Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 11/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 11 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Iran na gudanar da jana'izar manyan kwamandojinta
  • Kotu ta ba mu damar ci gaba da tsare El-Rufai - ICPC
  • Iran ta yi barazanar kai hari kan bankunan Amurka da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
  • An kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan wuraren Amurka a Iraq
  • Dangote ya rage farashin man fetur
  • Iran ta kai 'hari mafi muni' kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka
  • Amurka ta ce ta lalata jiragen Iran 16 masu sanya nakiyoyi a Hormuz
  • Za mu ɗauki duk wanda a fito zanga-zanga a matsayin maƙiyi - Iran
  • Me ya sa shugaban Iran ya nemi afuwar maƙwaftan ƙasar?

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Iran ta kai hare-hare a ƙasashen yankin Gulf

    Iran

    Asalin hoton, Isna

    Iran na cigaba da kai hare-hare a kasashen yankin Gulf a matsayin martani kan hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata.

    Oman ta ce an kai hari kan tankokin ajijyar manta da jirage marasa matuƙa. Tun da farko, an kai hari kan jiragen dakon man fetur guda uku, ciki har da mai ɗauke da tutar Thailand, wanda ya kama da wuta a lokacin da ya yi yunƙurin wucewa ta mashigar Hormuz.

    Tehran ta yi gargaɗin cewa babu jirgin da zai wuce ta mashigar, wadda hanya ce mai muhimmanci wajen kasuwancin man fetur a duniya.

  2. 'Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 600 a Lebanon'

    Lebanon

    Asalin hoton, STR/EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Isra'ila ta ce ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Iran da Lebanon. Ta ce an kai hare-haren ne kan ababen more rayuwa a fadin Iran, da kuma wuraren da kungiyar Hizbullah ta ke a Beirut babban birnin Lebanon.

    Wakiliyar BBC ta ce rundunar sojin Isra'ila ta ce wasu hare-harenta na baya-bayan nan, ta kai su ne kan dakarun Iran da ke shirin harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila.

    Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa, zuwa yanzu sun kashe kusan mutum dari shida tun bayan fara yakin.

    Cikin daren jiya Talata, sojojin Amurka sun ce sun lalata wasu jiragen ruwan Iran goma sha shida da ke sanya nakiyoyin karkashin ruwa a mashigar Hormuz, bayan da shugaba Trump ya gargadi Tehran kan sanya nakiyoyin.

  3. Yanzu ne za mu soma hare-harenmu bayan na ramuwar gayya - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta bayyana cewa ta kawo ƙarshen salon hare-haren mayar da martani, inda ta ce daga yanzu za ta fara kai hare-hare ne kai tsaye maimakon ramuwar gayya.

    Mai magana da yawun hedikwatar rundunar sojin Khatam al-Anbiya, Ebrahim Zolfaqari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce "Iran ta kawo ƙarshen salon hare-haren mayar da martani, yanzu luguden wuta ne kawai za ta riƙa yi."

    Iran ta kuma bayyana cewa ba za ta bari ko lita ɗaya na mai ya wuce ta mashigar Mashigar Hormuz ba domin isa ga Amurka da Isra’ila da kuma abokan hulɗarsu ba.

    Zolfaqari ya ƙara da cewa duk wani jirgin ruwa ko tankar mai da ke kan hanyar zuwa Amurka ko Isra’ila ko abokan hulɗarsu za a kai musu hari.

    Haka kuma ya ce a shirya ganin farashin gangar mai ya kai dala 200, yana mai cewa farashin mai yana da alaƙa da tsaron yankin da ya zargi waɗannan ƙasashe da lalatawa.

  4. Ministan tsaron Najeriya ya gayyaci manyan hafsoshin tsaro

    ....

    Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya gayyaci duka manyan hafsoshin sojin ƙasar zuwa ofishinsa kan ƙaruwar hare‑haren ƴanbindiga a baya-baya nan kan sansanonin soji a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    Taron wanda ke gudana a ma'aikatar tsaron ƙasar ya samu halartar babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Olufemi Oluyede, da babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Waidi Shaibu.

    Sauran sun haɗa da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sunday Aneke da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Idi Abass da wakilan Hukumar leƙen asiri ta Kasa (NIA) da wasu da dama.

    Rahotonni sun nuna cewa aƙalla manyan kwamandoji guda uku sun rasa rayukansu a hannun ƴanbindiga a Borno kwanan nan.

    Baya ga kwamandojin da suka mutu, dubban sojoji sun rasa rayukansu yayin da aka sace ɗaruruwan fararen hula.

    Gabanin fara taron, CG Musa ya ce sun yanke shawarar sake duba dabarun yaƙi da ‘yanbindiga duk da cewa rundunar.

  5. Me ya faru a kwana 10 na farkon yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ga wasu daga cikin jerin abubuwan da suka faru a kwana 10 na farkon yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran.

    • Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare a kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, inda suka hari cibiyoyin makaman nukiliya da shugabannin kasar.
    • Hare-haren sun kashe Jagoran Addinin Kasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya jagoranci kasar tun 1989.
    • Iran ta mayar da martani ta hanyar kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan Isra'ila da kasashen Gabas ta Tsakiya. Ta kira hare-haren Amurka da Isra'ila da “tsokana”.
    • Iran ta zargi Amurka da Isra'ila da kai hari wata makarantar yan mata, inda aka kashe mutum 168.
    • Amurka da Isra'ila ba su dauki alhaki ko musa hannunsu a harin ba
    • Kazalika, yakin ya ɗauki sabon salo bayan da Hezbollah ta kaddamar da hare-hare kan Isra'ila daga Lebanon.
    • Amurka da Isra'ila sun kaddamar da sabbin hare-hare a Iran, musamman kan wuraren ajiye mai.
    • An zabi Ayatollah Mojtaba Khamenei a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa a matsayin Jagoran Addini a ranar Lahadi.
  6. Iran na gudanar da jana'izar manyan kwamandojinta

    ....

    Asalin hoton, GETTY/ATTA KENARE

    Iran na gudanar da jana’izar wasu manyan kwamandojinta a Tehran waɗanda suka rasa rayukansu a hare‑haren da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a ƙasar.

    A cewar wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce gawarwakin manya sojojin waɗanda ta kira 'gungun mushahidan yaƙin Ramadan' za a binne su ne a 'maƙabartar mushahidai' ta ƙasar.

    Sanarwar ta ce daga cikin kwamandojin da suka rasu, akwai: Abdolrahim Mousavi, Shugaban Ma’aikatar Sojojin da Mohammad Pakpour, Kwamandan dakarunJuyin Juya Halin Iran da Ali Shamkhani, Sakataran Majalisar Tsaro da Aziz Nasirzadeh, Ministan Tsaro da Mohammad Shirazi, Shugaban Ofishin Kwamandan Sojojin da kuma Mohsen Darehbaghi da dai sauransu.

    Bugu da ƙari, al’umma da ke halartar jana’izar suna kallon wannan lokaci a matsayin rana ta tunawa da jarumtaka da sadaukarwa.

    Rikici dai na ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya a yayin da Iran da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai wa junansu hare-hare.

  7. An kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan wuraren Amurka a Iraq

    An kai hare-hare da jirage marasa matuƙa kan wasu wuraren Amurka a Iraq, ciki har da wani babban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagadaza a ranar Talata.

    Rahotanni sun ce harin bai jikkata kowa ba, kuma ana zargin ƙungiyoyin mayaƙa da Iran ke mara wa baya ne suka kai harin.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wani saƙon gargaɗi na cikin gida na Amurka da jaridun Washington da Reuters suka ruwaito.

    Jaridar Washington Post ta ce an harba jirage marasa matuƙa guda shida zuwa wurin, amma jami’an tsaro sun kakkaɓo guda biyar daga cikinsu.

    A arewacin Iraq kuma, an kakkaɓo aƙalla jirage marasa matuƙa guda uku a wajen birnin Erbil da ke yankin Kurdistan mai cin gashin kai, ba tare da samun rahoton asarar rai ba.

    Akwai wani sansanin sojojin Amurka kusa da filin jirgin saman Erbil, kuma birnin na daga cikin wuraren da hare-haren Iran da ƙungiyoyin da ke goyon bayanta suka fi kai hari a baya-bayan nan.

  8. Amurka ta ce ta lalata jiragen Iran 16 masu sanya nakiyoyi a Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta lalata jiragen ruwan Iran goma sha shida da ke sanya nakiyoyin ƙarkashin ruwa a mashigin Hormuz, wata hanya mai muhimmanci ta fitar da kashi 20 na makamashin da ake amfani da shi a duniya.

    Bataliyar rundunar sojin Amurkar da ke gabas ta tsakiya ta walafa wani bidiyo da ke nuna yadda ake kai wa jiragen hari tare da lalata su.

    Wannan ya zo ne bayan da Shugaba Trump ya gargaɗi Iran game da sanya nakiyoyi a mashigin da zummar hana zurga zurgar jiragen ruwa.

    Kafin hakan fadar White House ta karyata batun rakiyar wasu jiragen ruwa masu dauke da mai ta cikin mashigin na Hormuz, da sakataren Makamashin kasar Chris Wright ya wallafa cewa sojojin kasar sun yi.

  9. Iran ta kai 'hari mafi muni' kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wata sanarwa daga rundunar juyin juya halin Iran ta bayyana a shafin X.

    Sanarwar ta ce an harba makamai zuwa sansanin Al Udeid da ke Qatar, da sansanin Arifjan a Kuwait, da kuma sansanin Harir a Iraƙi.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran, ISNA, ya ce harin mai yawa da aka ƙaddamar ya kuma nufi rundunar ruwa ta biyar ta Amurka da ke yankin, inda aka ce wasu muhimman kayayyakin aikin sojojin Amurka sun lalace.

    A wani sako na daban, an bayyana harin a matsayin mafi girma kuma mafi muni da Iran ta kai tun bayan fara wannan rikici.

    Sai dai zuwa yanzu jami’an Amurka ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.

    A lokaci guda kuma an ji kuwwar na’urorin gargadi a sassa da dama na Isra’ila bayan wani sabon harin makamai masu linzami da Iran ta kai, wanda gidan talabijin na Isra’ila ya bayyana a matsayin mafi muni tun soma yakin.

    Isra’ila ta ce garkuwar tsaron sararin samaniyarta ta kakkabo makamai da dama.

    Rundunar juyin juya halin Iran ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar sadarwa ta tauraron dan adam a Haifa da ke arewacin Isra’ila, tare da wasu sansanonin soji.

    Iran ta kuma yi ikirarin kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka a yankin, ciki har da wurare a Kurdistan na Iraƙi da Bahrain, tare da rahotannin wasu hare-hare a Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya.

    Matakin Iran na faɗaɗa hare-haren zuwa ƙasashen da ke da alaƙa da Amurka na iya yin tasiri mai yawa ga tattalin arzikin duniya.