Yadda Majalisar Najeriya za ta fara muhawara kan samar da 'yansandan jihohi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Larabar nan ne ake sa ran Majalisar Dattawan Najeriya za ta fara muhawara kan wani gagarumin ƙudirin doka da ke neman samar da rundunonin 'yansandan jihohi, matakin da zai iya haifar da ɗaya daga cikin manyan sauye-sauye a tsarin tsaron ƙasar tun bayan komawarta mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar a ranar Talata, zai bai wa jihohin Najeriya 36 damar kafa tare da tafiyar da rundunonin 'yansandansu, baya ga rundunar 'yan sandan tarayya ta Najeriya.

Tsawon shekaru da dama, gwamnatin tarayya ce kaɗai ke da ikon kula da harkokin 'yan sanda a Najeriya, inda ake tura jami'ai zuwa sassan ƙasar ƙarƙashin tsari guda da ake gudanarwa daga tarayya.

Ƙudirin ya sake tayar da muhawarar da aka daɗe ana yi a Najeriya kan ko ya kamata a raba ikon gudanar da harkokin 'yan sanda a ƙasar da ke da sama da mutum miliyan 220, masu bambancin ƙabila, addini da kuma yankuna.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga dukkan sanatoci da su halarci zaman majalisar na ranar Laraba, yana mai jaddada muhimmancin muhawarar da kuma buƙatar samun cikakken halartar mambobi wajen yin gyaran kundin tsarin mulki.

Ko da yake muhawarar da za a fara a yau ita ce mataki na farko a cikin doguwar tafiyar da ƙudirin zai bi, ana kallon hakan a matsayin wani babban ci gaba ga ra'ayin da aka daɗe ana tattaunawa a kai a fannin gyaran tsarin tsaro da kundin mulki.

Dalilan masu goyon bayan samar da 'yansandan jihohi

Kiran samar da 'yansandan jihohi ya ƙara samun karɓuwa yayin da matsalolin tsaro ke ci gaba da ƙamari a sassa daban-daban na Najeriya.

Ƙasar na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro iri-iri da suka haɗa da ayyukan 'yan bindiga a arewa maso yamma, rikicin masu tayar da ƙayar baya a arewa maso gabas, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma hare-haren ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Masu goyon bayan ƙudirin na cewa rundunar 'yan sanda da ake tafiyar da ita daga tsakiya tana fuskantar yawan aiki, kuma sau da yawa ba ta da cikakken sanin yanayin yankunan da take aiki a cikinsu.

Sun kuma ce jami'an da aka ɗauka aiki daga cikin al'ummomin yankin za su fi fahimtar harsuna, da al'adu da kuma yanayin wuraren da suke aiki.

Har ila yau, suna ganin gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi ne kan fara fuskantar matsin lamba daga jama'a idan matsalar tsaro ta taso, amma kuma ba su da cikakken iko kan rundunar 'yan sanda da ke aiki a jihohinsu.

A cewar masu goyon bayan ƙudirin, raba ikon gudanar da harkokin 'yan sanda zai taimaka wajen inganta tattara bayanan sirri, da ƙarfafa aikin 'yan sandan al'umma da kuma saurin mayar da martani ga matsalolin tsaro.

Wasu daga cikinsu na yin nuni da yadda ƙasashe irin su Amurka da Indiya da Canada ke da matakai daban-daban na rundunonin tsaro da ke aiki lokaci guda.

Idan aka amince da ƙudirin, Najeriya za ta samu sabon tsarin da rundunonin 'yan sandan tarayya da na jihohi za su riƙa aiki tare bisa iyakokin ikon da kundin tsarin mulki ya tanada.

Damuwar masu adawa da ƙudirin

Sai dai duk da yadda ƙudirin ke samun goyon baya daga wasu ɓangarori, har yanzu akwai masu nuna damuwa game da shi.

Masu adawa da shirin sun daɗe suna gargadin cewa rundunonin 'yansandan jihohi na iya zama wata hanya da gwamnatocin jihohi za su yi amfani da ita wajen cimma manufofinsu na siyasa.

Daya daga cikin manyan damuwar da ake nunawa ita ce yiwuwar wasu gwamnoni su yi amfani da rundunonin wajen cimma manufofinsu na siyasa, musamman a lokutan zaɓe.

Masu sukar shirin na tsoron cewa wasu gwamnoni za su iya amfani da irin waɗannan rundunoni wajen matsa wa abokan hamayyarsu lamba, ko kuma amfani da su kan 'yan adawa, da masu fafutuka da masu sukar gwamnati.

Wasu masana na cewa har yanzu dimokuraɗiyyar Najeriya ba ta yi balagar da za a yi kasassabar karawa mai karfi karfi ba, kuma yin hakan hadari ne ga wanzuwar dimukradiyyar.

Wasu kuma na fargabar cewa samun rundunonin 'yan sanda da dama na iya haifar da saɓanin iko tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi, musamman a lokacin manyan ayyukan tsaro.

Matakan amincewa da kudurin

Ko da 'yan majalisa sun amince da ƙudirin a matakin farko, akwai kuma matakai masu yawa da dole ya bi kafin ya zama doka.

Saboda yana neman yin gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya, dole ne ya samu goyon bayan aƙalla kashi biyu bisa uku na mambobin Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

Idan ya tsallake wannan mataki, sai kuma ya samu amincewar aƙalla majalisun dokoki 24 daga cikin jihohin Najeriya 36.

Bayan ya cika dukkan wadannan sharudda ne kuma, za a miƙa shi ga Shugaba Tinubu domin sanya hannu ya zama doka.

Yayin da ake bin dukka wadannan matakai, za kuma a gudanar da sauraron ra'ayoyin jama'a, da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da masana harkokin tsaro, da ƙungiyoyin farar hula, da sarakunan gargajiya da gwamnatocin jihohi.