Babu adalci a shari'ar da ake yi wa ƴan Boko Haram a Najeriya - HRW

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta zargi hukumomin Najeriya da rashin adalci wajen gudanar da shari’o’in da suka shafi waɗanda ake zargi da zama ƴan ƙungiyar Boko Haram.
A wani rahoto da ta fitar ranar Laraba, ƙungiyar ta ce ba a yin adalci a shari’o’in da ake yi ga waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa tsawon shekaru.
HRW ta ce shari’o’in sun fi mayar da hankali ne kan waɗanda ba su da wani matsayi mai girma a ƙungiyar, yayin da manyan waɗanda ake zargi da hannu wajen aikata manyan laifuka ke ci gaba da tsallake hukunci.
Ƙungiyar ta bayyana cewa akwai matsaloli masu yawa da suka shafi tsarin shari’ar ta’addanci da kuma rashin ingancin hujjojin da ake gabatarwa a kotu.
Ta ce wasu daga cikin shari’o’in sun dogara ne kawai kan amincewar waɗanda ake tuhuma da laifi, ba tare da shaidu ko cikakkun hujjoji da za su tabbatar da zargin ba.
HRW ta kuma ce wasu daga cikin waɗanda ake tuhumar ana zarginsu ne da taimaka wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yanayi da ka iya kasancewa an tilasta musu yin hakan.
Ƙungiyar ta kuma nuna shakku kan ingancin lauyoyin da kotu ke ware wa waɗanda ba su da ikon ɗaukar lauyoyi, inda ta ce hakan na iya hana su samun cikakkiyar kariya a shari’a.
Wannan suka na zuwa ne bayan da Najeriya ta ke ci gaba da shari’o’in ta’addanci a wannan shekara, inda sama da mutum 1,100 ake tuhuma da laifukan da suka shafi Boko Haram da ƙungiyar ISWAP.







