KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 16/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 16/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Hamas ta tabbatar da kisan kwamandan sojinta a harin Isra'ila a Gaza

    Janaza

    Asalin hoton, AFPviaGETTY

    Ƙungiyar Hamas da sojojin Isra'ila sun tabbatar da kisan Izz al-Din Haddad, kwamandan rundunar sojin Hamas da aka fi sani da Qassam Brigades, a wasu hare-hare da Isra'ila ta kai Gaza ranar Juma'a.

    Isra'ila ta bayyana shi da ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

    Tuni dai aka gudanar da jana'izarsa yau a birnin Gaza.

    A lokacin hare-haren da aka kai da daddare an kuma kashe wasu daga cikin iyalan Haddad.

    Ƙungiyoyin bayar da agaji a Gaza sun ce aƙalla mutum bakwai ne suka mutu a lokacin hare-haren, yayain da gommai suka jikkata.

    Duk da cewa akwai yarjejeniyar dakatar da wuta tun watan Oktoban bara, gwamnatin Isra'ila na cewa tana da ikon kai hare-hare kan mambobin Hamas.

  2. 'Adadin ɗabilan da aka sace daga Borno sun kai 50'

    Wasu mahara

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan da ke fitowa daga Najeriya na cewa fiye da ɗalibai 50 ne aka bayar da rahoton garkuwa da su a wasu hare-hare da aka kai wa makarantu a yankin arewa maso gabashin ƙasar aranar Juma'a

    Rahotonni na cewa mafi yawan yaran ƴan tsakanin shekara biyu zuwa biyar ne, waɗanda aka sace daga makarantun nazare.

    Iyaye a ƙauyen Mussa na jihar Borno, na cikin zaƙuwar jiran bayanai game da yaran nasu.

    Kawo yanzu dai babau wanda ya ɗauki alhakin satar ɗaliban, yayin da rahotonni suka ce tuni wasu iyayen suka fara tsarewa daga ƙauyukan .

    Shaidu sun ce maharan na amfani da yaran a matsayin garkuwa domin guje wa hare-haren jami'an tsaro, bayan da suka tsere da su a kan babura.

  3. APC na gudanar da zaɓukan fitar da gwanin ƴan majalisar wakilai

    APC

    Asalin hoton, APC

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da gudanar da zaɓukan fitar da gwanin ƴantakarar majalisar wakilan ƙasar.

    Ana gudanar da zaɓukan ne a mazaɓukan ƙasar daban-daban, musamman a wuraren da aka kasa cimma maslaha wajen fitar da ƴantakara.

    Jam'iyyar ta tsara gudanar da zaɓukan ne domin tabbatar da adalci da ƴaƴanta da ke son yin takarar majalisar wakilan ƙasar.

    Sai a kwanaki masu zuwa ne za a gudanar da na ƴantakarar sanatoci da gwamnoni.

  4. Sayar mana makamai ne ƙashin bayan zaman lafiya yankin - Taiwan

    Wani babban jami'in gwamnatin Taiwan ya ce har kullum sayar wa da ƙasarsa makamai da Amurka ke yi, shi ne kashin bayan zaman lafiyar yankin, kuma hakan na cikin dokokin Amurka.

    Da yake magana da manema labarai a Taipei, mataimakin ministan harkokin waje na Taiwan ɗin ya kuma ce, dole ne tsibirin mai cin gashin kansa, ya kasance cikin shirin kare kansa.

    Jami'in ya yi kalaman ne, bayan taron ƙoli tsakanin Shugaba Trump da takwaransa na China, Xi Jinping.

    Trump ya dakatar da wannan shiri musamman a lokacin da ya koma daga taron ƙolin na China, ya nuna cewa yana ɗaukarsa a matsayin wata hanya ta yarjejeniya - kuma ba zai ce ko zai amince da shi ba.

    Ita dai China har kullum tana ɗaukar Taiwan a matsayin wani lardinta da ya bijire - kuma ba ta taɓa kawar da yiwuwar amfani da ƙarfi ba wajen dawo da shi ƙarashin ikonta ba.

  5. Abun Al-ajabin Zazzau ya janye daga takararsa ta majalisar wakilai

    Mahmud Sadis Buba

    Asalin hoton, Mahmud Sadis Buba/FB

    Dantakarar majalisar wakilan Najeriya mai wakilatar mazaɓar Sabon Garin Zariya a jam'iyyar APC, Mahmud Sadis Buba da aka fi sani da Abun Al'ajabin Zazzau ya janye takararsa.

    Cikin wata wasiƙar janyewar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abun Al-ajabin Zazzau ya sanar da janye takarar tasa ne nan take.

    Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da jagororin jam'iyyar APC da kuma iyalai da abokan arziki.

    ''Na ɗauki matakin ne domin haɗin kan jam'iyyarmu, na yi imanin cewa haɗa kai ƙarƙashin ɗantakara ɗaya shi ne zai bai wa jam'iyarmu nasara da ci gaban mazaɓarmu da ma jiharmu bakiɗaya'', in ji shi.

    Mahmud Sadis Buba

    Asalin hoton, Mahmud Sadis Buba/FB

    A makon da ya gabata ne Abun Al'ajabin Zazzau ya bayyana a gaban kwamitin tantance ƴantakara na jam'iyyar APC, aka kuma tantance shi domin tsayawa takarar majalisar wakiali.

    Sai dai bayan tantancewar an fara taƙaddama kan shekarunsa musamman a shafukan sada zumunta, inda aka yi zargin ya yi aringizon shekaru, saɓanin yadda yake bayyanawa.

  6. Iyalan El-Rufai sun zargi jami'an ICPC da hana su kai masa abinci

    El-Rufai

    Asalin hoton, El-Rufai

    Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir da ke tsare a hannun shukumar ICPC, sun yi zargin cewa jami'an hukumar sun hana su kai masa abinci.

    Cikin wata sanarwa da ɗansa, Hon. Muhammed Bello El-Rufai ya fitar ya zargi jami'an hukumar da hana mahimman haƙƙoƙinsa na ɗan'adam.

    ''Tun da farko sun hana likitansa ganinsa domin su tattauna sakamakon gwajin lafiyar da ya yi masa, suna cewa wai dole sai sun samu takardar izini daga shugaban ICPC'', kamar yadad Bello El-Rufai ya bayyana.

    Ita ma mai ɗakin El-Rufai, Aichatou El-Rufai wadda ta kai masa abincin, ta bayyana cikin wata hira da kafar yaɗa labaran DCL Hausa cewa jami'an hukumar sun hana ta shiga ofishin domin kai wa maigidan nata abincin.

    ''Kullum daidai wannan lokaci muke zuwa domin kawo masa abinci, amma yau ina zuwa suka ce wai ba zan shiga ba, an ba su sabuwar doka dakatar da kawo abinci daga ƙarfe 6:30 na yamma'', in ji shi.

    Kawo yanzu babu wata sanarwa daga hukumar ta ICPC game da wannan zargi.

    El-Rufai dai ya shafe watanni yana tsare a hannun hukumar - wadda ta kama shi bisa zargin aikata ba daidai ba, zargin da El-Rufai ya sha musanta.

  7. Isra'ila ta ce ta kai hari kan shugaban mayakan Hamas a Gaza

    Isra'ila ta ce ta kai hare-hare ta sama a Gaza inda ta nufi shugaban reshen mayaƙan Hamas, Izz al- Din al- Haddad ba - tana mai bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa hare-haren 7, ga watan Oktoba, kusan shekara uku da ta gabata.

    Ba a tabbatar da mutuwar Haddad a hukumance ba - daga Hamas ko hukumomin Isra'ila.

    Hukumomin agajin gaggawa a Birnin na Gaza sun ce harin na Isra'ila ya kashe aƙalla mutum bakwai, da raunata wasu gommai.

    Akwai dai yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a Zirin tun watan Oktoba, amma kuma Isra'ila, har kullum cewa take tana da damar kai hari kan mayaƙan Hamas.

  8. Amurka ta tuhumi wani ɗan Iraƙi da kitsa ta'addanci a Turai da Amurka

    Masu gabatar da ƙara a Amurka sun tuhumi wani ɗan ƙasar Iraqi da shirya hare-haren ta'addanci a faɗin Turai da nahiyar Amurka ta Arewa.

    Ana zargin Mohammad Baqer Saad Dawood al-Saadi, da kasancewa kwamandan wata ƙungiyar 'yan bindiga da Iran ke mara wa baya.

    Ana zarginsa da bayar da umarnin kai hare-hare a kan al'ummar Yahudawa a Belgium da Netherlands da Faransa da Jamus da kuma Birtaniya.

    An kama shi ne a Turkiyya, kafin a danƙa shi ga hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI.

    Mutumin mai shekara 32 ya bayyana ne a gaban kotun tarayya a manhattan kuma aka tsare shi - zaman waƙafi, kafin shari'ar.

    Lauyansa ya ce yana fuskantar shari'a ne ta siyasa kawai.

  9. Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya da na Amurka kan kisan Al-Manuki

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yaba wa abin da ya kira nasarar hare-haren haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasarsa da na Amurka wajen kisan mataimakin shugaban ISIS na duniya.

    Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar ranar Asabar ya ce harin da sojojin suka kai ranar Juma'a kan mayaƙan IS ya haifar da kisan Abu-Bilal Al-Manuki tare da wasu mayaƙansa.

    A cewar Tinubu, harin ya faɗa kan gidan Abu-Bilal Al-Manuki da ke yankin tafkin Chadi.

    “Ƙoƙarin sojojin Najeriya sun yi aiki tare da dakarun Amurka, wajen shirya harin haɗin gwiwa da ya haifar da mummunan ɓarna kan manyan jiga-jigan ƙungiyar ISIS.''

    Shugaba Tinubu ya gode wa Amurka kan goyon bayan da suke bayarwa a lamarin.

  10. Sojojin Najeriya sun tabbatar da kisan Abu-Bilal al-Manuki

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rudunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan Abu-Bilal al-Minuki, a wani harin haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasar da na Amurka.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rudunar sojin ta Najeriya Samali Uba ya fitar a yau Asabar, ya ce sun samu nasarar kai wani tsararren hari da muka shirya ƙarƙashin shirinta na yaƙi da ta'adanci da ya yi sanadiyar kisan Abu-Bilal al-Minuki, ɗaya daga cikin manyan mayaƙan ISIS kuma ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da ake da su a duniya."

    Ta ce an samu nasarar harin ne da taimakon haɗin gwiwa da tallafin haɗin gwiwar Amurka wajen musayar bayana shirri.

    "Tare da Amurka mun yi nasarar rusa gungun muggan yan ta'adda, da ke barazana ga rayukan ƴan Najeriya, da sauran ƙasashen da ke Afirka ta yamma."

    Sai dai rundunar sojin ta Najeriya ba ta sanar da inda aka kai harin ba.

    Rudunar sojin ta Najeriya ta danganta Abu-Bilal al-Minuki da hannu a sace ɗaliban makarantar ƴam mata da ke Dapchi, 2018, inda aka sace dalibai 100 a makarantar kwanan ta ƴanmata, da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda hakan ya jefa damuwa a faɗin ƙasar.

  11. Trump ya ce sojojin Amurka da na Najeriya sun kashe mataimakin shugaban IS na duniya

    sojojin Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump na Amurka ya ce dakarun ƙasarsa da na Najeriya sun kashe - mataimakin babban kwamandan ƙungiyar ISIS na duniya a wani hari na haɗin guiwa.

    A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka, ya ce, Abu-Bilal al-Minuki - wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a ISIS - na ɓuya ne a Afirka.

    ''Daga yanzu ba zai ƙara zama wata barazana ga sojojin Amurka da ƙasashen Afirka, ba kuma zai ƙara shirywa hari kan Amurkawa ba'', in ji shugaba Trump.

    Trump ya bayyana al-Minuki - a matsayin ɗan ta'adda lamba ɗaya, da mafi tasiri a duniya, kuma ya ce kawar da shi da aka yi, ayyukan ƙungiyar ISIS, na duniya za su ragu matuƙa gaya.

    ''Duk da cewa yana ɓoye a Afirka, bai san muna samun bayanan sirri game da shi ba'', in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya kuma godewa gwamnatin ta Najeriya kan haɗin gwiwar da suka yi wajen wannan aiki, sai dai bai bayar da wani ƙarin bayani ba baya ga haka ba.

  12. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da safiyar wanna rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu a sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa