Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Laraba 7 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. 'Sojojin Eritrea sun shiga yankin Tigray'

    Rahotanni daga Habasha na cewa sojojin Eritrea sun shiga garin Adigrat da ke yankin Tigray, a arewacin kasar.

    An ga manyan motocin da ke dauke da dimbin dakaru sanye da kayan sojan Eritrea su na bi ta cikin garin a ranar Talata, lamarin da ya tayar da fargabar ɓarkewar sabon rikici mai tsanani a yankin.

    A makon da ya gabata, Habasha ta katse hulɗar diflomasiyya da Eritrea, tana zarginta da goyon bayan ƙawancen ƴan tawaye da ke yaƙi da dakarun gwamnati a yankunan Tigray da Amhara da Afar.

    Sai dai ministan yada labaran Eritrea, Yemane Gebre-meskel, ya musanta cewa Asmara ta tura sojoji zuwa Habasha.

    Ya ce rahotannin, wata dabara ce ta gwamnatin Addis Ababa domin neman hujjar kai wa Eritrea hari.

  2. Harin Rasha ya kashe mutum 24 a Ukraine

    Akalla mutane 24 aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon hare-hare ta sama da Rasha ta kai a sassa daban-daban na Ukraine.

    Jami’an ceto na ci gaba da laluben ɓaraguzan wani rukunin gidaje bene da aka lalata a garin Pryluky.

    Kawo yanzu an gano gawarwaki 18, ciki har da jarirai maza uku da kuma wani yaro dan shekara takwas.

    An kuma kashe mutum biyu a birnin Kremenchuk, da wasu biyu a Kyiv.

    A Kyiv, ‘yan sandan Ukraine sun ƙwance wani makami mai linzami na Rasha wanda bai fashe ba.

  3. Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP 25 a tafkin Chadi

    Sojojin Najeriya
    Bayanan hoto, Sojojin Najeriya na ci gaba da farautar mayaƙan ISWAP a yankin tafkin Chadi

    A Najeriya dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun dakile tare da hallaka ƴan ta’adda 25 yayin wani harin haɗin gwiwa da mayaƙan ISWAP suka kai ta kusurwoyi daban-daban a garin Kukawa na Jihar Borno.

    Lamarin ya faru a yankin tafkin Chadi da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda gungun mayaƙan ƙungiyar ISWAP ɗauke da makamai suka kai mummunan hari a sansanin Bataliya ta 101 ta dakarun soji na musamman.

    Sai dai dakarun Najeriya, tare da tallafin jiragen yaƙin sojin sama, sun yi ɓarin wuta a wajen tare da tarwatsa harin, da kuma tilasta wa sauran mayaƙan arcewa.

    Bayanan farko daga rundunar sojin Najeriya, ya tabbatar da hallaka mayaƙan ƙungiyar sama da 25, tuni aka gano gawarwaki 14 a filin, tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda shida da tarin alburusai.

    A na ta bangaren rundunar sojin ta rasa wasu daga cikin sojojin ta ya yin artabun, sun kuma sanar da bin sahun ƴanbindigar da suka tsere kewayen gabar tabkin Chadi.

    Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Malam Dauda Iliya ya tabbatarwa da BBC wannan hari.

    Masana sha'anin tsaro a Najeriya sun bayyana cewa wannan gagarumar nasara ta nuna irin ci gaban da aka samu a dabarun yakin haɗin gwiwa, inda musayar bayanan sirri da aiki tare tsakanin sojojin ƙasa da na sama ke hana ‘yan ta’adda damar samun walwala da kai hare-hare a yankin.

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarunta za su ci gaba da kai hare-haren kakkaɓe ƴan ta'addan tare da haɗin gwiwar sauran Jami'an tsaro, domin rusa sansanonin ISWAP gaba ɗaya da kuma kare al'ummomin yankin.

  4. Somaliya na shirin ta kwana kan ɓarkewar Ebola

    Ebola
    Bayanan hoto, Ana sa ido akan waɗanda suka kamu da cutar Ebola a cibiyoyin da aka killace su domin yaki da yaɗuwarta tsakanin al'umma

    Ma’aikatar Lafiya a Somaliya ta bayyana cewa an girke jami'anta a a wuraren shige da ficen ƙasar ta sama da ƙasa da ruwa cikin matsanancin shirin ko-ta-kwana, tare da umartar su da su ƙara sa ido musamman kan cutar Ebola, bayan da aka tabbatar da bullar cutar a maƙofciyar ta Kenya.

    Ma’aikatar ta ce tana bibiyar dukkan bayanai da rahotannin da suka shafi cutar tun lokacin da Kenya ta sanar da gano mutum na farko da ya kamu da ita a ƙasar.

    Babban Daraktan cibiyar binciken cutuka ta kasa Dokta Hussein Abuukar, ya shaidawa BBC cewa tuni suka shirya da shirya ma'aikatan gaggawa na hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa domin tabbatar da an gudanar da aikin cikin ƙwarewa.

    A ranar Litinin ne ƙasar ta Kenya ta sanar da mutuwar mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola, wanda ya shafe shekaru 7 a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

    Kimanin wata guda ya yi fama da rashin lafiya kafin a gano Ebola, kuma ya rasu a asibiti a birnin Nairo.

    Tuni aka killace mutum 57 da sukai mu'amala da shi inda ake sanya ido a kan su da yin gwajin cutar.

  5. NLC ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a Abuja

    NLC
    Bayanan hoto, NLC ta ce za a ci gaba da yajin aikin har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu.

    Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, ta ayyana yajin aiki n sai baba-ta-gani a fadin birnin Abuja, tare da umartar ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu su dakatar da dukkan ayyuka daga ranar 7 ga watan Oktobar 2026.

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwa ƙungiyar da aka gudanar a ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2026, kuma shugaban majalisar na Abuja, Knabayi Adalo, ya sanya wa hannu.

    NLC ta ce bayan cikar wa'adin ƙwanaki 7 da ta bai Gudanarwar Babban Birnin Tarayya ya ƙare, kan ƙorafe-ƙorafen da ba a warware ba game da ƙarin girma a wurin aiki ga ma'aikata da kuma sharuɗɗan aiki na malamai a makarantu Abuja.

    Ƙungiyar ta ce rashin magance waɗannan matsaloli da suka shafi malamai ne ya tilasta mata ɗaukar matakin shiga yajin aikin na sai baba-ta-gani.

    Majalisar ta umarci dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da su tattara mambobinsu domin tabbatar da sun bi wannan umarnin na tsunduma yajin aikin, tare da kafa kwamitocin sa ido da tabbatar da aiwatar da shi a faɗin Abuja.

    A ƙarƙashin wannan umarni, ofisoshi, makarantu, asibitoci, da sauran cibiyoyin gwamnati da ke Babban Birnin Tarayya za su kasance a rufe har sai an biya buƙatun da ƙungiyar ta gabatar.

  6. 'Iran ta aike wa Hezbollah tallafin dala miliyan 200'

    Kudi

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Tehran ta aike wa ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon tallafin dala miliyan 200 domin taimaka wa mutanen da yaƙin da Isra'ila ya raba da muhallansu.

    Reuters ya ambato wasu majiyoyi biyu da suka ce suna da masaniya kan yadda aka tura kuɗaɗen, sai dai ba ta bayyana sunayensu ko ƙasashensu ba.

    A cewar majiyoyin, ƙungiyar Hezbollah ta karɓi kuɗaɗen ne a watan da ya gabata, “a daidai lokacin da matsin tattalin arzikin da Amurka ke yi wa Iran ke ƙaruwa, kuma ake fuskantar ƙarin ƙalubale wajen tura kuɗaɗe zuwa Hezbollah.”

    Rahoton ya ce masu shiga tsakani sun karɓi kuɗin hidima na kashi 20 cikin 100 domin aiwatar da wannan hada-hadar, adadin da ya kai sau huɗu na abin da aka saba biya.

    A martanin da ya mayar wa Reuters, wani jami’in Hezbollah ya ce an tanadi wasu kuɗaɗe kuma za a sanar da yadda za a rarraba su nan da kwanaki masu zuwa, amma bai yi ƙarin bayani ba.

    Reuters ya ce zuwa lokacin wallafa rahoton, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, da wakilcin dindindin na Iran a Geneva, da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, da kuma gwamnatin Lebanon ba su mayar da martani kan buƙatar jin ta bakinsu ba.

  7. An sako masu bautar ƙasa 20 da ƴanbindiga suka sace a Imo

    yan yi wa kasa hidima

    Ɗalibai 20 da ƴanbindiga suka sace akan hanyarsu ta zuwa sansanin horas da su daga Owerri zuwa Onitcha a jihar Imo sun shaƙi iskar ƴanci, kamar yadda fadar Olubadan da ke Ladoja ta bayyana.

    Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka su na karɓar kulawar likitoci a Asibitin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ke Owerri.

    Mai ba wa Olubadan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Adeola Oloko, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

    Ya ƙara da cewa gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya tabbatar da sakin waɗanda aka sace ɗin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da sarkin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

    Masu shirin shiga hidimar ƙasa na daga cikin fasinjojin bas guda biyu da suka taso daga Ibadan a Jihar Oyo zuwa sansanonin horaswa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai musu hari tare da yin garkuwa da su a ranar 1 ga Oktoba.

  8. Hukumar alhazan Sokoto ta koka kan tsarin yin Fasfo

    Aikin Hajji
    Bayanan hoto, Hukumomin Alhazan Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2027

    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto ta bayyana cewa mayar da aikin bayar da fasfo na aikin Hajji zuwa Abuja da Legas ya zama babban cikas, inda ake ɗaukar makonni uku kafin a kammala aikin, maimakon mako guda kamar yadda aka saba a baya.

    Shugaban hukumar, Alhaji Aliyu Musa, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata a Sokoto kan shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2027.

    A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da sadarwa na hukumar, Faruku Umar, ya fitar, shugaban hukumar ya roƙi Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa da ya sake rarraba cibiyoyin bayar da fasfo zuwa jihohi, da cewa tsarin da ake amfani da shi yanzu zai haddasa jinkiri wajen shirye-shiryen aikin Hajji.

    Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta yi wa maniyyata aikin Hajjin 2027 su 3,058 rijista, ciki har da waɗanda aka ware musu daga cikin ƙarin kujeru 300 da Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta bai wa jihar kwanan nan.

    Ya ce waɗannan ƙarin kujerun na daga cikin kujeru 10,000 da Gwamnatin Saudiyya ta ƙara wa Najeriya, ita kuma Hukumar Alhazai Najeriya ta rabbasu ga jihohin ƙasar da kamfanonin shirya tafiye-tafiyen aikin Hajji.

  9. Hukumomin Nijar sun tabbatar da tsare ɗan jarida Mousa Kaka

    Ministan shari'a na jumhuriyar Nijar ya shaidawa wakilan ƙungiyar Reporters sans Frontiere da cewa dan jaridar ƙasar Moussa Kaka da ya bace sama da wata guda da ya gabata, ya na tsare a hannun jami'an tsaron ƙasar.

    Sai dai bai bayyana dalilin kama shi ko laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.Tuni ƙungiyar farar hula ta G-25 a Nijar ta bakin mai magana da yawunta Tahirou Garba ta fara tsokaci kan hakan.

    Tahirou ya shaidawa BBC daman tun lokacin da aka nemi Mousa Kaka aka rasa suka gudanar da bincike, kuma sun gano ya na tsare a hannun jami'an tsaro. Amma suka jami'an tsaro sukai ƙus da bakinsu.

    Sai dai Tahirou ya ƙara da cewa ''A yanzu mun san Kaka ya na hannunsu amma ba a bayyana inda ake tsare da shi ba, ko dalilin kama shi, babu wanda ya gan shi bare a tabbatar da cewa ya na cikin ƙoshin lafiya.

    Abin da mu ke buƙata shi ne a sako Mousa Kaka ya koma cikin iyalanshi tun da ba shi da wani laifi, bai kamata gwamnati ta kama ɗan ƙasarta ba tare da bayyana dalili ba.''

    Kimanin wata guda kenan ba a ji ɗuriyar fitaccen ɗanjaridar jamhuriyar Nijar ba, Moussa Kaka ba, wanda ya bar ofishinsa zuwa gidansa da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar 31 ga watan Agustan 2026.

    Tun daga lokacin, iyalansa da abokan aikinsa ba su samu damar tuntubar sa ba, yayin da ita ma motarsa ta ɓace.

    Bacewarsa ta tayar da hankalin ƙungiyoyin kare 'yancin 'yan jarida da na farar hula, waɗanda ke kira ga hukumomin Nijar da su bayyana inda yake da kuma tabbatar da lafiyarsa.

  10. Sojojin Eritrea na dannawa yankin Tigray na Habasha

    Mazauna garin Adigrat a yankin Tigray, sun shaidawa BBC dakarun Eritrea sun tsallako iyaka tare da nausawa kudancin ƙasar Habasha a daidai lokacin da faɗa ke ƙara ƙazancewa tsakanin dakarun gwamnati da ƴantawayen Tigray.

    Majiyoyi da dama sun bayyana cewa, sojojin Eritrea sun nausa garin Zalambesa da ke iyakar ƙasashen biyu, inda wasu jerin gwanon motocin sojpjin ke nausawa Adigrat su na nufar Edaga Hamus wani gari da ke tsakanin adigrat da Mekelle.

    Wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC, ya ga akalla tankokin yaki 40 dauke da sojoji kuma su ma su na nufar Adigrat. Ya kara da cewa a makonnin da suka gabata sojojin Eritrea a kusa da Qerseber, sa ke iyakar ƙasar da Habasha.

    Sai dai BBC ba ta tabbatar da batun dannawar dakarun ƙasar Eritrea zuwa yankunan ƙasar Habasha ba, sannan su ma hukumomi a can ba su yi ƙarin haske kan iƙirarin mazauna yankuna da ganau suka bayyana ba.

  11. An yanke wa matashi hukuncin kisa bayan kashe mahaifinsa a Kogi

    Kotu

    Wata babbar kotu a birnin Lokoja na jihar Kogi a Najeriya, ta yanke wa wani matashi mai suna Dahiru Yusuf Abba mai shekara 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da kashe mahaifinsa Dahiru Yusuf a yankin Sarkin-Noma a Lokoja a jihar Kogi da.

    Da ya ke bayyana hukuncin, mai shari'a M.M. Gwatana, ya ce an samu matashin da aikata kisan karkashin sashe na 221 na dokoin shari'ar jihar Kogi.

    A ranar 4 ga watan Oktobar 2024 ne aka kama matashin da gurfanar da shi gaban shari'a kan zargin aikata kisan kai da aikata mugun laifi.

    Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya cakawa mahaifinsa wuka a ƙirji da bayan shi bayan saɓanin da ya faru tsakaninsu, amma lauyoyinsa sun ce za su ɗaukaka ƙara.

  12. Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi umarnin daina kai dabbobi sassan Filato

    Fulani Makiyaya
    Bayanan hoto, Ana yawan samun tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da ƙabilun da ke jihar Filato

    Shugabannin Fulani a jihar Filato a arewa ta tsakiyar Najeriya, sun yi kira ga mambobinsu su dakatar da kai dabbobi zuwa kasuwar Bukuru da ke ƙaramar Bukuru, bayan harin da aka kai wa mutane da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama da jikkatar wasu.

    Wannan na ƙunshe cikin sanarwar da ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria ta fitar ranar 6 ga watan Oktoba 2026.

    Dakatarwar na zuwa ne bayan harin da aka kai wa makiyaya da motocinsu ɗauke da dabbobi akan hanyarsu ta zuwa kasuwar da waɗanda ke fitowa.

    Rahotanni sun ce a ranar Lahadin ƙarshen mako, ƴanbindiga sun buɗewa makiyayan da ke dawowa daga ƙaramar hukumar Bassa wuta, mutum niyu suka rasu wasu sha ɗaya suka jikkata.

    Ko a ranar 20 ga watan Satumba da ya gabata, ƴanbindiga sun kai hari kan makiyaya a yankin Kassa da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi tare da hallaka mutum biya da jikkata wani.

  13. 'Eritrea ta girke dakarunta a kan iyakar Ethiopia'

    Rahotanni daga yankin Tigray a arewacin Ethiopia na cewa, an girke dakarun Eritrea a kewayen garin Adigrat a ƴan kwanakin nan.

    Wani jami'in yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an ga manyan motocin dakon kaya ɗauke da dakarun da ke sanye da kakin sojin Eritrea a kan wata hanya mai tazarar kilomita 40 a kudu da iyakar Eritrea.

    An kuma ga wani ayarin motocin sojoji yana nufar garin Idaga Hamus, mai tazarar kilomita 20 da Adigrat.

    Tura sojojin na zuwa ne bayan da dakarun gwamnatin Ethiopia suka sake kwace Mekelle, babban birnin yankin Tigray, daga hannun 'yan tawayen Tigray a ƙarshen mako.

    Ethiopia ta zargi Eritrea da goyon bayan ƙungiyar TPLF, sannan ta yanke huldar diflomasiyya da Asmara a makon jiya.

  14. Fasinja ya rasu a jirgin Kenya Airways jim kaɗan kafin ya sauka a Legas

    ..

    Wani fasinja ya rasu a cikin jirgin Kenya Airways da ke tafiya daga Nairobi zuwa Legas, bayan ya daina motsi jim kaɗan kafin jirgin ya sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed.

    Kenya Airways ya ce lamarin ya faru ne jiya Talata da ƙarfe 9:20 na dare agogon Najeriya, kimanin mintuna 20 kafin jirgin ya sauka a Legas.

    Rahotanni sun ce ma'aikatan jirgin sun kai wa fasinjan agajin gaggawa tare da bin ƙa'idojin da aka tanada domin irin wannan yanayi.

    Jirgin ya sauka da ƙarfe 9:41 na dare, inda jami'an lafiya suka shiga jirgin. Bayan sun duba fasinjan, sun tabbatar da cewa ya rasu.

    Kamfanin jirgin bai bayyana sunan fasinjan ko musabbabin mutuwarsa ba.

    Kamfanin dai ya ce yana bayar da gudunmawa da yin aiki tare da iyalan mamacin, hukumomin Najeriya da kuma hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama.

  15. Hamas ta kira harin 7 ga Oktoba a matsayin 'babban abin tarihi'

    ..

    Hamas ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana harin 7 ga Oktoban 2023 da ta kai kan Isra’ila a matsayin "babban abin tarihi" a cikin abin da ta kira gwagwarmayarta da ke ci gaba.

    Sanarwar da aka danganta ga ƙungiyar, wadda kafofin yaɗa labaran Falasɗinu suka yaɗa, ta bayyana harin a matsayin "martani kan abin da ta kira wahalhalun da Isra'ila ta jefa Falasɗinawa ciki.

    Hamas dai ta ce har yanzu rikicin da ke tsakaninta da Isra’ila bai ƙare ba.

    Ƙungiyar ta zargi Isra'ila da aikata kisan ƙare dangi, zargin da Isra'ila ta musanta.

    Hamas ta kuma ce kusan Falasɗinawa 1,500 ne aka kashe a hare-haren Isra'ila tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoban bara.

  16. Kenya ta killace mutum 10 bayan Ebola ta halaka mutum na farko a ƙasar

    ..

    Jami'an lafiya a Kenya sun ce sun killace mutum 10 da suka yi mu'amala da wani mai cutar Ebola wanda ya mutu a Nairobi ranar Litinin.

    Ƙasar ta ƙara tsaurara matakan sanya ido bayan tabbatar da ɓullar cutar a karon farko da wani ɗan Kenya da ke zaune a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya kamu da ita.

    Mutumin ya koma gida ne ranar Asabar ta Uganda.

    Lamarin ya haifar da fargaba game da yiwuwar yaɗuwar cutar Ebola daga gabashin Congo, inda kawo yanzu cutar ta kashe fiye da mutum 4,000.

  17. Sojojin Mali sun ƙwace birnin Kidal daga ƴan awaren Abzinawa

    ..

    Gwamnatin Mali ta ce sojojin ƙasar sun ƙwace iko da birnin Kidal da ke arewacin ƙasar, kwana guda bayan wata ƙungiyar 'yan aware ta janye mayaƙanta daga birnin.

    Ƙungiyar 'Yantar da Azawad ta ce ta janye daga Kidal, birni mai muhimmanci ta fuskar dabarun yaƙi, bayan hare-hare ta sama da sojojin Mali suka kai tare da samun goyon bayan sojojin hayar Rasha.

    Ƙungiyar 'yan aware ta Abzinawa ta ƙwace iko da Kidal watanni shida da suka gabata, a lokacin hare-haren da ta kai a sassa daban-daban na ƙasar tare da mayaƙa masu iƙirarin jihadi.

    Daga cikin ƙungiyoyin akwai Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda a yankin.

  18. An kama matar tsohon shugaban Sri Lanka kan zargin almundahana

    ..

    Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na Sri Lanka sun kama tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar, Shiranthi Rajapaksa, bisa zargin wata ƙungiyar agaji da ke da alaƙa da ita ta karkatar da kuɗin da aka ware domin tallafa wa asibitin yara.

    Masu bincike na son yi wa matar tsohon shugaban ƙasar Mahinda Rajapaksa, mai shekara 73, tambayoyi dangane da gudummawar dala 30,000 da ƙungiyar agaji ta Siriliya Saviya ta tara domin sayen wata na'urar gwaji ta musamman da aka yi nufin bai wa wani asibitin gwamnati na masu fama da cutar kansa.

    Jami'ai sun ce tuni gwamnatin China ta bayar da irin na'urar a matsayin gudummawa.

    Sai dai Shiranthi Rajapaksa ta musanta aikata ba daidai ba, tana mai cewa ba a karkatar da kuɗin ba.

  19. Mene ne ke ruruta wutar rikici a jam'iyyar APC a Kano?

    ..

    Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya, na neman faɗawa cikin cikin gida a Jihar Kano da ke Arewacin ƙasar, ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar ke fatan samun ƙuri'u maso yawa a zaɓen da ke tafe.

    Takun saƙa da gugar zana da kuma shaguɓe na neman dabaibaye siyasar jihar, ko da yake rikici ne da ake yi a cikin duhu.

    Rikici ne da yake neman girmama tsakamin mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin da Ɗan Majalisar Tarayya na yankin Bichi, Abubakar Kabir Abba Bichi.

    Rahotanni sun ambato cewa, duk da cewa akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa tsakanin jiga-jigan siyasar biyu, amma lamarin ya ƙara tsami ne bayan da mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo ya yi wasu kalamai masu kama da jirwaye da kamar wanka a wani taro da ya gudana a Bichi.

    Garo ya bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda yake cewa duk wanda ya taɓa Abba Bichi sai ya ji su "ba a Bichi ba ko a Kabo ne".

    Wannan zance ya haifar da maida martani daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau Jibrin.

    A wani bidiyo na daban kuma an ga shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi na mayar da martani cikin kan masu ingiza rikicin da yake tsakaninsa da Sanatan.

    Ku shiga nan domin karanta labarin.

  20. Dole Iran ta rage inganta Uranium ɗinta don kawo ƙarshen yaƙi - JD Vance

    ..

    Mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Washington na ci gaba da tattaunawa da shugaban Iran da kuma ministan harkokin wajen ƙasar.

    Vance ya ce kawo ƙarshen yaƙin na buƙatar Iran ta rage yawan sinadarin uranium da take tacewa sosai, maimakon kawai ta yi alƙawarin rage shi nan gaba.

    A wata hira da Reuters bayan halartar taron yaƙin neman zaɓe na jam'iyyar Republican a Alaska, Vance ya ce Washington ba ta da tabbacin yadda Tehran za ta ɗauki matsaya a tattaunawar da ake yi kan shirinta na nukiliya.

    A cewar mataimakin shugaban Amurkan, babban makasudin yaƙin shi ne hana yaɗuwar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya.

    Vance ya kuma yi watsi da rade-radin cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2028, yana mai cewa a yanzu hankalinsa yana kan ganin jam'iyyar Republican ta yi nasara a zaɓukan tsakiyar wa'adi.