KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 20/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 20/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ba gaggawa nake don cimma matsaya da Iran ba - Trump

    Trump

    Shafin labarai na Axios ya rawaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ba gaggawa yake kan cimma matsaya da Iran ba.

    A cewar wakilin shafin, Barak Ravid, Mista Trump ya ce:

    "Sai mun ga abin da zai faru a farkon shekara mai zuwa."

    Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka gabata sun ce ana sa ran Mista Trump zai tattauna batun Iran yayin ganawarsa da shugabannin China da Rasha a taron ƙasashe uku da za a gudanar a Shenzhen.

  2. Amurka ta kashe dala biliyan 48 a yaƙin Iran - Pentagon

    Kudi

    Wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ya sanar a ranar Alhamis cewa kuɗin da aka kashe a yaƙin da ake yi da Iran yanzu ya haura dala biliyan 48 tun bayan da rikicin ya fara a ƙarshen watan Fabrairu.

    "Wannan adadi ya haɗa da kuɗin alburusai da, maye gurbin kayan aiki da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan soja," in ji mataimakin sakataren harkokin kuɗi na Pentagon, Arthur Miller.

    Ya bayyana hakan ne lokacin da Majalisar Dattawan Amurka ke zaman tantance shi don naɗa shi mataimakin sakataren Rundunar Ruwa mai kula da harkokin kuɗi.

    Sai dai wannan adadi bai haɗa da asarar da sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya suka yi ba, ko kuma makaman sojin da aka lalata a wuraren, waɗanda wasu daga cikinsu suka yi mummunar ɓarna sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da makamai masu linzami da Iran ta kai.

    Wannan ne karo na farko da aka fitar da sabon bayani kan kuɗin yaƙin tun tsakiyar watan Oktoba, lokacin da rundunar CENTCOM ta ce kuɗin da aka kashe ya kai dala biliyan 47.1.

    Bisa ga kimantawar da aka yi a baya, mafi yawan kuɗin da aka kashe, kimanin dala biliyan 29, sun tafi ne wajen maye gurbin alburusan da aka yi amfani da su.

    Haka kuma asarar kayan aiki, ciki har da jiragen sama da jirage marasa matuƙi, ta kai kusan dala biliyan 6 daga cikin jimillar kuɗin da aka kashe.

  3. An gina yaƙin Iran a kan ƙarya - Bernie Sanders

    Bernie Sanders

    Fitaccen ɗansiyasar Amurka na jam'iyyar Demokrats, Bernie Sanders ya ce yaƙin Iran da Amurka ke yi an gina shi ne a kan ƙarya.

    "An gina Yaƙin Vietnam bisa ƙarya. An gina Yaƙin Iraki bisa ƙarya. Haka kuma ana gina yaƙin da Iran bisa ƙarya," kamar yadda ya bayyana.

    Mista Sanders ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya yi a shirin podkast mai suna "The Diary of a CEO", wanda aka fitar a ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba.

    "Iƙirarin cewa gwamnatin Iran na shirin kai mana hari ƙarya ne... Na yi imanin cewa Netanyahu ya shafe shekaru 40 yana ƙoƙarin jawo Amurka cikin yaƙi da Iran, domin a tada zaune tsaye a ƙasar tare da raunana ta."

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a,

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.