Yadda za a yi zaɓen fitar da gwanin shugaban Najeriya a jam’iyyar APC

Asalin hoton, Multiple
A yau ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasar, domin zaɓen mutumin da zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Za a gudanar da zaɓen ne ta hanyar ƴartinƙe kamar yadda jam'iyyar ta tsara.
Cikin sanarwar zaɓen da ta fitar, APC ta ce ta tsara gudanar da zaɓen ne bayan kammala na gwamnoni da na ƴan majalisun tarayya.
A tsakiyar makon nan ne aka gudanar da na gwamnonin jihohi, yayin da a farkon makon aka gudanar da na ƴan majalisar dattawan bayan na ƴan majalisar wakilai a ƙarshen mako.
Ƴan takara nawa ne za su fafata?

Asalin hoton, Multiple
Kawo yanzu mutum biyu ne suka sayi fom ɗin takara domin fafatawa a zaɓen.
- Bola Tinubu
Shugaban ƙasar mai ci, Bola Ahmed Tinubu, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu.
A shekarar 2023 ne aka zaɓe shi matsayin shugaban ƙasa, ƙarƙashin inuwar jam'iyyar.
Tun a shekarar da ta gabata ne, jam'iyyar ta ayyana shi a matsayin wanda zai yi mata takarar 2027.
Tuni dai ya nuna sha'awarsa ta saya wa takarar bayan da ya sayi fom.
- Stanley Osifo
Stanley Osifo ne ɗan takara ɗaya tilo a APC, da ya ƙudiri aniyar ƙalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar.
Bayanai na nuna cewa Mista Osifo ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan kuɗi naira miliyan 100 a shalkwatar jam'iyyar, kuma tuni ya cika tare da mayar da fom ɗin.
Stanley Osifo haifaffen garin Benin ne daga jihar Edo, da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Ɗan siyasar mai shekara 50, ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2019.
A ina za a yi zaɓen fitar da gwani
Cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar, ta ce za a gudanar da zaɓukan fitar da gwanin a faɗin mazaɓun ƙasar 8,809 ta hanyar ƴartinƙe.
APC ta ce za a tattara sakamakon zaɓukan kowace mazaɓa a ƙaramar hukuma, kafin a aika shi babbar cibiyar tattara sakamakon ta ƙasa da ke Abuja.
Tuni dai jam'iyyar ta kafa kwamitin da zai lura da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasar, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Pius Anyum Pius.
Yayin da duka gwamnoni APC za su kasance masu tsara zaɓen a jihohinsu.
Haka ma jam'iyyar ta kafa kwamitin ƙarɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen, ƙarƙashin jagorancin Sanata Ali Ndume.
Me ya sa APC ba za ta yi maslaha a zaɓen ba?
Daga abin da ya gabata na zabukan fitar da gwani a wannan kari, jam'iyyar APC dai galibi ta yi amfani da hanyar masalaha wajen fitar da ƴantakarar.
To sai dai Mallam Bala Ibrahim Daraktan yaɗa labaran sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa ta ce a wannan karo za a yi amfani da zaɓen ƴantinƙe ne domin fitar da ɗan takatar shugaban ƙasar.
Yayin hirarsa da BBC, Mallam Bala ya ce ''tun da aka samu wanda ya sayi fom ya cike, bayan Shugba Tinubu, ka ga ya nuna yana son ya tsaya takara kenan''.
Su wane ne za su yi zaɓen fitar da gwanin?
Sabuwar dokar zaɓen ƙasar dai ta yi tanadin cewa masu riƙe da katin jam'iyya ne za su yi zaɓen fitar da gwanin.
To amma Bala Ibrahim ya ce akwai ƙarin abubuwan da jam'iyyar za ta yi la'akari da su wajen bai wa mutane damar shiga zaɓen na fitar da gwani.
"Akwai wasu abubuwa da za mu yi la'akari da su wajen fayyace waɗanda za su shiga zaɓen na fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa'', in ji shi.
''Ƴan jam'iyya ne cikakku masu katin jam'iyya, waɗanda ke biyan haƙƙoƙin jam'iyya, da sauran sharuɗɗan da aka gindaya, ba wai duk wanda ya mallaki katin jam'iyya kawai ba'', kamar yadda Mallam Bala Ibrahim ya bayyana.
Ya ƙara da cewa ''magoya bayan kowa za su fito su jeru a bayansa, domin ganin wanda nasa suka fi yawa domin samun nasara'', in ji shi.











