Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftanta da kuma sassan duniya na ranar Litinin 24 ga watan Agusta, 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Me ya sa malaman addini suka fara nuna inda suka karkata a siyasance?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A tsawon shekaru, malaman addini na daga cikin fitattun muryoyin da al'umma ke saurare a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar.

    Sai dai duk da tasirin da suke da shi a tsakanin mabiyansu, ba kasafai ake ganin ƙungiyoyin malaman addini suna fitowa tare da bayyana goyon bayansu ga wani ɗan siyasa ko jam'iyya ba.

    To amma sannu a hankan na hakan na neman sauyawa, domin kuwa a ƙarshen makon da ya gabata ne wata haɗakar ƙungiyoyin malaman addinin Musulunci ta arewacin Najeriya ta gudanar da wani taro a jihar Jigawa tare da bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.

    Haka kuma, a wani lamari da ya ja hankali, fitaccen malamin Musulunci Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce tasiri da martabar Sanata Abdul'aziz Abubakar Yari kaɗai sun isa Tinubu ya samu goyon bayan Arewacin Najeriya tare da tabbatar wa jam'iyyar APC nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

    Waɗannan batutuwa sun haifar da muhawara a tsakanin 'yan Najeriya, inda wasu ke ganin cewa malaman addini suna da 'yancin bayyana ra'ayinsu a matsayin 'yan ƙasa kamar kowa.

  2. Iran ta yi yunƙurin kashe ɗana - Netanyahu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Iran ta yi yunƙurin kashe ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza biyu, sai dai bai bayar da cikakken bayani kan lamarin ba.

    A wata hira ta wayar tarho da tashar talabijin ta Isra'ila Channel 14, Netanyahu ya shaida yadda abin ya faru.

    "Wani abin mamaki ya faru. Iran ta kai hari kan ɗaya daga cikin 'ya'yana. Iran ta yi yunƙurin kashe ɗaya daga cikin 'ya'yana."

    Netanyahu ya yi wannan ikirarin ne yayin wata muhawara da ta shafi rahotannin da ke cewa hukumar tsaron cikin gida ta Isra'ila, Shin Bet, ta ƙi samar da tawagar tsaro ga Gadi Eisenkot, tsohon babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar.

    Mista Netanyahu yana da 'ya'ya maza biyu da ɗiya mace ɗaya.

    Har yanzu ba a bayyana ko wanne daga cikin 'ya'yansa mazan ne aka yi yunƙurin kai wa harin ba.

    Babban ɗansa, Yair Netanyahu, mai shekara 35, yana zaune a birnin Miami na ƙasar Amurka tun farkon shekarar 2024, kuma rahotanni na cewa yana ƙarƙashin kariyar hukumar tsaron cikin gida ta Isra'ila.

  3. Baitil Malin Amurka ya sanar da sabbin takunkumai ga Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Baitul Malin Amurka, Scott Besant ya sanar da fannoni biyar da takunkuman ƙasar za su shafa, waɗanda suka haɗa da:

    • Kadarorin dijital
    • Fasaha
    • Zinariya
    • Sufurin jiragen sama
    • Jigilar kayayyaki ta ruwa

    Scott Besant ya kuma ce manufar wannan kamfe ita ce 'katse duk hanyoyin samun kuɗi da tallafin da ke ci gaba da raya gwamnatin Iran'.

    Besant ya ƙara da cewa Amurka ta bai wa kamfanoni da ƙungiyoyi wa'adin dakatar da mu'amalarsu ta tattalin arziƙi da Iran.

    A lokaci guda kuma, Ma'aikatar Baitul Malin Amurka ta yi magana kan matsa lamba ga duk wata ƙasar da take tallafa wa Iran.

  4. Za mu mayar da martanin da ya fi na baya tsanani - Iran

    Mai bai wa Jagoran addinin Iran shawara Mohammad Mokhbar, ya ce martanin da Iran za ta mayar kan matsin tattalin arzikin Amurka zai fi tsauri fiye da yadda aka saba gani a baya.

    Mokhbar ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce tsawon shekaru 47 da aka ƙaƙaba musu takunkumi, yaƙe-yaƙe da kuma ƙoƙarin raba kan Iran ba su cimma nasarar da aka yi niyya ba.

    Kalaman nasa sun zo ne gabanin sanar da sabon shirin Amurka na matsin tattalin arziki, wanda ake sa ran zai shafi ƙasashen da ke hulɗa da Iran ta fuskar tattalin arziki.

    Iran ta kuma yi gargadin cewa duk ƙasar da za ta taimaka wa Amurka wajen aiwatar da wannan matsin tattalin arziki za ta ɗauke ta a matsayin "maƙiya", kuma za ta mayar mata da martani.

  5. Trump ya tattauna da shugaban sojojin Pakistan ta waya

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar White House ta tabbatar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wata tattaunawa ta waya da shugaban sojojin Pakistan Asim Munir.

    Tattaunawar tasu na zuwa ne jim kaɗan kafin Munir ya tafi Tehran.

    Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta tabbatar da hakan ga BBC.

    Sai dai ba a bayyana ƙarin bayanai kan abin da shugabannin biyu suka tattauna ba.

  6. An kashe jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu

    An kashe jami'an wanzar da zaman lafiya biyu na Majalisar Dinkin Duniya, yayin da wasu bakwai suka jikkata bayan wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan ayarin jami'an a jihar Jonglei da ke gabashin Sudan ta Kudu.

    Ofishin MDD da ke Sudan ta Kudu ya ce ayarin na kan hanyarsa zuwa garin Pajut, wani babban gari a jihar Jonglei, lokacin da aka kai masa harin kwanton bauna.

    Majalisar ta ce cikin mutum bakwai da suka jikkata akwai jami'an wanzar da zaman lafiya uku, jami'an rundunar 'yan sandan Sudan ta Kudu biyu da kuma ma'aikatan farar hula biyu.

    Shugabar UNMISS, Anita Kiki Gbeho, ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa kai wa jami'an MDD hari abu ne da ba za a amince da shi ba.

  7. APC na sake nazarin jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu

    Abdulaziz Yari da Tinubu

    Asalin hoton, Abdulaziz Yari/FB

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sake nazarin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027, sakamakon ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan fitar da jerin sunayen da aka fitar.

    Wata majiya daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da ke cikin kwamitin ta tabbatar wa BBC cewa an umurci shugabannin jam'iyyar da fadar shugaban ƙasa da su sake duba jerin sunayen ne saboda kura-kuran da aka samu, ciki har da sanya sunayen wasu jami'an gwamnati da ake ganin bai dace su kasance cikin tsarin yaƙin neman zaɓen jam'iyya ba.

    Matakin ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan fadar shugaban ƙasa ta sanar da kwamitin mutum 223, inda aka naɗa tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari, a matsayin Darakta-Janar.

    Daga cikin sunayen da suka janyo tambayoyi akwai Betta Edu, tsohuwar ministar jin ƙai da rage talauci, wadda aka dakatar daga mukaminta a 2024 bayan zargin badakalar kuɗi.

    Akwai kuma wasu manyan ƴan jam'iyyar da ake ganin ya kamata su kasance cikin kwamitin amma babu sunayensu ba, ciki har da gwamnoni.

    Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, wanda ya jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Haka kuma babu sunan Festus Keyamo, wanda yana ɗaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a 2023.

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya jagoranci ɓangaren hulɗa da masu ruwa da tsaki a kwamitin 2023, shi ma ba ya cikin jerin farko.

    Sai dai majiyar ta shaida wa BBC cewa, duk da wannan umarnin, ba a janye naɗin Sanata Abdul'aziz Yari a matsayin Darakta-Janar ba, amma za a sake nazari domin yin gyare-gyare da sake fitar da sabon jerin sunayen.

  8. Ya kamata Abdul’aziz Yari ya sake tunani - Kwankwaso

    Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso

    Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FM

    Bayanan hoto, Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso

    Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Rabiu Kwankwaso ya soki lamirin jerin sunayen da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta fitar na waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu a 2027.

    A ranar Asabar ne aka fitar da jerin sunayen, inda tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari zai kasance shugaba, sai dai lamarin ya janyo muhawara a faɗin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Rabiu Kwankwaso ya ce jerin sunayen “abin damuwa ne ga mutanen Najeriya waɗanda ke cikin wahala a faɗin ƙasar”.

    Kwankwaso ya yi zargin cewa akwai matuƙar damuwa game da mutanen da aka sanya a jerin kasancewar an yi amfani da wasu shugabannin hukumomin gwamnati, kamar shugaban hukumar tara kauɗaɗen shiga ta ƙasar, Dr Zacch Adedeji da shugaban ofishin kasafin kuɗi na tarayya Tanimu Kurfi .

    Ya bayyana cewa “shugabancin muhimman hukumomin gwamnati na buƙatar mutane waɗanda ba su ɗaukar ɓangare, waɗanda kuma al’umma suka yarda da su.

    “Ina kira ga Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya amince ya jagoranci tawagar yaƙin neman zaɓen, ya yi nazari sannan ya sauya tunani,” a cewar Kwankwaso.

  9. Dawo da tallafin man fetur zai mayar da tattalin arzikin Najeriya baya – Idris

    Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Mohammed Idris

    Asalin hoton, Mohammed Idris/X

    Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Mohammed Idris, ya ce idan aka dawo da tallafin man fetur zai mayar da tattalin arzikin Najeriya baya cikin matsalolin da ta fuskanta a shekarun baya.

    A wata sanarwa ma'aikatar ta wallafa a shafinta na sada zumunta a ranar Litinin, ministan ya ce cire tallafin ya samar wa gwamnati da ƙarin damar kashe kuɗi a fannoni kamar ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da tsaro.

    Ya ce dawo da tallafin zai sake jefa ƙasar cikin matsi wajen yin kasafin kuɗi da ƙara wa gwamnati wani nauyi a kan kuɗaɗen da take da su.

    Ministan ya ce masu son a dawo da tallafin ya kamata su yi la'akari da abin da ƙasar za ta rasa wajen gudanar da wasu shirye-shiryen, inda ya ce tun bayan cire tallafin, gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun samu ƙarin kuɗaɗen da suka kai kusan naira tiriliyan 15.8 tsakanin Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.

    Ya ce an kashe kusan naira tiriliyan 6.47 kan manyan ayyukan more rayuwa, yayin da sama da naira biliyan 400 aka ware wa wasu shirye-shiryen tallafawa jama'a, ciki har da NELFUND, asusun saka hannun jari a gidaje da kuma shirye-shiryen rance ga 'yan ƙasa da 'yan kasuwa.

    "Shin mu dawo da tallafin man fetur, ko mu ci gaba da tallafawa shirin lamunin karatu ga matasan Najeriya?" in ji ministan

    Ya kuma tambayi masu suka tsarin "ko a dawo da tallafin ne maimakon ci gaba da ba jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin kuɗaɗen shiga, da kuma ci gaba da samun kuɗin gina hanyoyi, layin dogo, wutar lantarki da tsaro?"

    Ministan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su duba sauye-sauyen tattalin arzikin da za a ci gajiyar shi na dogon lokaci, yana mai cewa manufar ita ce gina tattalin arziki mai ƙarfi da zai iya samar da ci gaba mai ɗorewa.

  10. An yanke wa babban malamin Musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai

    Ahmed al-Sharaa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Syria Ahmed al-Sharaa

    Wata kotu a Syria ta yanke wa wani babban malamin addinin Musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun shi da laifin tayar da rikici da kuma amfani da muƙami ta hanyar da ba ta dace ba.

    A ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasar Bashar al-Assad, Ahmad Hassoun na daga cikin malaman Musulunci masu matuƙar tasiri.

    Wasu na masa laƙabi da ‘mai bakin reza’ saboda tsananin goyon bayansa ga gwamnati.

    Shi ne mutum na 10 a cikin manyan mutanen gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Basar al-Assad da aka yanke wa hukunci ƙarƙashin sabuwar gwamnatin da ta kama mulki bayan hamɓarar da Assad a watan Disamban 2024.

  11. Mun cika alƙawuran da muka ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta cika alƙawuran da ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, kuma ƙasar na gab da fara cin gajiyar matakan da aka ɗauka.

    A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar na sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar na 2027, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta sanya Najeriya a kan hanyar samun ci gaban tattalin arziki.

    "Babu shakka mun fito daga cikin duhun da muke ciki, kuma yanzu muna gab da girbar amfanin tattalin arzikin da zai amfani dukkan ƴan Najeriya," in ji Shugaba Tinubu.

    Ya ƙara da cewa yayin da ake tunkarar lokacin yaƙin neman zaɓen, gwamnatinsa na da nasarori da dama da za ta bayyana wa ƴan Najeriya.

    Ya ce za su fito da abubuwan da gwamnatinsa ta cimma domin ƙara wa al'umma fata da ƙarfafa musu gwiwa a sassan ƙasar.

    Tinubu ya kuma ce za su yi nasara kan dukkan masu ƙoƙarin mayar da Najeriya baya.

    Shugaban ya buƙaci dukkan mambobin kwamitin su yi aiki tuƙuru domin ganin jam'iyyar ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na Janairun 2027.

  12. Yariman Saudiyya zai tattauna da shugaban Faransa

    Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohamed Bin Salman da shugaban Faransa Emmanuel Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohamed Bin Salman da shugaban Faransa Emmanuel Macron

    Rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka na daga cikin manyan batutuwan da za su mamaye tattaunawar da shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman za su yi a birnin Paris a yau Litinin.

    Baya ga haka, Macron da Bin Salman za su jagoranci taron farko na sabuwar majalisar hadin gwiwar dabarun siyasa da tattalin arziki tsakanin Saudiyya da Faransa.

    Ana kuma sa ran bangarorin biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyi a fannonin da suka hada da lafiya da sufuri da makamashi.

  13. Ƴan awaren Mali sun sake sakin sojoji 20

    Azawad Liberation Front (FLA)

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar masu fafutukar ballewa daga arewacin Mali, wato Azawad Liberation Front (FLA), ta sake sakin wasu sojojin Mali 20 da ta yi garkuwa da su, wasu daga cikinsu sun shafe sama da shekaru uku a tsare.

    Ƙungiyar ta ce sakin sojojin ya biyo bayan musayar fursunoni, inda aka saki wasu fararen hula da hukumomin Mali suka tsare a babban birnin ƙasar, Bamako.

    Wani kakakin FLA ya ce wasu daga cikin sojojin da aka saki suna cikin “mummunan yanayi da ya taba jikinsu da tunaninsu”, bayan wasu daga cikinsu sun shafe kusan shekaru biyar a tsare.

    Sai dai rundunar sojin Mali ta musanta bayanin cewa mutanen da aka musanya da sojojin fararen hula ne.

    Wata majiyar tsaro ta ce a maimakon haka, an saki aƙalla mayakan FLA takwas ne.

    Sojojin da aka saki dai an kama su ne a lokuta daban-daban tun bayan barkewar rikicin Mali, ciki har da fadan da aka yi a ƙarshen watan Afrilu da kuma hare-haren haɗin gwiwa da FLA da ƙungiyar JNIM mai alaƙa da al-Qaeda suka kai a farkon watan Yuli.

    Sakin na baya-bayan nan ya zo ne bayan jerin musayar fursunoni da aka gudanar a Mali cikin kwanakin baya.

    A ranar 13 ga Agusta, an saki sama da sojoji 80 da aka tsare tun watan Afrilu, sannan bayan kwana uku aka sake wasu sojoji shida da suka samu raunuka.

  14. Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin daji

    Jirgin yaƙin sojin Najeriya

    Asalin hoton, NAF/FB

    Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ƙaddamar da wani shirin yaƙi ta sama a jihohin arewa maso yammacin ƙasar kan “ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka” da suka addabi yankin.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce yaƙin wanda ta yi wa laƙabi da ‘Hannun ƙarfe’ zai tallafa wa sojojin da ke kai samame ta ƙasa domin dawo da tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna, inda sojoji ke aiki ƙarƙashin shirin ‘Operation Fansan Yamma’.

    “Wannan shiri ya tabbatar da ƙoƙarin dakarun saman Najeriya wajen amfani da dabarun yaƙi ta sama da haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro wajen daƙile ayyukan ƙungiyoyin miyagu’.

    Haka nan a cikin wani saƙo na daban rundunar sojin Najeriya ta sanar da wani shiri na kawar da ƴan ƙungiyar Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi.

    A watan Mayu ƙungiyar IS a yankin Sahel ta yi iƙitrarin ɗaukar nauyin wasu hare-hare a jihohin Sokoto da Kebbi.

  15. Wa'adin da Amurka ta ɗiba kafin 'gallaza' wa Iran ya cika

    xxxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hafsoshin tsaron Pakistan, Field Marshal Asim Munir, zai kai ziyara Iran a yau domin kokarin farfado da tattaunawar da ta kakare tsakanin Tehran da Amurka.

    Zai kai ziyarar ne yayin da Amurka ke shirin sanar da karin takunkuman tattalin arziki kan Iran.

    Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana matakan a matsayin mafiya tsauri da girma da aka taba shirya wa wata kasa abokiyar gabar Amurka.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya yi watsi da barazanar, yana mai cewa alama ce ta rashin mafita da Amurka ke ciki.

    Iran tana nan yadda take, ko gezau, kuma tana ci gaba da barzanar kai hari kan duk wani jirgin ruwa da zai bi Mashigar Hormuz wanda ba ta ba shi izini ba.

    Sai dai kuɗin ƙasar ta Iran, wato Rial, ya faɗi zuwa mafi karancin matsayi a tarihinsa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

  16. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin (Monde tushen aiki) a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.