Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 24/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 24/07/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. China da Rasha sun yi min alƙawarin ba za su sayar wa Iran makamai ba - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugabannin China da Rasha, Xi Jinping da Vladimir Putin, sun yi masa alƙawarin cewa ba za su sayar wa Iran makamai ba.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Xi ya tabbatar masa a ganawarsu ta baya-bayan nan a Beijing cewa China ba za ta bayar ko ta sayar wa Iran makamai ba a kowane hali, har da kamfanonin ƙasar.

    Trump ya ƙara da cewa shi ma Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi masa irin wannan alƙawari.

    Ya ce Putin ya fahimci cewa Amurka ba ta sayar wa Ukraine makamai kai tsaye, sai dai ga ƙasashen ƙungiyar NATO, waɗanda ke biyan cikakken kuɗinsu.

    "Kasashen biyu da aka fi dangantawa da Iran, ba na tsammanin suna da hannu. Kuma idan suna da hannu, hakan ba zai kasance cikin maslaharsu ba," in ji Trump.

    A baya-bayan nan kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa hukumomin leƙen asirin Amurka na binciken yiwuwar Rasha ta taimaka wa Iran bayan hare-haren jirage marasa matuƙa da aka kai kan wasu cibiyoyin CIA a yankin Tekun Fasha.

  2. Netanyahu zai gana da Trump a Fadar White House ranar Talata

    Netanyahu da Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin Firaministan Isra'ila ya sanar dacewa Benjamin Netanyahu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump a Fadar White House ranar Talata.

    Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake cewa alaƙar shugabannin biyu ta ɗan yi tsami kan batun yaƙin da ake yi da Iran da sanya hannu kan yajejeniyar nukiliyar Saudiyya.

    A cikin wata sanarwa, ofishin Netanyahu ya ce firaministan zai bar Isra'ila zuwa Washington ranar Litinin domin wannan ziyara.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, baya ga ganawarsa da Trump, Netanyahu zai kuma halarci jana'izar Sanatan Amurka Lindsey Graham, wanda ya bayyana a matsayin abokin Isra'ila.

    Ana sa ran ganawar za ta mayar da hankali kan batutuwan tsaro da kuma rikicin da ke ci gaba da ƙamari a Gabas ta Tsakiya.

  3. Masar ta yi Allah wadai da hare-haren Iran a Bahrain da Jordan da Kuwait

    Masar

    Asalin hoton, Getty Images

    Masar ta yi Allah wadai da hare-haren da Iran ta kai kan Bahrain da Jordan da Kuwait, inda ta ce hakan keta hurumin waɗannan ƙasashe ne tare da ƙara rura wutar rikicin da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin.

    A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar, ta ce hare-haren sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma kundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Sanarwar ta fito ne kusan awa guda bayan tattaunawa ta waya tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Masar Badr Abdel Ati.

    Masar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Bahrain da Jordan da Kuwait, kuma ta ce za ta mara musu baya kan duk wani mataki da za su ɗauka domin kare kansu.

    Ta kuma bayyana adawarta da kai hari kan cibiyoyin fararen hula da muhimman kayayyakin more rayuwa, ko kuma duk wani mataki da zai jefa rayuwar fararen hula cikin haɗari.

    A yau Juma'a ne rundunar IRGC ta Iran ta sanar da cewa ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait da Bahrain, yayin da a jiya Alhamis kuma wasu hare-haren jirage marasa matuƙa suka sauka a iyakar Kuwait da Iraƙi.

  4. Kotu a Afirka ta Kudu ta dakatar da yunƙurin tsige Shugaba Ramaphosa

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, FRENNIE SHIVAMBU/GALLO IMAGES VIA GETTY IMAGES)

    Wata babbar kotu a lardin yammacin Cape na Afirka ta Kudu ta dakatar da yunƙurin majalisar dokokin ƙasar na tsige Shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa kan zarge-zargen rashin ɗa'a da ake yi masa.

    Hukuncin da kotun ta yanke a ranar Juma'a ya bai wa Ramaphosa umarnin wucin gadi da ya hana majalisar ci gaba da ɗaukar matakan tsige shi har sai an kammala shari'ar da ya shigar yana ƙalubalantar rahoton kwamitin bincike.

    Rahoton kwamitin ya ce akwai hujjojin da ke nuna shugaban yana da tambayoyin da zai amsa dangane da satar kuɗaɗe da aka yi daga gonarsa ta Phala Phala a shekarar 2020.

    Lamarin ya shafi satar dalar Amurka 580,000, kuɗin da Ramaphosa ya ce an samu ne daga sayar da wasu shanun dawa, amma masu sukar sa sun yi tambaya kan dalilin da ya sa aka ajiye makudan kuɗin a cikin kujera a gidansa.

    Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a Afirka ta Kudu tun bayan da aka samu labarin batun.

    Tun da farko, Kotun Tsarin Mulkin ƙasar ta yanke hukuncin cewa Majalisar Dokoki ba ta bi ƙa'ida ba lokacin da ta yi watsi da rahoton kwamitin binciken, inda ta umarce ta da ta sake fara shirin tsige shugaban.

    Bayan wannan hukunci ne aka kafa kwamitin da zai gudanar da aikin tsige shugaban, sai dai Ramaphosa ya garzaya kotu yana neman a dakatar da aikin har sai an yanke hukunci kan ƙarar da ya shigar.

    Ramaphosa ya musanta aikata wani laifi, inda ya ce kuɗin da aka sace daga gonarsa ba kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya ba.

    Shugaban dai na ci gaba da samun goyon bayan jam'iyyarsa ta African National Congress (ANC), wadda ke jagorantar gwamnatin haɗaka ta ƙasar.

    Har yanzu ba a san yadda sauran jam'iyyun da ke cikin gwamnatin haɗaka za su kaɗa ƙuri'a ba idan aka ci gaba da shirin tsige shugaban, sai dai ANC na da isassun mambobi a majalisa da za su iya hana tsige shi.

    An fara rikicin ne a watan Yunin shekarar da ta gabata bayan tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta Afirka ta Kudu, Arthur Fraser, ya shigar da ƙara ga 'yan sanda yana zargin Ramaphosa da ɓoye satar miliyoyin daloli daga gonarsa ta Phala Phala.

  5. Sojoji Najeriya sun kama mutum biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Yobe

    Dakarun Operation Hadin Kai

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun Operation Hadin Kai na rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar maharba sun kama wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙauyen Jegalari da ke ƙaramar hukumar Fune a jihar Yobe.

    Muƙaddashin jami'in yaɗa labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Mohammed Goni, ya ce an gudanar da wani samame a ranar Alhamis 23 ga watan Yulin 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargin.

    "Dakarun Bataliya ta 233 da ke sansanin soji na Damaturu ne suka gudanar da samamen bayan samun ingantattun bayanan sirri kan ayyukan waɗannan da ake zargin," in ji nsanarwar da ya fitar

    Nigerian Army

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Ya ce dakarun sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda uku ƙirar gida, da bindiga pistol guda ɗaya da alburusai iri-iri da kuma wayoyi guda huɗu

    Sanrwar ta ce a halin yanzu waɗanda ake zargin suna tsare a hannun sojoji tare da kayan da aka ƙwato domin ci gaba da bincike da kuma tantance rawar da suka taka a ayyukan garkuwa da mutane da sauran laifuka.

    Nigerian Army

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar ta ce za ta ci gaba da ƙaddamar da hare-haren domin hana ƴan ta'adda da sauran masu aikata laifuka samun damar gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas.

  6. Ya kamata ƴan adawa su daina ɓata sunan Najeriya a idon duniya - Matawalle

    Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle

    Asalin hoton, Matawalle/X

    Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya buƙaci ƴan adawa da su daina yin abubuwan da ka iya tunzura ƴan Najeriya ko kuma ɓata sunan ƙasar a idon duniya.

    A cikin wata sanarwa da kakakinsa Ahmad Dan-Wudil ya fitar, Matawalle ya ce abin takaici ne yadda ake zargin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ɗauki hayar kamfanonin kamun kafa na ƙasashen waje domin yaɗa tsofaffin takardu da suka shafi Shugaba Bola Tinubu a Amurka.

    Ya ce hakan sam ba ya amfanar da dimokuraɗiyyar ƙasar.

    "Maimakon ƙoƙarin ɓata sunan Najeriya da kuma ƙasƙantar da martabar ofishin shugaban ƙasa a ƙasashen waje, ya kamata ƴan adawa su mayar da hankali wajen tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar tsaro, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma inganta rayuwar ƴan Najeriya," in ji Ministan

    Ya ce ofishin shugaban ƙasa na da martabarta, don haka ya kamata a mutunta shi duk da bambancin siyasa.

    Matawalle ya kuma buga misali da yadda shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa Shugaba Tinubu kan jagorancinsa da kuma ƙoƙarin gwamnatinsa kan tsaro da yaƙi da ta'addanci.

    Ministan ya ƙara da cewa yaɗa farfaganda da ƙiyayya kan gwamnati ba zai kawo ƙarshenta ba.

    "Waɗanda suke tunanin cewa ƙarya da makirci za su kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu suna yaudarar kansu, domin Najeriya ta ƴan Najeriya ce, kuma su ne za su sake yanke hukunci a zaɓen 2027," in ji sanarwar

  7. An fara gwajin allurar riga-kafin Ebola

    An yi wa mutum na farko allurar gwajin riga-kafin cutar Ebola da aka samar domin yaƙi da nau’in cutar da ke yaɗuwa a yankin tsakiyar Afirka.

    Mutumin mai shekara 37 an yi masa allurar ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Oxford, inda aka samar da ita cikin makwanni takwas kacal.

    Mutanen da za a yi gwajin riga-kafin a kan su ba za su yi hulɗa da masu cutar Ebola ba, maimakon haka, masana za su nazarci yadda garkuwar jikin su ke amsa allurar, domin hakan zai ba da haske kan ko rigakafin na iya kare mutum daga kamuwa da cutar.

    An yi amfani da irin fasahar da aka yi amfani da ita wajen samar da allurar riga-kafin cutar corona, wadda aka yi wa ɗaruruwan miliyoyin mutane a lokacin annobar.

  8. EU ta zargi TikTok da gaza kare ƙananan yara

    Shafin TikTok

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Tarayyar Turai ta zargi masu manhajar TikTok da gazawa wajen kare yara daga cutarwa, inda ta ce akasarin yara da ke amfani da dandalin na fuskantar hantara da kuma cin karo da miyagun mutane masu cutar da su.

    Hukumar ta ce ya kamata a tabbatar da cewa babu wanda zai iya alaƙa da yara a shafin sai wanda aka bai wa izini.

    Babbar mai kula da ɓangaren ci gaban zamani ta hukumar Henna Virkkunen ta ce bai kamata a ce sai yaro ya ga dama ne za a kare shi ba, a maimakon haka ya kamata a kare su da zarar suna kan mahajar.

    TikTok ya ce zai yi nazari kan bayanin na Tarayyar Turai domin ganin yadda za su haɗa hannu wajen gyara lamarin.

    Idan rahoton na EU ya zama gaskiya, hukumar za ta iya cin tarar TikTok na kuɗi masu yawa da za su kai kashi 6 cikin 100 na jimillar kuɗin da yake samu a shekara.

  9. Iran ta ce ta kai hari tare da lalata sansanin sojin Amurka da ke Kuwait

    makamai

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Juyin Juya halin Iran (IRGC) ta sanar da sake kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al-Adiri da ke Kuwait, inda ta ce ta banka wa rumbunan adana makamai da kayan aiki guda uku wuta.

    A cikin sanarwar IRGC ya bayyana cewa ta kai hari kan hasumiyar sa ido ta rundunar ruwa ta biyar ta Amurka da ke Bahrain, tare da lalata ta.

    Har zuwa yanzu, babu wani martani daga Amurka kan wannan rahoto.

    A cikin makonni biyu da suka gabata, an kai hare-hare sau da dama a wasu wurare a Bahrain da Kuwait da ake dangantawa da Iran.

    Iran ta ce sansanoni da kadarorin Amurka da ke yankin suna cikin halastattun wuraren da za ta iya kai wa hari.

  10. MDD ta buƙaci a kuɓutar da matuƙa jiragen ruwan da suka maƙale a Hormuz

    Shugaban hukumar kare haƙƙin biladama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira ga ƙasashen da ke da hannu a yaƙin Iran su taimaka wajen fitar da matuƙan jiragen ruwa kusan 6,000 da suka maƙale a mashigar Hormuz.

    kakakinsa ya ce ya kamata ɓangarorin da ke rikicin su sauƙaƙa hanyoyin da za su ba su damar wucewa cikin aminci.

    Yayin da faɗan ke ci gaba da tsananta, hukumomin Iran sun gargaɗi fararen hula su nisanci sojojin Amurka da ke yankin.

    Haka kuma Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kadarori da sansanoni Amurka, a matsayin martani ga hare-haren bama-bamai da Amurka ke ci gaba da kai mata.

  11. 'Matakai uku da muke bi don ceto ɗaliban da aka sace a Borno'

    Gwamnan Borno

    Asalin hoton, Governor Borno/X

    Fiye da wata biyu bayan sace ɗalibai a makarantu uku da ke garin Mussa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu iyaye na jiran ganin an ceto ƴaƴan nasu.

    Yawaitar satar yara a makarantun Najeriya a baya-bayan nan na daga cikin abubuwa da ke nuna cewa har yanzu matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita na nan, duk da iƙirarin da gwamnatin ƙasar ke yi na cewa tana bakin ƙoƙarinta.

    A baya-bayan nan ƴan bindigar sun ƙara ƙaimi wajen sace ɗalibai a sassa daban-daban na ƙasar.

    A ranar 10 ga Yulin 2026, gwamnatin Najeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai da malaman makarantar da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo, kwanaki 56 bayan sace su daga makarantarsu da ke ƙaramar hukumar Orire a yankin Ogbomoso na jihar Oyo.

    Gwamnatin Bornon tya bayyana wasu matakai uku da ta ce tana ɗauka don tabbatar da kuɓutar da yaran.

  12. Jamus ta naɗa Jurgen Klopp sabon kocin ƙasar

    Jurgen Klopp

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafar Jamus ta bayyana tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, a matsayin sabon kocin tawagar ƙasar.

    Naɗin nasa na zuwa kwanaki bayan murabus ɗin Julian Nagelsmann, wanda ya ajiye aiki bayan da tawagar Jamus ta fice daga Gasar Kofin Duniya tun a matakin ƴan 32.

    Klopp, wanda ke cikin manajojin a duniyar ƙwallon ƙafa - bai riƙe wani aikin horaswa ba tun bayan da ya bar Liverpool shekaru biyu da suka gabata.

    Aikinsa na baya-bayan nan shi ne shugaban harkokin ƙwallon ƙafa na duniya na kamfanin Red Bull, tare da yin sharhi a talabijin kan harkokin ƙwallon kafa.

    Yanzu yana fuskantar ƙalubalen farfaɗo da martabar wannan babbar tawagar Turai, wadda ta taɓa lashe Kofin Duniya har sau huɗu a tarihinta.

  13. Gwamnan Sokoto ya bai wa ma'aikatan jihar hutu don rajistar zaɓe

    Ahmad Aliyu Sokoto

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu Sokoto/FB

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ayyana yau Juma'a 24 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar domin waɗanda ba su yi rajistar katin zaɓe ba su samu damar yin hakan.

    Cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan, Gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar ya ce gwamnan ya buƙaci ma'aikatan gwamnati a jihar su yi rajistar domin samun damar kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen ƙasar da ke tafe cikin shekara mai zuwa.

    Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da ma'aiakatn jihar sun samu cikakkiyar damar aiwatar da ƴancinsu.

    A baya-bayan nan ne dai hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da tsawaita wa'adin rajistar zaɓen da mako biyu, wanda zai ƙare ranar 26 ga watan Yulin da muke ciki.

    Gwamna Ahmad Aliyu ya buƙaci sauran al'ummar jihar da ba su yi rajistar zaɓen ba, su yi amfani da damar tsawaita wa'adin don yin rajistar.

  14. Matakin ministan Isra'ila kan Masallacin Ƙudus ya fusata musulmi

    Masallacin Kudus

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasashe takwas na Larabawa da na Musulunci sun yi Allah wadai da shigar wani ministan Isra'ila - da kuma yahudawan ƴan kama wuri zauna cikin Masallacin Al-Aqsa - cikin Masallacin Al'aqsa da ke Ƙudus.

    Cikin wata sanarwar hadin gwiwa ministocin harkokin wajen ƙasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Jordan da Masar da Qatar da Turkiyya da Pakistan da kuma Indonesia sun yi kakkausar suka kan shigar Itamar Ben-Gvir, Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra'ila, tare da wasu yahudawan Masallacin, wanda ke birnin Ƙudus a gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Sanarwar, wadda aka fitar da maraicen Alhamis, ta bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa matsayin tarihi da na doka da aka tanadar wa Masallacin Al-Aqsa, tare da bayyana shi a matsayin tsokanar da ba za a amince da ita ba, wadda za ta iya haddasa karin tashin hankali a yankin.

    Ƙasashen na musulmi sun kuma buƙaci:

    • Mutunta matsayar Jordan a matsayin mai kula da wurin ibadar mai tsarki ga Musulmi da Kiristoci a Birnin Kudus.
    • Kin amincewa da duk wani yunƙuri na sauya matsayin tarihi da na doka da ya shafi Masallacin Ƙudus
    • Bukatar dakatar da matakan abin da suka kira tsokana da kuma ɗaukar matakai ba tare da tuntɓa ba, waɗanda za su iya jefa tsaro da zaman lafiyar yankin cikin hadari.
    • Bin dokokin duniya da kuma ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka shafi Birnin Kudus.

    An fitar da sanarwar ne bayan da Mista Itamar Ben-Gvir ya shiga harabar Masallacin Al-Aqsa tare da ɗaruruwan yahudawa ƴan kama wuri zauna.

    Matakin ya jawo suka daga Falasdinawa da Jordan da kuma wasu ƙasashen Larabawa da na Musulunci.

  15. Sojojin Najeriya na farautar wani soja kan zargin sayar wa ƴanbindiga kakin soji

    Sojan da ake nema

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Sashen kula da kayan aiki na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ayyana neman ɗaya daga cikin jami'anta ruwa a jallo, saboda zarginsa da sayar da kakin soji ga ''ƴanta'adda da masu aikata laifuka''.

    Jami'in sojin wanda kurtu ne, mai suna Mohammed Yusuf Amutu tuni ya tsare daga wurin aikinsa bayan da zargin da ake yi masa ya fito fili.

    Cikin wata sanarwar da sashen kula da kayan aikin soji na rundunar sojin ya fitar, ya ce yana ƙoƙarin gano inda sojan yake domin kama shi don fuskantar ladabtarwa.

    Rundunar ta jaddada matsayin na rashin lamuntar saɓa wa aiki ko rashin ɗa'a ko duk wani abu da zai janyo wa rundunar sojin ƙasar barazana.

    ''Duk wani jami'inmu da muka samu da laifin taimaka wa ayyukan ƴanta'adda da masu aikata laifuka ko wasu ƙungiyoyi da gwamnati ta haramta, ta hanyar sayar musu da kakin soji ko wasu kayyaki, to zai fuskanci hukunci ƙarƙashin dokokin soji da kundin tsarin mulkin ƙasa'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Sojan Najeriya da ake nema

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Sanarwar ta kuma yi kira ga mutane su taimaka wajen kai rahoton jami'in a duk inda suka ganshi.

    ''Muna kira ga jama'a duk inda suka ganshi su yi ƙoƙarin sanar da sojoji mafi kusa da su ko wata hukumar tsaro mafi kusa'', in ji sanarwar.

  16. Trump ya sanar da ƙara haraji ga ƙasashe ciki har da Najeriya

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A watan Afrilun 2025 ma Trump ya sanya wa wasu ƙasashe haraji

    Trump ya sanar da ƙaƙaba sabbin harajin shigar da kayayyaki Amurka daga wasu ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya.

    Shugaba Trump ya ɗauki matakin ne a ƙoƙarin farfaɗo da manufarsa ta kare masana’antun cikin gida - matakin da ake ta ƙalubalanta a kotu.

    Sabbin harajin, waɗanda suka kai tsakanin kashi 10 zuwa 12.5 cikin 100, sun dogara ne kan zargin cewa abokan hulɗar kasuwancin Amurka ba sa yin abin da ya dace wajen daƙile ayyukan tilasta wa jama'a.

    Matakin ya maye gurbin wani harajin wucin gadi da aka sanya bayan da Kotun Ƙolin Amurka ta soke wani jerin harajin daban-daban da gwamnatin Trump ta kakaba a baya.

    Ƙasashe da dama sun nuna rashin jin daɗinsu game da wannan mataki, inda Brazil da Australia, suka ce babu wani dalili na sabon harajin.

    Yayin da Japan ta bayyana matakin a matsayin abin takaici, New Zealand cewa ta yi ta ji matuƙar takaici da matakin na Amurka.

  17. Hare-haren Amurka sun faɗa tashar jiragen ruwan Iran

    Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya ce an ji ƙarar fashe-fashe sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Amurka ta kai a wurare da dama da ke gaɓar Tekun Fasha.

    Rahotannin sun ce hare-haren sun shafi tsibirin Qeshm da kuma tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas, tare da wasu bayanan da ke nuna cewa an kuma samu fashe-fashe a yankunan yamma da tsakiyar Iran ɗin.

    Haka kuma rahotannin sun ce an kunna garkuwar sararin samaniya a babban birnin ƙasar Tehran.

    Lamarin na zuwa ne bayan Shugaba Trump na Amurka, ya yi barazanar abin da ya kira hukunta Iran da ƙawayenta na Houthi da ke Yemen, a kan hare-haren da mayaƙan Houthin ke kaiwa kan jiragen ruwa na dakon man Saudiyya a Tekun Maliya.

  18. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirara.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.