Iran ta ce ta kai hari kan jirgin Amurka a mashigar Hormuz
Dakarun Juyin Juya Hali na Iran sun ce sojojin su sun kaiwa wani jirgi maras matuki na Amurka hari a daidai mashigar Hormuz.
Harin ya afku sa’o’i ƙalilan bayan rundunar sojin Iran ta yi barazanar ramuwar gayya, idan sojojin Amurka suka ci gaba da kaiwa jiragen ruwan Iran hari.
Gargadin ya biyo bayan harin da Amurka ta kaiwa tankokin man Iran 3 ranar Asabar. Amurka ta bayyana cewa hare-haren da ta kai na matsayin martanin harba makamai masu linzami da Iran ta yi kusa da jiragen ruwa na Amurka.