Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 26 ga watan Mayun 2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Isra'ila za ta faɗaɗa hare-harenta a Lebanon - Netanyahu

    ,

    Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa ƙasarsa na shirin ƙara tsananta hare-harenta a Lebanon.

    Wakilin kamfanin dillanci labarai na AFP a Nabatieh ya ce harin da aka kai ranar Talata ya janyo turnuƙewar hayaƙi a sassa da yawa na birnin.

    Kafar yaɗa labaran kasar ta ruwaito cewa daya daga cikin hare-haren an kai shi ne kusa da asibitin gwamnati kuma ya janyo mummunar barna a wasu yankunan asibitin.

    Isra’ila ta faɗaɗa hare-harenta zuwa Kudancin Lebanon, dakarun Hezbollah sun sanar da sun yi taho mu gama da dakarun Isra’ila da suka yi yunƙurin kwace birnin Nabatieh.

  2. Trump zai yi tattaunawar gaggawa da 'yan majalisar ministocinsa

    w

    Asalin hoton, TRump

    Rahotanni na cewa Shugaban Amurka Donald Trump zai yi wata tattaunawa da ba kasafai aka saba ganin irinta ba da ‘yan majalisar ministocinsa a gidan gona na Camp David a gobe Laraba.

    Gidan talabijin na Fox News ya tabbatar da duka ‘yan majalisar ministocin nasa ciki har da daraktan hukumar leƙen asirin kasar Tlsi Gabbard za su halarci tattaunawar.

    Tattaunawar na zuwa ne loakcin da gwamnatin Amurka ke duba yiwuwar fara amfani da matakin gaba na yajejeniyar da ake so a fadada tsakaninta da Iran.

    Kafafen yaɗa labaran Amurka sun rawaito cewa duka tattaunawar ana yi ne karkashin yarjejeniar tsagaita wutar da ba ta da tabbas.

  3. Aƙalla mutum 608 wani harin Isra'ila ya kashe a Lebanon

    Hukumar lafiya ta Duniya tace akalla an kashe mutum 608 a harin da Isra’ila ta kai Lebanon tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki.

    Wannan na zuwa ne lokacin da Ministan Lafiya na Lebanon yace adadin mutanen da aka kashe daga 2 ga watan Maris zuwa 26 ga watan Mayu ya kai 3,213 kuma 9,737 sun jikkata.

    Sojin Isra’ila su ma sun sanar da cewa dakarun Heboullah sun kai hari da wani jirgi maras matuki kan sojin Isra’ilan da ke Arewacin biranen Isra’ila tun bayan tsagaita wuta, kuma ya kashe sojoji 11.

    Sojojin Isra’ilan sun kaddamar da wasu sabbin hare-hare a fadin kasar ta Lebanon.

    Da yake zargin Hezboullah da kai hari kan sojin Isra’ila, Benjamin Netanyahu yace ya baiwa sojojinsa umarnin kai hari kan Hezboullah ta ko ina.

  4. PDP ta ayyana Sandy Onor ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027

    ,

    Asalin hoton, Sandy Onor

    Jam'iyyar PDP a Najeriya tsagen Wike da Abdurrahama Mohammed ke jagoranta, ta sanar da tsohon gwamnan jihar Cross River Sanata Sandy Onor a matsayin dan takarar shuganacinta na 2027, bayan sulhu da aka gudanar.

    Shugaban kwamitin da ya gudanar da zaɓen fitar da gwani kuma tsohon gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ne ya sanar da hakan, yayin tattara alkaluma zaɓukan fidda gwanin da aka yi a ranar Talata a hedikwatar jam'iyyar Wadata Plaza da ke Abuja.

    Mambobin kwamtin zaben fidda gwamanin sun ce an gudanar da zaɓukan ne ta hanyar tuntuɓa da kuma furta wanda ake so tsakanin mambobin jam'iyyar a faɗin jihohin Najeriya.

    Sanata Onor ya zama shi ne ya lashe zaɓen bayan bayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa ƙarƙashin jam'iyyar ta PDP, kuma ya sai fom kamar yadda kowanne ɗan takara wanda ya cancanta yake saya.

  5. Tarayyar Turai ta zargi Rasha ta yunƙurin ruguza dimokraɗiyyarta

    Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta zargi Rasha da yunƙurin ruguza dimokraɗiyyar ƙasashen Turai bayan da ta haddasa jin sautin ankararwar harin jirage marasa matuƙa a faɗin yankin Baltic.

    Ms von der Leyen na jawabi ne bayan ganawa da shugbannin ƙasashen Lithuania da Latvia da kuma Estonia a Vilnius, babban birnin Lithuania.

    Ziyarar na zuwa ne mako guda bayan da aka samu ankararwar harin jirage marasa matuƙa a birnin na Vilnius, inda aka buƙaci mutane su nemi mafaka.

    Ƙasashen yankin Baltic na zargin Rasha da karkatar jiragen Ukraine marasa matuƙa zuwa cikin yankunansu da gangan.

    A nata ɓangare Rasha na zargin ƙasashen da taimaka wa Ukraine wajen ƙaddamar da hare-haren.

  6. Mahajjata sun kammala tsayuwar Arfa

    Mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahajjata sun kammla tsayuwar Arfa, ƙololuwar ibada a aikin hajji.

    Mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka yi tsayuwar a wannan shekara

    mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan kammala tsayuwar Arfa, mahajjatan na wucewa zuwa filin Muzdalifa, inda a can ne za su yi jifa, har na tsawon kwanaki uku.

  7. Wani jirgin dakon mai ya kama da wuta a gaɓar ruwan Oman

    Jirgi

    Asalin hoton, Anatolia

    Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Birtaniya, UKMTO, ta ce wani jirgin dakon mai ya kama da wuta a kusa da gaɓar tashar jiragen ruwa ta Oman.

    UKMTO ta ce jirgin ba shi da tazara mai yawa da Muscat, babban birnin ƙasar Oman.

    Hukumar ta kuma ce jirgin da ma'aikatansa na cikin ƙoshin lafiya, to amma ta ce man da yake ɗauke ya fara malala a cikin tekun.

  8. Hotunan yadda Alhazai ke tsayuwar Arfa

    Mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Al'ummar Muslumi fiye da miliyan ɗaya da rabi ne ke tsayuwar Arfa, ƙololuwar ibada a aikin hajji

    Mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun da asubahin yau ne mahajjata suka riƙa tururuwa zuwa filin na Arfa.

    mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahajjata kan shafe tsawon wunin yau a filin na Arfa, domin gudanar da addu'o'i da sauraron huɗaba

    Mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

    Aikin Hajji ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci, wanda ake son kowane Musulmi ya yi idan ya samu hali.

    Mahajjata

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Za mu zafafa hare-hare kan Hezbollah - Netanyahu

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta soma ƙaddamar da jerin hare-hare a sassan Lebanon bayan sanarwar da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya yi cewa ƙasarsa za ta zafafa hare-harenta kan Hezbollah.

    Dakarun IDF sun ce sun kai hare-hare kan Hezbollah a Bekaa Valley da ke gabashin Lebanon da wasu yankunan ƙasar.

    Hezbollah wadda ke samun goyon bayan Iran ta ce ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare da jirage marasa matuƙa 22 da hare-haren jiragen roka inda ta ce waɗanda ta hara da hare-haren nata sune sojojin Isra'ila da tankokin yaƙi da barikin soji da gine-gine.

    A farkon watan nan ne, Lebanon da Isra'ila suka amince su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana 45 duk da cewa an ga yaƙi nan da can.

  10. Iran ta sake gargaɗin Amurka kan sabunta hare-hare a ƙasar

    Rundunar juyin juya hali ta Iran ta ce tana da ikon rama hare-haren da aka kai mata da suka saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta bayan da Amurka ta sabunta hare-hare kan cibiyoyin harba makamai masu linzami da wasu jiragen dasa nakiya.

    Sun kuma ce sun yi nasarar kakkaɓo wani jirgin Amurka mara matuƙi tare da harba jirgon yaƙi da ya ratsa sararin samaniyar Iran.

    Amurka ba ta tabbatar da iƙirarin na Iran ba.

    A kalaman baya-bayan nan da aka danganta da jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei ya yi gargaɗi cewa ƙasashen Gulf ba za su ci gaba da zama maɓoya ga Amurka ba.

  11. PDP ta tsayar da Pantami takarar gwamnan Gombe a 2027

    ...

    Asalin hoton, Abba Sani Pantami/FB

    Tsohon Ministan Sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu tikin takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar PDP bayan da ya koma cikinta.

    Ya yi nasarar ne lokacin zaɓen fitar da ƴantakara da aka yi yau a wani wajen taro a jihar Gombe.

    Shugaban kwamitin zaɓe na PDP, Hon Gregory Yenlong ne ya ayyana fitaccen malamin addinin a matsayin ɗantakara ɗaya tilo a wani.

    Da yake magana jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin wanda zai yi wa PDP takarar gwamna, Farfesa Pantami ya ce hidimta wa al'ummar Gombe ne ya sa yake neman kujerar gwamnan jihar.

    Ya yi alƙawari cewa idan har aka zaɓe shi a 2027, zai yi shugabanci bisa gaskiya da adalci.

    A halin da ake ciki, Pantami zai fafata da wasu ƴantakarar a zaɓen an 2027, ciki har da Jamilu Gwamna na APC mai mulkin jihar.

    Tun farko Farfesa Ali Isa Pantami ya janye daga takarar gwamna a APC bisa zargin 'maguɗi' da 'son rai' da ya ce sun saɓa da dokokin zaɓen Najeriya na 2026, kuma ya yi haka ne bayan tuntuɓa da kuma duba na tsanaki na yadda tsarin zaɓen fitar da gwanin yake.

    Da ma dai Farfesa Pantami ya shaida cewa bai aminta da sulhun da aka yi a baya ba, wanda ya fitar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ta Gombe kuma ya sha alwashin "yaƙar zalunci bisa doka".

  12. Kotu ta ce Jonathan zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027

    ,,,

    Asalin hoton, @GEJonathan/X

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta ce tsohon Shugaban ƙasar Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    A makon da ya gabata ne wani ɓangare na Jami'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya amince wa Jonathan ya yi wa jam'iyyar takara.

    Sai dai wani Johnmary Jideobi ya shigar da ƙara yana neman kotu ta hana Jonathan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    Wanda ya shigar da ƙarar tun farko ya nemi kotu ta hana INEC amincewa ko ma wallafa sunan Jonathan cikin jerin ƴan takarar shugaban ƙasa.

    Ya kuma buƙaci kotu ta fayyace ko Jonathan ya cancanci ya sake yin takarar shugaban ƙasa bisa tanade-tanaden sashe na 1(1), (2), (3) da 137(3) na Kundin tsarin mulkin Najeriya.

    Sai dai a hukuncin da ya yanke yau Talata, alƙali Peter Lifu ya ce Jonathan zai iya takara a zaɓen na 2027.

    Ya kuma buƙaci Jideobi ya biya tsohon shugaban Najeriyar tarar naira miliyan 20 sannan kuma ya biya tarar naira miliyan ɗaya ga babban atoni janar na Najeriya.

    Alƙali Lifu ya ce Jideobi ba shi da hurumin shigar da ƙarar kasancewar babu wata asara gare shi kan takarar Jonathan a zaɓen 2027.

  13. An zaɓi Ousmane Sonko a matsayin shugaban majalisar dokokin Senegal

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    An zaɓi Ousmane Sonko, mai shekara 51 a matsayin shugaban majalisar dokokin Senegal.

    A baya-bayan nan ne shugaban ƙasar Senegal Bassirou Faye ya sauke Sonko daga muƙamin Firaiminista tare da maye gurbinsa da Ahmadou Al Aminou Lo.

    Sonko dai ya maye gurbin El Malick Ndiaye da ya yi murabus ranar Lahadi.

    Sabon shugaban majalisar dokokin ya yi magana kan saɓanin da ke tsakaninsa da Shugaba Faye inda ya ce ba zai yi amfani da sabon muƙaminsa ba wajen yaƙar mutane kuma zai tabbatar da cewa majalisa ta yi aikinta bisa buƙatun ƴan ƙasa.

    Sonko ya kuma ce sauke shi da aka yi ba ya nufin siyasarsa ta zo ƙarshe.

    Sonko dai ya samu ƙuri'u 132 cikin 165 da aka kaɗa.

  14. Mutum 27 sun mutu sakamakon amai da gudawa a Borno

    ...

    Aƙalla mutum 27 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa a sassan ƙananan hukumomi biyar na jihar Borno.

    An ƙiyasta mutum 2,715 da ake zargi sun kamu da cutar.

    Takardar da ke ɗauke da ƙididdigar da aka turawa manema labarai ta ce an samu rahoton mutanen da suka kamu cikin kwana ɗaya kacal.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Jere inda mutum 834 suka kamu saii Mafa da aka samu mutum 159 sai Konduga mai 95, Monguno 56 sai Ngala mai mutum 2 da Magumeri da aka samu mutum 1.

    A birnin Maiduguri kuma an samu mutum 1,568 da suka kamu da cutar.

    Zuwa yanzu al'umma na fargabar bazuwar cutar musamman yayin da ake shirye shiryen babbar sallah.

  15. Sojoji sun kashe gomman ƴanbindiga a jihar Neja

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta kashe ƴanbindiga da dama tare da daƙile harin da mayaƙan suka shirya a wani jerin samame da ta kai jihar Neja tsakanin 20 da 23 ga Mayu.

    Mai magana da yawun rundunar Ehimen Ejodame ya ce an kai hare-haren ne a sassan ƙananan hukumomin Rafi da Mariga da ke jihar Neja.

    Ya ce "a ranar 20 ga Mayu, sojojin sama sun farwa wani taron ƴanbindiga a Tungan Bako da Kasuwan Daji a ƙaramar hukumar Rafi inda suka kashe ƴan ta'adda da dama tare da tarwatsa mahaɗarsu."

    A ranar 21 ga Mayu ne rundunar sojin saman Najeriya ta kai hare-hare kan ƴanbindiga a Tungunguna zuwa Uregi da ke ƙaramar hukumar Rafi.

    Sojojin saman kuma daga baya sun taimaka wa sojoji wajen daƙile ƴanbindiga tare da ƙwace iko da yankin Tungan Makeri da ke ƙaramar hukumar Borgu.

    Rundunar sojin saman a watannin baya-bayan nan ta tsananta kai samame kan ƙungiyoyin mayaƙa, lamarin da a wani lokacin ke shafar farar hula.

    An zargi sojoji ma a farkon watan da muke ciki da kashe farar hula 12 a wani hari da suka kai kan Neja sai dai sun musanta lamarin inda suka ce hare-haren sun halaka fiye da ƴanbindiga 70.

    Neja dai tana fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan miyagu da ƴnbindiga har ma da rikici tsakanin manoma da makiyaya.

  16. Shugaba Faye ya naɗa sabon Firaiminista don maye gurbin Sonko

    ..

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya naɗa Ahmadou Al Aminou Lo a matsayin Firaiminista don maye gurbin Ousmane Sonko, mutumin da ya taimaka wa Faye yin nasara a 2024 amma ya sallame shiranar 22 ga watan Mayu bayan shafe tsawon watanni ana takun saƙa tsakaninsu.

    Sakataren Fadar Shugaban ƙasa Oumar Samba Ba ya ce shugaban ƙasar ya zaɓi tsohon ma'aikacin babban bankin ƙasar saboda ƙwarewarsa a batutuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma biyayya.

    Lo mai shekara 60, tsohon sakatare janar ne na ƙungiyar manyan bankunan ƙasashen yammacin Afirka kuma minista a fadar shugaban ƙasa mai sa ido da kuma tafiyar da manufar sauye-sauye ta gwamnati.

    Ba ya ce Faye ya umarci sabon Firaiministan da ya kafa majalisar ministoci ba tare da ɓata lokaci ba.

    Naɗin nasa na zuwa ne sa'oi kafin Majalisar Dokoki ta ƙasar ta yanke shawarar duba yiwuwar naɗa Sonko a matsayin shugaban majalisa da maido da shi kan muƙaminsa.

    Matsayin ya kasance babu kowa a kai bayan da makusancin Sonko El Malick Ndiaye ya yi murabus daga muƙamin shugaban majalisa a ranar 25 ga watan Mayu.

    Sonko ya nemi Faye ya tsaya takarar shugaban ƙasa bayan da aka haramtawa Sonko yin takara saboda laifin ɓata suna da aka same shi da shi amma an samu saɓani tsakanin mutanen biyu kan tattalin arzikin ƙasar.

  17. Kotu za ta yanke hukunci kan makomar Jonathan ta yin takara a 2027

    ..

    Asalin hoton, @GEJonathan/X

    Yau ake sa rai babbar kotun tarayya a Najeriya za ta yanke hukunci kan ko tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai iya yin takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    Wani ɗan Najeriya, Johnmary Jideobi ne ya shigar da ƙarar a kotu inda yake neman kotu ta dakatar da tsohon shugaban ƙasar daga komawa kan kujerar shugabancin ƙasar.

    Wanda ya shigar da ƙarar ya ce ya shigar da ƙarar ce saboda a halin da ake ciki Jonathan ya karɓi rantsuwar kama aiki sau biyu kafin wa'adin shugabancinsa ya ƙare a 2015.

    Yana neman kotu ta yi ƙarin haske kan sashe na 1 da 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 kan cancantar tsayawa takarar shugaban ƙasa da kuma shekarun da aka ƙayyade na wa'adin mulkin.

    Ƙarar kuma na neman a hana hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC karɓa ko wallafa sunan Jonathan cikin jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

    An shigar da ƙarar ce yayin da wani tsagi na Jam'iyyar PDP ke ƙoƙarin ganin Jonathan ya shiga takarar bayan rahotanni da ke cewa sun amince ya tsaya takara ba tare da hamayya ba.

  18. Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran

    Jirgin Yaƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Kudancin Iran da suka shafi cibiyoyin harba makamai masu linzami da jiragen ruwa da ke ƙoƙarin dasa nakiya.

    Farmakin na Amurka an kai su ne da nufin kare kai don kare dakaru daga barazanar sojojin Iran, in ji cibiyar ayyukan soji ta Amurka.

    Kakakin cibiyar, Kyaftin Tim Hawkins ya ce sojojin Amurka "na ci gaba da kare dakarunmu yayin da suke taka tsantsan a lokacin tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu".

    Iran zuwa yanzu ba ta mayar da martani kan hare-haren na Amurka ba. Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baqai tun farko ya ce an samu ci gaba a wasu fannonin na tattaunawar da aka yi don kawo ƙarshen yaƙin, ba lalle a cimma yarjejeniya nan kusa ba.

    Zuwa yanzu ba a san tasirin hare-haren kan yiwuwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ba.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce akwai yiwuwar a iya cimma yarjejeniya inda ya yi nuni da tattaunawar ranar Talata tsakanin babban jami'in tattaunawa kuma ministan harkokin wajen Iran da Firaministan Qatar.

  19. Maraba

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.