Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 29 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Abdullahi Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. WHO za ta ci gaba da sa ido kan Uganda duk da ayyana ƙarshen cutar Ebola

    Ebola

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce za ta ci gaba da bibiyar halin da ake ciki a Uganda, duk da cewa hukumomin lafiyar ƙasar sun ayyana cewa ba a da mai ɗauke da cutar Ebola.

    Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido na tsawon kwanaki 42, wanda aka fara ƙirga daga ranar 16 ga watan da ya gabata lokacin da aka sallami mara lafiya na ƙarshe daga asibiti, bayan ya kamu da cutar da ya shigo da ita daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

    WHO ta ce ana ci gaba da gudanar da gwaje-gwaje da sauran matakan sa ido domin tabbatar da cewa cutar ba ta yaɗu tsakanin al'umma ba.

    A ranar Laraba ne Uganda ta sanar da cewa ba ta da wani mutum da ke ɗauke da cutar Ebola, bayan shafe makonni ba tare da samun sabon wanda ya kamu da cutar ba.

    Mutane 20 ne aka tabbatar sun kamu da sabon nau'in cutar Ebola tun bayan barkewarta a watan Maris. Cikin su, mutum biyu sun rasu, yayin da sauran 18 suka warke.

  2. Amnesty ta buƙaci a binciki kisan sojojin Mali 19

    Assimi Goita

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi kira da a gudanar da bincike kan kisan sojojin Mali 19.

    Amnesty ta ce lamarin na iya kasancewa laifin yaƙi.

    An kashe sojojin ne a ranar 19 ga watan Yuli bayan wasu masu ɗauke da makamai sun yi wa ayarin motocinsu kwanton ɓauna a yankin Gao.

    Amnesty ta ce binciken da ta yi kan wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna cewa maharan sun kama sojojin, suka ɗaure musu hannu a baya, sannan suka kewaye su kafin daga bisani su buɗe musu wuta.

    Wata ƙungiya mai iƙirarin jihadi ta Buzaye ce ta ɗauki alhakin kai harin.

    Ƙungiyar ta Amnesty ta ce dole ne a gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban shari'a idan aka same su da laifi.

  3. Jamus ta kare matakin mayar da ƴan Afghanistan gida

    Gwamnatin Jamus ta kare matakin da ta ɗauka na tasa ƙeyar wasu ƴan Afghanistan zuwa ƙasarsu, duk da cewa ba a samu wasu daga cikinsu da aikata wani laifi ba.

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Jamus ya ce gwamnati na da niyyar fara mayar da waɗanda aka samu da aikata laifuka zuwa Afghanistan, sannan ana iya ƙara sanya sunayen wasu ’yan ƙasar cikin jerin waɗanda za a mayar.

    Jirgin da ya tashi daga Jamus a ranar Talata ɗauke da ƴan Afghanistan shi ne na farko da aka tura tun bayan da ƙungiyar Taliban ta sake karɓar mulki a ƙasar.

    Matakin na daga cikin tsauraran matakan shige da fice da gwamnatin Jamus ke aiwatarwa kan baƙin haure da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba ko kuma waɗanda aka samu da aikata laifuka, wanda gwamnatin Shugaba Friedrich Merz ta amince da shi.

  4. Wani jirgin dakon man Amurka ya kama da wuta a tekun Mediterranean

    Mediterranean

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce wani jirgin dakon man Amurka ya kama da wuta a kusa da tashar jiragen ruwa ta Damietta da ke tekun Mediterranean.

    Kamfanin tsaron teku na Ambrey ya ce akwai yiwuwar wani jirgi maras matuƙi ne ya bugi jirgin, sai dai ya tabbatar da cewa babu wanda ya mutu ko ya jikkata a lamarin.

    Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da rikici ke ci gaba da ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

    A daren Talata, haɗakar sojojin Amurka da Saudiyya ta kai hare-hare kan wasu sansanonin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na mabiya Shi'a da Iran ke mara wa baya a Iraq.

    Wakiliyar BBC ta ce wasu mazauna Iraq na nuna damuwa cewa ƙasarsu na ƙara faɗawa cikin rikicin da ba sa so.

  5. An kashe dakaru huɗu a hare-haren Amurka da Saudiyya a Iraq

    Dakarun IRGC

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce an kashe jami’an rundunar juyin juya halin ta RGC guda huɗu a hare-haren da Amurka da Saudiyya suka kai a Iraq a daren da ya gabata.

    Kamfanin dillancin labarai na Mehr na Iran ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe: Ali Asghar Astaneh, Abolfazl Mottaqi, Morteza Akbari da Amir Abbas Dirhamforosh.

    A halin da ake ciki kuma, kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa an kai wasu daga cikin mutanen Iraq da suka jikkata a hare-haren zuwa wani asibiti da ke yammacin Iran, kusa da iyakar ƙasar, domin samun magani.

  6. Ƙungiyar Fulani makiyaya ta yi Allah wadai da harin ƴan bindiga a Kaduna

    Ƙungiyar makiyaya ta Kulen Allah Cattle (KACRAN) ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu mutane a ƙaramar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna.

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar makiyaya ta Kulen Allah Cattle (KACRAN) ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu mutane a ƙaramar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna.

    KACRAN da nuna damuwa kan ƙaruwar sace shanu, garkuwa da mutane da kuma hare-haren da ake kai wa manoma a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

    A cikin wata sanarwa da shugaban ƙasa na ƙungiyar, Khalil Mohd Bello, ya fitar, KACRAN ta bayyana hare-haren a matsayin abin takaici, rashin tausayi da kuma barazana ga samar da abinci da haɗin kan Najeriya.

    “Muna Allah wadai da waɗannan kashe-kashen na rashin imani da ake yi wa ƴan Najeriya waɗanda ke aiki a gonakinsu domin ciyar da iyalansu da ƙasa.”

    Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda wasu ke danganta duk wani laifi da ake aikatawa ga Fulani makiyaya, tana mai cewa hakan ba daidai ba ne.

    KACRAN ta ce makiyaya ma na daga cikin waɗanda suka fi shan wahala daga hare-haren ’yan bindiga, inda ta ce an sace shanunsu, an yi garkuwa da iyalansu, sannan an kashe da dama daga cikinsu saboda ƙin haɗa kai da masu aikata laifuka.

    “Ba daidai ba ne a kira duk wani Bafullatani ɗan bindiga. ’Yan bindiga ba su da ƙabila ko addini," in ji KACRAN.

    Ta yi kira ga ƴan bindiga da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da su daina aikata abin da suke yi su rungumi zaman lafiya da tattaunawa.

    Ta kuma roƙi gwamnatin tarayya ta yi amfani da tsarin zaman lafiya na ƙungiyar da suka haɗa da tattaunawar sulhu, kare wuraren kiwo da gonaki, tare da amfani da waɗanda suka tuba daga ayyukan ta’addanci wajen ƙarfafa wasu su rungumi zaman lafiya .

    KACRAN ta ce tana da yaƙinin cewa idan aka aiwatar da shirin kan gaskiya da kuma kyakkyawar manufa zai magance matsalar tsaro a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

  7. An kashe Iraniyawa biyar a harin Amurka da Saudiyya a Iraƙi

    Harin Amurka da Saudiyya a Iraƙi

    Asalin hoton, snntv

    Rahotannin sun ce akwai wasu Iraniyawa cikin waɗanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Saudiyya suka kai kan sansanonin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai masu goyon bayan Iran a Iraƙi a daren da ya gabata.

    Wasu jami’ai PMF biyu sun shaida wa AFP cewa an kashe masu ba da shawara na Iran biyar a wani hari da aka kai a lardin Diyala da ke tsakiyar Iraq.

    Kafofin yaɗa labaran Iran kuma a ɗazu sun ruwaito cewa an kashe sojojin Iran huɗu a hare-haren.

    A lokacin jana’izar waɗanda aka kashe a birnin Bagadaza, AFP ta lura cewa an lulluɓe akwatunan gawarwakin wasu daga cikinsu da tutocin Iran.

    Ƙungiyar PMF, wadda ake kuma kira Hashd al-Shaabi, ta ce bisa bayanan farko, akalla mambobinta 20 ne aka kashe, yayin da wasu 32 suka jikkata a hare-haren.

    Amurka da Saudiyya sun bayyana cewa sun kai hare-haren ne kan sansanonin ƙungiyoyin masu samun goyon bayan Iran a Iraq, a matsayin martani ga hare-haren da aka kai wa sojojin Amurka da kuma wasu wuraren samar da man fetur na Saudiyya.

  8. Gwamnati ta gano wuraren da ambaliyar ruwa za ta iya shafa a Abuja

    Abuja city gate

    Asalin hoton, X

    Hukumar agajin gaggawa ta birnin tarayyar Najeriya (FCTEMA) ta gano yankunan da ke cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa a Abuja

    Sakamakon hakan hukumar ta ƙaddamar da gangamin shirin wayar da kan jama’a domin rage illolin da ake sa ran ambaliyar za ta haifarwa a Abuja.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa matakin ya biyo bayan umarnin Ministan Birnin Tarayyar, Nyesom Wike, na ɗaukar matakan kariya tun da wuri domin magance matsalolin da ka iya tasowa sakamakon hasashen ambaliyar ruwa.

    NAN) ya ruwaito cewa an fara gangamin ne a ƙaramar hukumar Gwagwalada da wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a fadar Aguna na Gwagwalada, Muhammad Magaji.

    Jami'in hukumar Mark Nyam, ya ce ƙananan hukumomin Gwagwalada, tsakiyar birnin Abuja (AMAC), Kuje, Kwali da Abaji na daga cikin wuraren da ke buƙatar ɗaukar mataki sosai.

    Ya ce FCTEMA ta rubuta wa shugabannin ƙananan hukumomin Abuja shida takarda domin su tabbatar da inganta tsaftar muhalli.

    Ya ƙara da cewa zubar da shara a wuraren da ba su kamata da kuma rashin tsaftace magudanan ruwa akai-akai na daga cikin dalilan da ke haifar da ambaliyar ruwa.

  9. 'Ni da ƴan adawa sai dai mu yi kokawa' - Shugaba Tinubu

    Bayanan bidiyo, INEC na gudanar da ayyukanta bisa doron doka - Tinubu

    Yayin da yake jawabi ga jagororin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) a Abuja ranar Talata, Tinubu ya ce zai ce zai 'yi kokawa' da yan adawa a ƙasar.

    Tinubu ya kuma ce INEC na gudanar da ayyukanta bisa doron doka.

  10. Ƴan bindiga sun kashe masallata uku, sun sace mutane da dama a Sokoto

    Ahmed Aliyu Sokoto

    Asalin hoton, Ahmed Aliyu/FB

    Rahotanni sun ce ƴan bindiga sun kashe mutane uku a cikin wani masallaci, yayin da suka yi garkuwa da wasu da dama a ƙauyen Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun isa ƙauyen ne cikin gungu da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata, inda suka ci gaba da harbe-harbe har zuwa misalin ƙarfe 3:00 na asubahin Laraba.

    "Sun shafe sama da sa'o'i shida suna kai farmaki, sun kashe mutane, sun sace wasu, sun kwashe dabbobi, da wawure kayayyaki da kuma yin harbe-harbe ba kakkautawa," in ji mazauna yankin

    Sai dai wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce bayan ƴan bindigar sun bar yankin, mazauna garin sun gano gawarwakin mutane bakwai a safiyar Laraba.

    Ya bayyana cewa biyu daga cikin waɗanda aka kashe ƴan asalin Tsamaye ne, yayin da sauran biyar ɗin kuma ƴan gudun hijira ne daga wasu ƙauyukan da suka nemi mafaka a yankin.

    "Maharan sun kuma shiga shaguna da dama, inda suka kwashe kayayyaki, suka ƙone wata mota tare da banka wa wasu shaguna biyu wuta kafin su bar ƙauyen".

    Sai dai ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace ba, saboda da dama sun gudu zuwa cikin dazuka domin ɓuya.

    Jairdar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar na sane da faruwar lamarin, amma tana jiran cikakken bayani daga jami’anta da ke wurin.

    Ya ce har yanzu ba su samu cikakken rahoto kan abin da ya faru ba.

  11. Za mu yi wa Iran luguden wuta - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta kai "munanan hare-hare" kan Iran bayan harin makamai masu linzami da aka kai kan sansanonin sojojin Amurka da ke Jordan.

    Kafar yaɗa labarai ta Fox News ta ruwaito Trump yana cewa: "Za mu kai musu mummunan hari. Za su fuskanci hukunci mai tsanani."

    Trump ya kuma yi amfani da wata kalma mai zafi wajen jaddada barazanarsa, inda ya ce "Za mu yi musu luguden wuta."

    Fox News ta kuma ruwaito cewa Trump ya ce hare-haren sama da Amurka da Saudiyya suka kai kan ƙungiyoyin mayaƙan da Iran ke marawa baya a Iraq an gudanar da su ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin Iraq.

    Sai dai kalaman Trump ɗin na zuwa ne a daidai lokacin da fadar shugaban ƙasar Iraq ta yi Allah wadai da hare-haren na Amurka da Saudiyya inda ta ce keta ƴancinta ne.

  12. An garzaya da waɗanda suka jikkata a hare-haren Amurka da Saudiyya a Iraq zuwa Iran domin jinya

    Kafofin yaɗa labarain Iran sun ruwaito cewa an kai wasu daga cikin waɗanda suka jikkata a hare-haren sama da Amurka da Saudiyya suka kai kan wani sansanin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Iraq zuwa Iran domin samun kulawa ta musamman.

    Rahotannin sun ce an kwantar da waɗanda suka jikkatan a wani asibiti da ke yammacin Iran mai ingantattun kayan aiki, inda aka fara yi musu magani.

    Sai dai har yanzu ba a bayyana adadin waɗanda aka kai Iran ba da sunan asibitin da aka kwantar da su ko kuma halin da suke ciki.

    Tun da farko, Rundunar Tsakiyar Amurka (CENTCOM) ta sanar da cewa dakarun Amurka da na Saudiyya sun kai hare-hare na haɗin gwiwa kan sansanonin ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya a Iraq.

    Ƙungiyar PMF ta ce aƙalla mambobinta 20 ne suka mutu, yayin da wasu 32 suka jikkata sakamakon hare-haren.

  13. An ci gaba da sukar matakin Fifa kan sayar da hannayen jarin shirya wasanni

    Shugaban Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu ana ci gaba da nuna bacin rai game da shirin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, na sayar da hannun jari kan dala biliyan 20 don ci gaba da gudanar da wasannin da take shiryawa.

    Shugaban hukumar wasanin Turai ,Glenn Micallef ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa: ''Tsame hannun ku a wasanninmu''.

    Shugaban hukumar wasannin na Turai ya zargin FIFA da yunƙurin sayar da ƙwallon kafa kamar wata kadara, zai kuma gudanar da taron gaggawa kan hakan nan gaba a yau.

    Tsohon shugaban hukumar FIFA, Sepp Blatter, ya ce alaƙar kud-da-kud tsakanin shugaban FIFA, Gianni Infantino,da shugaba Trump na Amurka na zubar da kimar hukumar.

  14. Amurka ta ƙaƙaba sabbin takunkumai kan tankokin mai da kamfanoni masu alaƙa da Iran

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta sanar da ƙaƙaba sabbin takunkumai kan tankokin dakon mai takwas da kuma kamfanoni 10 da ake zargin suna da alaƙa da Iran.

    Kamar yadda sanarwar Ma'aikatar Kuɗi ta Amurka ta bayyana, shida daga cikin kamfanonin da aka ƙaƙabawa takunkumin suna da hedikwata a ƙasar China.

    An ɗauki wannan mataki ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da toshe mashigar ruwa a kudancin Iran, inda dakarunta suka dakatar tafiyar wasu jiragen ruwa.

    Sabbin takunkuman na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran "mummunan hari" idan tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin ta gaza samar da mafita.

  15. An naɗa kwamandojin sabbin rundunonin sojin Najeriya da aka ƙirƙiro

    Babban hafsan sojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar, Waidi Shaibu ya amince da naɗin sabbin kwamadojin sabbin rundunonin sojin ƙasar.

    A makon da ya gabata ne shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya amince da kafa sabbin rundunonin sojin ƙasar huɗu, lamarin da ya sa rundunonin ƙasar ƙasar suka ƙaru daga takwas zuwa 12.

    Janar Shu'aib ya ce nan ba da jimawa ba sabbin rundunonin za su fara aiki.

    Sabbin kwamandojin da aka naɗa sun haɗa da Manjo Janar Moses Gara da zai shugabanci sabuwar Runduna ta 5 mai shalkwata a Makurdi, da za ta kula da jihohin Benue da Nasarawa da kuma Kogi.

    Sai Manjo Janar Yakubu Yahaya da zai jagoranci Runduna ta 9 mai shalkwata a Ilorin, da za ta kula da jihohin Kwara da Neja.

    Sannan kuma Manjo Janar Chinedu Nnebeife da zai jagoranci Runduna ta 10 mai shalkwata a Jalingo da za ta kula da jihohin Taraba da Adamawa.

  16. Ƴanbindiga sun kashe mutum 13 a Benue

    Hoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ƴanbindiga suka kai hari wani garin manoma a jihar Binuwai da ke tsakiyar Najeriya.

    Lamarin na zuwa ne makonni bayan wasu hare-hare a kudancin jihar, inda aƙalla mutum 18 suka mutu, lamarin da ya haddasa zanga-zangar fusatattun mazauna yankin waɗanda suka koka kan abin da suka bayyana a matsayin ƙaruwar matsalar rashin tsaro.

    Shaidu sun ce sama da mutum 30 ɗauke da makamai, a kan babura ne suka kutsa cikin ƙauyen Efeyi da ke Ugboju a ƙaramar hukumar Otukpo ranar Talata, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa tare da amfani da adduna wajen sare mutane, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu.

    Sun kuma yi zargin cewa maharan makiyaya ne, waɗanda wasun ma sun taɓa zama a yankin a baya. Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan iƙirari.

    Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa ya ƙirga gawarwaki 13 da aka kai ɗakin adana gawa na asibiti.

    A cikin watannin baya-bayan nan, jihar Beneu ta sha fama da munanan hare-hare da suka janyo asarar rayuka.

  17. Iran ta yi watsi da tayin Oman na karɓe iko da mashigar Hormuz

    Mashigar Hormuz

    Asalin hoton, ..

    Iran ta yi watsi da tayin Oman na karɓe ikon gudanar da mashigar ruwan Hormuz ta hanyar haɗin gwiwa da Iran.

    Wani babban jami’in ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba cewa hakan ba za ta saɓu ba.

    Hakan ya dusashe fatan samun mafita ga taƙaddamar da ta janyo dakatar da harkokin kasuwanci a yankin Tekun Fasha na tsawon watanni.

    Oman ta gabatar da wata sabuwar yarjejeniya ga ƙasashen yankin domin warware rikicin da ya shafi wannan muhimmiyar mashigar ruwa.

    Sai dai Tehran ta ƙi amincewa da shirin Oman na gudanar da mashigar Hormuz tare da sauran ƙasashen yankin, tana mai cewa shirin ba shi da wata damar nasara.

    Jami’in ya shaida wa Reuters cewa Amurka da Saudiyya na ƙoƙarin matsa wa Oman lamba domin aiwatar da abin da ya kira “tsare-tsare marasa tushe na zahiri” game da wannan muhimmiyar mashigar ruwa.

    Ya ƙara da cewa Iran na nan daram kan matsayinta na cewa duk hanyoyin zirga-zirgar ruwa da ke cikin mashigar Hormuz, da kuma wani ɓangare na hanyoyin da ke fita daga gare ta, ya kamata su kasance ƙarƙashin ikon Iran.

  18. Amurka na neman yaƙi ya ƙazance - Iran

    Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, TASNIM

    Bayanan hoto, Mojtaba Khamenei

    Iran ta soki lamirin Amurka kan hare-haren da ta kai tare da haɗin gwiwar Saudiyya a ƙasar Iraqi, inda Iran din ta ce wani mataki ne na faɗaɗa rikicin da ake fama da shi a yankin.

    Iran ta yi wannan suka ne bayan wata ƙungiya mai goyon bayan Iran da ke samun mafaka a Iraqi ta ce an kashe mambobinta aƙalla 20 sanadiyyar hare-haren da Amurka da Saudiyya suka kai a cikin dare.

    Hare-haren da aka kai wa ƙungiyar na zuwa ne bayan Iran ta ce ta kai hari da makamai masu linzami kan wani sansanin sojin Amurka da ke Jordan.

    Amurka ta ce ta kakkaɓo makaman.

  19. An zargi Saudiyya da zartar da hukuncin kisa ba bisa ƙa'ida ba

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Yariman Saudiyya Mohammed bn Salman

    Ƙungiya mai rajin kare hakkin bil'adama, Human Rights Watch ta ce hukumomin Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa kan wasu ƴan asalin ƙasar Habasha biyar kan zargin safarar ƙwaya ba tare da bin matakan shari'a da suka dace ba.

    Ƙungiyar ta ce an zartar da hukuncin ne bayan wani zaman kotun da bai taka kara ya karya ba, wanda a wani lokaci ake yi cikin ƴan mintuna ƙalilan, ba tare da an samu lauyan da zai kare su ko kuma mai tafinta ba.

    HRW ta ce mutanen waɗanda aka zartar da hukuncin kansu a ranar Litinin ya sanya yawan ƴan Habasha da aka zartar wa hukuncin ya kai 17 a wannan shekara, yayin da wasu da dama ke cikin haɗarin fuskantar hukuncin na kisa.

    Hukumomin Saudiyya sun ce waɗanda aka zartar wa hukuncin an kama su ne da laifin safarar 'ganye', kuma an zartar da hukuncin ne domin ya zama darasi ga wasu.

  20. Jordan ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami biyar da Iran ta harba mata

    Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Jordan ya ce dakarun ƙasar sun kakkaɓo tare da lalata makamai masu linzami biyar da aka harba daga Iran.

    Sanarwar ta zo ne bayan rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta bayyana cewa ta daƙile dukkan makaman da Iran ta harba zuwa Jordan kafin su kai inda aka nufa.

    Tun da safiyar Laraba ne wasu kafafen yaɗa labarai na Iran suka fara ruwaito cewa an kai harin makamai masu linzami kan Jordan, yayin da mazauna wasu yankunan Iran suka ce sun ga makaman suna ratsawa a sararin samaniya.

    Har zuwa yanzu, hukumomin Iran ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.