Ko sheƙa gudu a mota na sawa mu isa inda za mu je da wuri?

Ko sheƙa gudu a mota na sawa mu isa inda za mu je da wuri?

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, BBC News Mundo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Rédaction
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

"Ka bi a hankali direba, ba sauri nake ba."

Tana iya yiwuwa ka sha jin haka ko kuma ƙila ka taɓa faɗa wa wani haka domin a rage gudu: ko da a lokacin da muke da wani abu na gaggawa, idan muka riƙa sheƙa gudu a mota a ƙarshe sauri zai iya haifar da nawa, domin an fi shiga hadarin tafka kuskure.

Duk da cewa a zahiri mukan yanke hukuncin ƙara gudun abin hawa a duk lokacin da muke sauri, wani nazari da aka yi zai iya sawa ka sauya tunaninka game da hakan.

Bincike ya gano cewa yayin da kake ƙara gudu domin ka yi sauri, lokacin da kake tunanin kana ragewa bai taka kara ya karya ba. Sannan kuma ka fi shiga cikin haɗarin yin hatsari a kan hanya.

Nazarin da aka yi, da kuma alƙaluman da aka samu duk sun tabbatar da gaskiyar hakan.

Amma ba muna nufin cewa idan ka sheƙa gudu ba za ka isa da wuri ba, sai dai ba kamar yadda kake tunani ba.

Ƙara gudu zai sa ka rage yawan lokacin da za ka ɗiba kafin isa inda za ka je, to amma akwai lokacin da zai kasance ɗan hanzarin da zai ƙaru bai taka kara ya karya ba, sannan kuma hadarin da ke tattare da hakan na da matuƙar yawa.

Bari mu yi misali da tafiyar kilomita 10.

Idan kana tafiya cikin mota kan gudun kilomita 10 a awa ɗaya, za ka kwashe awa ɗaya kenan kana tafiya kafin ka isa.

Idan kuma ka nunka gudun zuwa kilomita 20 a awa ɗaya, za ka ɗauki minti 30 kenan kacal kafin ka isa inda za ka je, ka rage lokaci mai yawa.

Idan ka sake nunka gudun zuwa kilomita 40 a cikin awa ɗaya, za ka kenan cikin minti 15.

To amma ko ka lura da abin da ke faruwa?

Bari mu ƙara gudu

Yayin da bambancin tafiya a gudun kilomita 10 cikin awa ɗaya da kuma gudun kilomita 40 a awa ɗaya ke da yawa, tunda za ka isa a cikin minti 15 a maimakon awa ɗaya, yawan lokacin da ke raguwa a duk lokacin da ka ƙara gudu na raguwa.

Haka nan kuma akwai wani abin da ya kamata mu kula da shi.

A zahiri, akwai wasu abubuwan da ke katse wa mutum hanzari, kamar danjar bada hannu, da cunkoson ababen hawa da kuma rashin kyawun hanya.

Idan ka lura da duk wadannan abubuwa, za ka ga cewa gara ma ka kira inda za ka je ka ce musu za ka ɗan makara kafin ka isa.

Ba kawai domin lokacin da za ka rage bai taka kara ya karya ba, har ma da la'akari da haɗarin da ke tattare da gudun.

Gargaɗi: Haɗari

Yayin da yawan lokacin da kake ragewa idan kana ƙara gudu ke raguwa, tsautsayin samu haɗari kuma na ƙaruwa ne, haka nan ma munin irin raunukan da za a samu.

Yawan gudun da kake yi zai rage maka damar ɗaukar mataki idan wani abu ya gitto maka, ko lokacin da wanda ke gabanka ya taka burki cikin hanzari ko kuma wani abu da ba a yi tsammani ba ya faru.

Haka nan a duk lokacin da ka taka burki, tazarar da motar za ta kwashe kafin ta tsaya na ƙaruwa daidai da gudun da kake sheƙawa.

Bari mu duba bayanin da hukumomin jihar Queensland da ke ƙasar Australia suka fitar.

Kamar mutum ne da ke tuƙa mota yadda aka saba yau da kullum.

  • Idan yana gudun kilomita 40 a awa ɗaya sai ya ci ga wani abu ya fado masa babu tsammani, motar za ta yi tafiyar mita 17 kafin direban ya kai ƙafarsa kan burki, kuma motar za ta yi tafiyar mita 26 kafin ta tsaya bayan taka burkin.
  • Idan kuma direba na gudun kilomita 80 a awa ɗaya ne zai yi tafiyar kimanin mita 33 kafin ya kai ƙafarsa kan burki sannan kuma motar za ta yi tafiya mita 69 kafin ta tsaya.
  • Idan kuma ana gudun kilomita 110 ne a awa ɗaya, duk hanzarin da direban zai yi wajen taka burki motar ba za ta tsaya ba sai ta yi tafiyar mita 100, kafin ya iya kauce wa abin da ya gitto masa.

Irin wannan ne ke jefa matafiya cikin haɗari, inda gudu zai iya haifar da baƙin ciki.

Abin da zai iya faruwa

An fi so dai ko ma mene ne, hanyar lafiya a bi ta da shekara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An fi so dai ko ma mene ne, hanyar lafiya a bi ta da shekara
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sheƙa gudu a mota ba kawai yana shafar lokacin da za ka kai inda za ka je ne ba, yana kuma matuƙar shafar abin da zai faru idan aka samu haɗari.

Idan motar da ke gudu ta ci karo da wata motar, ko keke ko kuma da mutum, ɓarnar da za ta faru ta danganta ne da yawan gudun motar da kuma ƙarfin tafiyarta.

Bari mu duba yadda lissafin yake.

Idan aka jefe ka da ƙwallon da aka buga a hankali, ƙila ba za ka ji zafi sosai ba, amma idan aka bugo ƙwallon da ƙarfi ta same ka, to za ka ji zafi sosai ko ma ta ji maka rauni.

A nan ƙwallo ɗaya ce, amma ƙarfin da aka bugo ta ya bambanta, wannan shi ne ƙarfin tafiyar abu.

Hakan na nufin ba gudun ba ne kawai ke taka rawa a wannan lokaci, girma da nauyin abin ma yana da muhimmanci a nan.

Idan aka buga abubuwa biyu a lokaci ɗaya, da ƙarfi ɗaya, abin da ya fi nauyi ya fi yin illa a kan wanda ba ya da nauyi sosai.

A lokacin da aka samu karo, yawan gudu na ƙara ƙarfi da illar da abin zai yi idan ya ci karo.

Wani nazari da aka yi a shekara ta 2019 ya lissafa yawan haarin mutuwar mutumin da mota ta buge, daidai da yawan gudun da mota ke yi.

Haarin mutuwa na ƙaruwa da kashi 11% a duk ƙarin gudun kilomita ɗaya cikin awa da mota za ta yi.

Haɗarin mutuwar mutumin da mota ta buge an ƙiyasta shi a kan:

  • kimanin kashi 5% kan kimanin gudun kilomita 30 a awa ɗaya da mota ke yi
  • 10% a gudun kilomita 37 cikin awa ɗaya
  • 50% a gudun kilomita 59 cikin awa ɗaya
  • 75% a gudun kilomita 69 cikin awa ɗaya
  • 90% a gudun kilomita 80 cikin awa ɗaya

A duk ƙarin gudun kilomita daya, ba wai kawia yiwuwar shiga cikin hatsari na ƙaruwa ne kawai ba, a'a, yana nunkawa ne.

Idan mota ta buge mutum hadarin kashe shi ya kai 5% idan motar tana gudun kilomita 30 cikin awa ɗaya, amma haɗarin mutuwar ya zarce 50% idan gudun motar ya nunka zuwa kilomita 60 cikin awa ɗaya.

Wannan alaƙa da ke tsakanin gudun mota da yiwuwar faruwar haɗari na nuna cewa tafiya a hankali na rage yiwuwar kashe mutum ko kuma samun mummunan rauni.

Wani zai iya ganin tamkar duk wannan mummunan labari ne, to amma akwai wani labarin mai daɗi: shi ne, a rage gudu.

Tabbas, hakan ya ƙunshi ƙoƙarin danne zuciyarka da ke ce maka ka ƙara taka wuta saboda kana ganin za ka yi latti.

Idan zuciyarka ta fara raya maka haka, ka tsaya ka tambayi kanka, shin ya kamata na jefa rayuwata cikin babban haɗari kawai saboda na ƙara saurin minti 5 ko 10?