Kongo

    Dakta Tedros Adhanoum Ghebreyesus

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ya ce cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na ci gaba da yaɗuwa, sai dai akwai alamun da ke nuna ana samun ci gaba wajen daƙile ta.

    Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yaduwar cutar ta ragu a lardin Ituri, inda annobar ta fara ɓarkewa , kuma ba a samu sabon mutum mai ɗauke da cutar ba a lardin gabashin Kivu tun daga watan Mayu.

    A wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Geneva, Dakta Tedros ya ce ana samun nasara a ƙoƙarin da ake na shawo kan cutar Ebola sai dai har yanzu ba a kai ƙarshen yaƙi da cutar ba.

    Ya bayyana cewa yankunan gabashi da arewa maso gabashin Kongo suna da girma sosai, kuma ana shan wahala a yankin saboda ƙarancin ababen more rayuwa.

    Ya ce adadin wadanda suka kamu da Ebola a arewacin Kongo ya ƙaru da kusan kashi hamsin cikin ɗari a cikin mako guda.

    Ya ƙara da cewa cutar ta bazu zuwa larduna bakwai na Kongo, kuma akwai yiwuwar ta ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu yankuna.

    Tun daga tsakiyar watan Mayu, lokacin da aka ayyana barkewar annobar, an tabbatar da sama da mutane dubu bakwai sun kamu da cutar, yayin da mutum sama da dubu uku da dari biyar suka rasu.

  5. An yanke wa tsohon shugaban Kosovo zaman kason shekaru 25

    Alkalan kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Kotu ta musamman a birnin Hague ta yankewa Tsohon shugaban ƙasar Kosovo, Hashim Thaci, hukuncin daurin shekara 25 a gidan yari kan laifukan yaki.

    Alƙalan kotun sun same shi da laifin kisan kai da azabtar da daruruwan mutane a lokacin yakin neman ‘yancin kan Kosovo daga Serbia a shekarun 1990, lokacin da yake jagorantar rundunar ‘yan tawayen Kosovo Liberation Army

    Kotun ta kuma yankewa tsohon shugaban ƴan tawayen KLA Yakup KrasniqI shi ma shekaru 25 a kurkuku. Da kwamandan KLA Kadri Veseli da aka yankewa zaman shekara 18, ya yin da Racep Selimi ya samu zaman shekara shekaru 13, bayan samunsu da laifukan take hakkin dan adam, da cn zarafi da kashe-kashen farar hula.

    An samu Thaçi, mai shekara 58, da hannu dumu-dumu a kisan an adawar siyasa 96, da azabtar da daruruwan mutanen da ake zargi da taimakawa ƴan Serbia.

    Thaci ya na tsaye a kotun a lokacin da aka yanke masa hukuncin, a baya dai ya sha musanta zarge-zargen.

  6. Houthi: Mun kakkaɓo jirgin yaƙin Saudiyya F-15

    Jirgi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan tawayen Houthi na Yemen sun yi iƙirarin kado jirgin yaƙin Saudiyya, ta amfani da makaman da aka ƙera a cikin gida.

    Mai magana da yawun Houthi Yahya Saree ya wallafa a shafin sada zumunta cewa sojojin Yemen sun yi nasarar kaɗo jirgin yakin Saudiyya mai lamba F-15 lokacin gudanar da aiki a yankin Marib.

    Yahya Saree ya ƙara musanta iƙirarin Saudiyya na cewa sun yi koƙarin kai harin makamai masu linzami birnin Makka.

    "Hare-haren da mu ke kai wa, mu na yi ne wuraren ajiyar mai da sansanonin soji," in ji shi.

    Sa'o'i kaɗan da suka gabata, rundunar sojin Saudiyya ta yi sanar da kakkaɓo jirage marassa matuƙa da ƴan tawayen Yemen suka harba birnin Makka, lamarin da Houthi uka musanta.

    Sama da shekaru 10 kenan da yaƙinb basasa ya ɓarke a ƙasar Yemen tsakanin ƴan tawayen Houthi da gwamnatin Yemen, wadda Saudiyya ke marawa baya.

    A ɓangare guda kuma, su sanar da rufe mashigar ruwa ta tekun Maliya wato Babul-Mandhab da Saudiyya ke amfani da ita wajen fitar da mai ƙasashen ƙetare, bayan Iran ta rufe mashigar Hurmoz.

  7. Sama da mutum 100,000 sun cika shekara 100 a Japan

    Mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya a Japan ta ce a karon farko a tarihin ƙasar, adadin mutanen da suka cika shekaru 100 ko sama da haka da haihuwa, sun haura 100,000.

    Kididdiga ta nuna akalla akwai mutum 107,677 da suka kai shekaru 100 ko fiye, adadi mafi girma a duniya, kuma kashi 88 cikin 100 na mutanen mata ne.

    Macen da ta fi kowa tsufa a ƙasar ita ce Kishimoto Fuyo, mai shekara 114, daga yankin Kyoto, ya yin da a ɓangaren maza ake da Kato Hikaru, mai shekara 112, ɗan asalin yankin Kumamoto.

    Ministan lafiyar Japan Kenichiro Ueno, ya sanar da farin cikin ganin yadda mutane ke tsahon rai, cikin kwanciyar hankali da ingantacciyar lafiya. Ya ƙara da cewa wannan gagarumin ci gaba ne da zai amfani masu binciken kimiyya da fasaha.

    Sai dai ya yi gargaɗin ya yin da ake murnar adadin tsofaffi na karuwa, a ɓangare guda kuma akwai fargabar ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar na rashin ma'aikata matasa.

    Ƙwararru dai na cewa tsahon rai da ake samu a Japan na da nasaba da cin abinci mai gina jiki da motsa jiki. Yawancin abincin da ƴan Japan ke ci sun haɗa da kifi, da shinkafa da kayan lambu da na marmari da ba sa ɗauke da maiko idan aka ƙwatanta da nau'in abincin da ake ci a ƙasashen turai.

    Haka kuma, yawancin tsofaffin mutane a Japan na tafiya da kafafunsu, su na hawa motocin haya na safa-safa, da hawa keke da sauransu.

    Japan dai na fama da karancin matasa inda ƙasar ta cika da tsifaffi cikin shekarun nan. Hakan ya kara bude kasuwar masu saida kunzugun manyan wata Pampers a turance, da ake sanya tsofaffi domin kaucewa yin najasa kafin su karasa banɗaki.

  8. Saudi Arabia ta ce ta kakkaɓo jirgi maras matuƙi na mayaƙan Houthi a kusa da Makka

    Saudi

    Asalin hoton, Reuters

    Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirgin ƴantawayen Houthi maras matuƙi da suka harba kusa da birnin Makka

    Rundunar kare sararin samaniyar Saudiyya ta ce ta kakkaɓo tare da lalata wani jirgin sama maras matuƙi da ƴan tawayen Houthi na Yemen suka harba kafin ya shiga yankin da aka haramta zirga-zirgar jiragen sama kusa da birnin Makka mai tsarki.

    A cewar ƙawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta a yaƙin Yemen, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙaruwar hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da ake kai wa wurare daban-daban a faɗin ƙasar.

    Mai magana da yawun ƙawancen, Turki al-Maliki, ya ce a cikin wata sanarwa cewa wannan ne karo na biyu da Houthi suka yi yunkurin kai hari kan Makka.

    Ya ce yunkurin farko ya faru ne a watan Yulin 2017 lokacin da aka harba wani makami mai linzami mai dogon zango zuwa yankin.

    A halin da ake ciki, an fitar da gargadin tsaro na wani dan lokaci a ranar Talata 15 ga watan Satumba a biranen Makka da Jiddah da kuma Taif. Sai dai daga bisani hukumomin tsaron farin kaya suka sanar da cewa an shawo kan barazanar kuma babu wata matsala ga jama'a.

    Gargaɗin da aka bayar a Makka ya haifar da fargaba a tsakanin al'umma, domin birnin bai fuskanci irin wannan lamari ba a 'yan kwanakin nan duk da tashin hankalin da ake ci gaba da samu tsakanin Houthi da Saudiyya.

    Kwana guda kafin haka, hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka da Houthi suka kai kan birane uku a Saudiyya sun jikkata fararen hula 13, kamar yadda kawancen ya bayyana.

    Kawancen ya kuma ce hare-haren sun yi sanadin lalacewar gidaje bakwai da motoci biyu.

    Ya zuwa yanzu dai kungiyar Houthi ba ta fitar da wata sanarwa ba kan ikirarin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya yi.

  9. Kanada na gab da zama abokiyar huldar Tarayyar Turai

    Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bayyana goyon bayanta ga wani sabon shiri da zai bai wa Kanada damar zama ƙasa ta farko da za ta samu matsayin abokiyar hulda ta Tarayyar Turai.

    Wannan na zuwa ne yayin da dangantaka tsakanin Kanada da Amurka ke fuskantar ƙalubale sakamakon rikicin kasuwanci da sabanin ra'ayi tsakanin ƙasashen biyu.

    Ursula von der Leyen ta shaida wa Majalisar Tarayyar Turai cewa tana son a fara tattaunawa kan bude wata kafa ta musamman ga Kanada domin kara ƙarfafa alaka tsakanin ɓangarorin biyu.

    Ta ce wannan ba yunkuri ne da aka yi domin ƙalubalantar wata ƙasa ba, mataki ne na bunƙasa karfi da hadin kai a tsakanin ƙasashen da suke da dabi'u iri daya. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Kanada ke fuskantar matsin lamba daga Amurka, bayan rushewar tattaunawar kasuwanci da karin haraji kan kayayyaki.

    Kalaman Shugaba Donald Trump na cewa Kanada za ta iya zama jiha ta 51 ta Amurka sun kara tada kura a dangantakar kasashen biyu.

    Ursula von der Leyen ta ce Kanada da Turai suna da ra'ayi iri daya kan muhimman batutuwa da suka hada da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sauyin yanayi, tsaro, Ukraine da kuma dimokuradiyya.

    Sai dai ba ta bayyana yadda wannan sabon matsayi da ake son ba Kanada zai kasance ba, musamman ganin cewa babu wannan tsarin a cikin dokokin Tarayyar Turai a halin yanzu.

    Masu sharhi na ganin duk wata tattaunawa kan wannan batu za ta iya daukar shekaru kafin ta kai ga cimma matsaya, sannan suna ganin wannan yunkuri na iya sauya yanayin siyasa da tattalin arziki a yankin yammacin Turai da Arewacin Amurka a cikin shekaru masu zuwa.

  10. Amurka ta takaita Visa ga 'ƴan Afurka ta Kudu kan zargin wariya ga farar fata

    A sabuwar danbarwar da ta kunne kai tsakanin Afurka ta Kudu da Amurka, kasar ta sanar da takaita ba da Visa ga mutanen da ake zargi da nuna wariya ko kin jinin tsirarun farar fata ƴan Afurka ta Kudu.

    Gwamnatin shugaba Trump ta soki batutuwa da dama da suka hada da tsarin Afurka ta Kudu na magance wariyar launin fata da ƙyamar ƴan kasashen waje musamman ƴan asalin Poland da Faransa da ke zaune a ƙasar.

    Sai dai Afurka ta Kudu ta musanta zarge-zargen, inda ministan harkokin wajen ƙasar Ronald Lamola ya ce su na nazari akai.

    Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya jaddada cewa hukumomin Afurka ta Kudu ba su taɓuka abin azo a gani ba don shawo kan matsalar.

  11. Gwamnan Kano ya naɗa Barista Hafsat Kutama shugabar hukumar PCACC

    ..

    Asalin hoton, PCACC

    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Barista Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙo ta Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (PCACC) ta Jihar Kano.

    Naɗin ya biyo bayan murabus da shugaban hukumar ta PCACC, Saidu Yahaya, ya yi a ranar Talata.

    Rahotanni dai na cewa Saidu Yahaya ya miƙa wasiƙar murabus ne bayan fuskantar matsin lamba daga Gwamnatin Jihar Kano kan rashin cika wasu daga cikin abubuwan da ake sa ran zai aiwatar a yayin gudanar da aikinsa.

    An naɗa Saidu Yahaya a matsayin shugaban hukumar ne a watan Agustan shekarar 2025, bayan karewar wa'adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

    Sabuwar shugabar riƙon ƙwaryar, Barista Hafsat Kutama ta yi karatun Shariʼa a Jamiʼar Bayero, kuma ta yi aiki da Maʼaikatar Shariʼa ta Kano, kafin bisani ta koma aiki a hukumar ta PCACC, inda gwamnan Kano ya naɗa ta a matsayin sakatariyar hukumar a watan Agustan 2025.

  12. 'Ɓarnar da Iran ta yi wa sansannonin sojin Amurka'

    Jiragen Amurka

    Asalin hoton, CBS

    A karon farko kafar yada labaran Amurka ta CBS kuma abokiyar hular BBC, ta wallafa hotunan abin da ta kira girman ɓarnar da hare-haren Iran suka yi wa sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

    CBS ta ce hare-haren sun yi mummunar ɓarna, inda gine-gine suka rushe da lalata motocin sojoji da sauran abubuwa masu muhimmanci sakamakon harin jirage marassa matuƙa da Iran ta kai.

    CBS ta ambato ɗaya daga cikin sojojin da aka girke a wurin na cewa, ba a bayyana wa Amurkawa girman ɓarnar da hare-haren suka yi ba.

    "An yi wa sansanonin Amurka gagarumar ɓarna, amma an lulluɓe batun ba a son bayyanawa. Mu na fuskabtar hare-hare babu ƙaƙƙautawa, kuma ba mu da ikon mai da martani," in ji shi.

    Cikin hotunan da aka yaɗa akwai wanda a ka yi zargin an ɗauke shi ne a sansanin sojin sama na Prince Sultan da ke Saudiyya. Hoton ya nuna abin da a ka yi amanna da cewa lalacewar da sansanin ya yi ne bayan kai harin kan jirgin yaƙi samfurin Boeing A-3 Sentry.

    Bayan jirgin ya fita daga jikinsa, yayin da sauran ɓangaren ya ƙone.

    Gidajen da ke sansanin sun ruguje wasu sun ƙone, yayin da na'urar da ke ankarar da sojoji lamuran da ke faruwa a sararin samaniya ta lalace baki daya.

    Wani wuri da harin ya faɗawa

    Asalin hoton, CBS

    Bayanan hoto, Tantin sojoji da aka kona a sananin Bowering a Kuwait
    Wani gini

    Asalin hoton, CBS

    Bayanan hoto, Yadda harin jirage marassa matuƙa ya lalata sansanin Arifjan da ke Kuwait.
  13. 'Za mu yi adalci kan kisan mata a Afirka ta Kudu'

    ..

    Asalin hoton, Thuthuka Zondi/BBC

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi alƙawarin gano masu hannu a kisan wasu mata a wani yanki da ke arewa maso gabashin Johannesburg.

    An sake gano ƙarin gawarwaki a ranar Talata inda ƴansanda suka ce binciken da suka yi ya haɗa da mutuwar mata takwas, galibinsu an gano sune wasu sanye da kaya, wasu kuma tsirara.

    "Lamarin na haifar da fargaba da rashin tabbas a tsakanin al'umma musamman tsakanin mata," in ji shugaban ƙasar.

    Ƴansanda sun ce suna gudanar da bincike kan yiwuwar wata ƙungiya tana da hannu a kashe-kashen.

    An dai kama mutum ɗaya dangane da gano gawar farko. Har yanzu mutumin da aka kama yana hannun ƴansanda.

    Ƴansanda sun kuma yi tayin tuƙwicin rand 400,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da ya kai ga kama masu hannu a lamarin.

    Zuwa yanzu mata biyu cikin su takwas ne aka iya tantancewa.

  14. Aƙalla mutum 60 sun rasu sanadin rufatawa mahaƙar zinare a Sudan

    Aƙalla mutum sittin sun rasu bayan da wata mahaƙar zinare ta rufta ajihar West Kordofan da ke Sudan.

    Wani da ya samu tsira ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa, wasu da dama sun yi ɓatan dabo sannan babu tabbaci kan ko sun maƙale ƙarƙashin ɓuraguzai.

    Masu aikin ceto na ƙoƙarin gano gawarwaki da waɗanda ke da sauran kwana a gaba a mahaƙar ta Al Zaara da ke kusa da El Nahud.

    Ana yawan samun irin wannan haɗari na ruftawar mahaƙar ma'adanai a Sudan.

  15. A shirye muke mu kare haƙƙoƙin Iran - China

    ..

    Asalin hoton, s_a_araghchi

    Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ya ce ƙasarsa tana da burin kare haƙƙoƙin Iran.

    Mr Wang ya bayyana a wata ganawa da Abbas Araghchi, ministan harkokin wajen Iran wanda ya yi bulaguro zuwa China ya ce ƙasar a shirye take ta ƙarfafa tattaunawa da haɗin kai tsakaninsu da Iran da kuma kare haƙƙoƙi da buƙatunsu.

    An tsara Shugaba Xi Jinping zai isa Washington a makon gobe inda zai gana da Shugaba Donald Trump.

    China, wadda ɗaya ce cikin manyan abokan hulɗar tattalin arzikin Iran ta yi ƙoƙarin sassauta rikicin Gabas ta Tsakiya da aka shafe watanni ana yi wanda kuma ya bazu zuwa maƙwabtan Iran.

    Sin, ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar tattalin arzikin Iran, tun daɗewa tana daga cikin membobin Iran. Ta yi ƙoƙarin rage tasgaroƙi a rikicin Gabas ta Tsakiya da ya ɗauki watanni da dama, wani rikici da ya kuma bazu zuwa ƙasashen makwabta na Iran.

  16. Mutanen da suka mutu sanadin rugujewar gini a Gaza ya ƙaru zuwa 20

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rugujewar ginin da ya yi rauni sakamakon yaƙi ya ƙaru zuwa aƙalla mutum 20 cikinsu har da ƙananan yara biyar.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda ake aikin zaƙulo gawarwaki da kuma masu sauran numfashi daga ɓuraguzan giin mai hawa shida a Tal al-Hawa da ke Gaza.

    Daraktan hukumar tsaro a birnin Gaza, Raed al-Dahshan ya bayanna cewa har yanzu ana jiyo muryar mutane maƙale a ƙarƙashin ɓuraguzai.

    Ya ƙara da cewa:"Ƙarancin wajen kwana ne ya tilastawa mutane tarewa a ginin bisa tunanin cewa za su fi samun tsaro.

    Sai dai kuma ginin ya rufta inda ya faɗa kan mutanen da ke barci.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ....

    Asalin hoton, Reuters

  17. Amurka ta sanar da taƙaita biza ga jami'an Afirka ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta sanar da taƙaita bayar da takardun biza ga mutanen da ake zargi da nuna wariyar launin fata ga tsirarun farar fata a Afirka ta Kudu.

    Wannan ce taƙaddama ta baya-bayan nan tsakanin ƙasashen biyu.

    Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta soki Afirka ta Kudu kan batutuwa da dama da suka haɗa da manufofi da aka bijiro da su don magancenuna wariya.

    Trump ya ce manufofin suna nuna wariya ga farar fata ƴan Afirka ta Kudu. Tuni dai Afirka ta Kudun ta musanta waɗannan zarge-zargen.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce gwamnatin Afirka ta Kudu ba ta warware matsalolin da ta bayyana ba, kamar yadda ya faɗa cikin wata sanarwa da ke ƙunshe da matakin.

    Ya ce taƙaita bayar da bizar za ta shafi waɗanda ke tunzura wariyar launin fata.

    Sai dai Rubio bai fito ya bayyana sunan waɗanda matakin ya shafa ba.

  18. ADC ta zargi Tinubu da jefa ƴan Najeriya cikin halin ha'ula'i

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jam'iyyar hamayya ta African Democratic Congress (ADC) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da taɓarɓara tattalin arzikin ƙasar sakamakon tashin farashin mai da ya kai har ₦1,470 kowace lita.

    Jam'iyyar ta ce tashin farashin man ya janyo ƙaruwar farashin sufuri da abubuwan yau da kullum, lamarin kuma da ya ƙara jefa ƴan Najeriya cikin mawuyacin yanayi.

    A cewar Gidan Talabijin na Channels, wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran ADC, Bolaji Abdullahi, jam'iyyar ta ce ana jin raɗaɗin tasirin tashin farashin man har a kayan masarufi da sufuri da wutar lantarki da ilimi da sauran ɓangarorin rayuwa.

    "Shugaba Tinubu ya mayar da batun man fetur wani makamin gallazawa ga ƴan Najeriya. Kayan masarufi, sufuri, lantarki, ilimi da duk abubuwan da ƴan Najeriya ke nema don ci gaba da rayuwa na da alaƙa da farashin mai," in ji jam'iyyar.

    ADC ta kuma bayyana wasu rahotanni na makarantun kuɗi da suka ƙara kuɗin makaranta da kashi 30 zuwa 40, inda jam'iyyar ta ce hakan ya ƙara nuna yadda taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar ya yi ƙamari.

  19. Ɓarnar da Iran ta yi wa sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya

    ..

    Asalin hoton, CBS

    Kafar yaɗa labarai ta CBS ta saki wasu sabbin hotuna da ke nuna irin ɓarnar da aka yi wa gine-gine da motoci a sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya bayan da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa da Iran ta kai.

    Sojoji ne suka aikewa kafar ta CBS inda suka nemi a saka sunansu kasancewar akwai takunkumi kan yaɗa labarai a rundunar sojin Amurka.

    Ɗaya daga cikin hotunan da CBS ta samu daga sansanin sojoji na Prince Sultan a Saudiyya sun nuna yadda harin ya shafi bayan injin jirgi ƙirar Being A-3.

    ...

    Asalin hoton, CBS

    ..

    Asalin hoton, CBS

  20. Fitaccen jarumin Nollywood Olu Jacob ya rasu

    Olu Jacobs

    Asalin hoton, Olu Jacobs

    Iyalan ɗaya daga cikin fitattun ƴan fim a masana'antar fina-finai ta Nollywood, Olu Jacob sun sanar da rasuwarsa yana da shekara 84.

    Sun yi sanarwar ne da safiyar yau Laraba inda suka nemi jama'a da su yi wa mamacin addu'a.

    An jima rabon da a ga Olu Jacobs a bainar jama'a kuma a 2021 ne mai ɗakinsa Joke Silva, wadda ita ma fitacciyar ƴar Nollywood ce - ta bayyana cewa an gano mijin nata na ɗauke da cutar mantuwa.

    Cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa da lafiyar mutum, kamar yadda mai ɗakin nasa ta faɗa a wata hira da ɗan jarida Chude Jideonwo.

    Lokuta da dama a baya, an sha yaɗa labarin mutuwarsa amma iyalansa suka gaggauta ƙaryatawa, inda ko a shekarar 2024 ma sai da babban ɗansa Soji ya yi jawabi a talabijin don ya ƙaryata jita-jitar.

    Marigayin ya soma harkar fim ne a Birtaniya a shekarun 1970 inda ya haska a fina-finai kamar The Goodies, Till Death Do Us Part, Angels and The Tomorrow People.