Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tasu'a da Ashura: Saɓanin fahimtar Sunna da Shi'a kan ranakun biyu
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
A kowace ranar 9 da 10 ga watan Almuharram, wata na farko a sabuwar shekarar Musulunci, Musulmi mabiya manyan mazhabobin addinin biyu, Sunni da Shi'a kan gudanar da wasu abubuwa na tunawa da ranar.
Kalmar Tasu'a na nufin tara ga wata yayin da Ashura ke nufin goma ga wata, a cewar Imam Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin masallacin Nagazi-uvete da ke garin Okene na Jihar Kogi a tsakiyar Najeriya a wata tattaunawa da ya yi da BBC a 2021.
Rana ce mai matuƙar muhimmanci ga mabiya addinin Musulunci a faɗin duniya.
To sai dai manyan mazhabobin addinin na duniya, Sunni da Shi'a na da mabambantan hanyoyin tunawa da wannan ranar.
Musulmai kan ɗauki ranar da muhimmanci ta yadda wasu ke azumi, wasu kuma ke alhini ko baƙin ciki.
Tarihin ranar
Mabiya mazhabar Sunni kan ɗauki ranar da muhimmanci domin tunawa da ranar da Annabi Musa ya tsallake Kogin Nilu tare da mabiyansa domin tsira daga cutarwar Fir'auna.
Sheikh Hussaini Zakariyya, fitaccen malami mai bin tafarkin sunna a Najeriya, ya ce ranar na da alaƙa da tseratarwar da Allah ya yi wa Annabi Musa da ɗan'uwansa Annabi Haruna.
''A ranar ne Annabi Musa da mabiyansa suka ƙuduri aniyar tsallaka Kogin Nilu zuwa ɗaya ɓangaren domin tsira daga zalunci da muzgunawar da Fira'auna ke yi wa Bani Isra'ila''.
''Ana tsaka da hakan ne kuma sai Fir'aunan ya samu labari nan take ya haɗa mabiyansa domin zuwa su murƙushe su'', in ji shi.
Ya ce bayan da Annabi Musa da mabiyansa suka isa gaɓar kogin sai ya daki tekun da sandarsa, sai kuma ya dare, yayin da shi da mabiyansa suka shige ta ciki suka tsallaka.
''Shi ma Fir'auna da tawagarsa bayan da suka iso wurin sai ya daki tekun da sandarsa, teku ya dare suka bi ta cikin domin cimma Annabi Musa da mabiyansa, amma suna zuwa tsakiya sai Allah ya umarci kogin ya haɗe, inda ya halaka su duka ya kuma tseratar da gawra Fir'auna domin ta zama aya ga sauran mutane'', kamar yadda ya yi bayani.
Sheikh Hussaini Zakariyya ya ce wannan al'amari ya faru ne ranar 10 ga watan Almuharram, don haka ne Annabi Musa ya ɗauki ranar a matayin ranar tunawa da tseratarwa da Allah ya yi masa da mutanensa.
''Rana ce ta gode wa Allah, saboda ni'imar tseratarwar da ya yi wa Annabi Musa da mabiyansa, to haka abin ya biyo annabawan da suka biyo baya, kamar Annabi Isa AS, wanda shi da mutanensa suka riƙa azumta'', in ji Shehin malamin.

Wace ibada ake yi a ranar?
Dangane da dalilin da ya a Musulmi ke ibada a ranar kuwa, Sheikh Zakariyya ya ce su Musulmi masu biyayya ne ga koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W, kuma duka annabawan Allah saƙo ɗaya suka kawo wato bautar Allah da guje wa shirka.
Don haka lokacin da Annabi S.A.W ya zo da saƙon Ubangiji ya tarar da mutanensa Larabawan gargajiya suna azumtar ranar a matsayin ibadar gargajiya a Makka.
''Lokacin da ya je Madina ya samu Yahudawa suna azumtar wunin, kuma ana bikin da kaɗe-kaɗe, sai ya tambayi dalili, sai aka ce masa suna yin bikin ne domin tunawa da ranar tseratawar da Allah ya yi musu, sai Annabi S.A.W ya ce ai mu (Musulmai) mu ne muka fi cancanta da azumin''.
Hadisin Abdullahi ibn Abbas cikin Bukhari da Muslim ya tabbatar da haka, a cewar malamin addinin.
A cikin hadisin annabi ya ce ''idan Allah ya kai mu shekara mai zuwa za mu haɗa da Tasu'a - wato 9 ga wata - domin mu bambanta da Yahudawa''.
To sai dai malamai sun ce kafin shekarar ta zagayo Annabi ya yi wafati.
Abdullahi bin Abbas ya ce ''Annabi ya ce azumin ranar Ashura zai kankare zunubin shekarar da ta gabata''.
Ibadun da Sunna ta tabbatar a ranar Ashura
Sheikh Hussaini Zakariya ya ce abubuwan da koyarwar sunna ta koyar domin yin su a ranar Tasu'a da Ashura su ne kamar haka:
- Yin Azumin nafila a ranar 9 ga wata
- Azumin nafila a ranar 10 ga wata
Sai dai malam Muhammad Mashhud da ke jihar Zamfara ya bayyana abubuwa 11 da ake son Musulmi ya aiwatar a ranakun duk da cewa wasu malamai sun ce hadisin bai inganta ba. Abubuwan su ne:
- Azumi
- Sada zumunci
- Sallar nafila
- Ziyaratar malami
- Wanka
- Shafa kan maraya saboda tausaya masa
- Sadaƙa
- Shafa kwalli
- Yalwata wa iyali
- Yanke farce
- Karanta Suratul Iklas
Amma a mazhabin Shi'a kuma asalin ranar Ashura ta bambanta da na koyarwar Sunni.
Sheikh Hussaini Lawan Kano Sautul Shi'a, fitaccen malamin Shi'a a Najeriya ya ce mabiya Shi'a Imamiyya ba su yarda da abin da Sunna ke ganin shi ne asalin ranar.
''Abin da muka sani, shi ne sai da Annabi S.A.W ya shekara 10 a Madina kafin ya rasu, amma me ya sa duk bai yi ba sai a shekarar ƙarshe ya ce shekara mai zuwa zai yi kuma bai kai shekarar ba ya rasu?''
Ya ce a mazhabin Shi'a ana ɗaukar ranar Tasu'a da Ashura a matsayin ranar tunawa da baƙin cikin kisan da aka yi wa Imam Hussaini AS, jikan Manzon Allah S.A.W.
''A ranar ne aka yi masa kisan gilla a Karbala, don haka rana ce ta baƙin ciki ba farin ciki ba, waɗanda suka kashe shi sun yi niyyar kashe shi a aranar Tasu'a, amma ya roƙe su suka jinkirta masa zuwa ranar 10 ga wata wato Ashura'', kamar dadda Sheikh Hussani Lawan ya yi ƙarin haske.
Ya ci gaba da cewa Hakimunnaisaburi ya faɗa cikin wani littafinsa cewa mala'ika Jibrilu ya faɗa wa Annabi cewa jikan nan nasa (Imam Hussani) za a kashe shi a Karbala.
''Don haka ya kawo masa wata ƙasa da ya ce masa ta Karbala ɗin ce, wanda Manzon Allah ya damƙa wa Nana Ummussalama cewa ta ajiye ƙasar a cikin kwalba, kuma duk ranar da ƙasar ta zama jini to alama ce da ke nuna cewa an kashe Iman Hussaini'', in ji shi.
Malamin ya ce da wannan alama ce Ummussalam ta gane an kashe Imam Hussaini saboda a lokaci babu waya, kwalbar na ajiye a ɗakinta ta ga ta rikiɗe ta koma jini.
''A ranar ta yi kuka har sai dai aka ji kururuwarta a cikin garin Madina'', in ji shi.
Ibadun da Shi'a ke yi a ranakun Tasu'a da Ashura
Sheikh Hussaini Lawan Kano ya ce abin da koyarwar Shi'a ta tanada a yi domin wannan rana shi ne jimami da nuna baƙin ciki ga kisan Imam Hussaini.
''Babbar ibadar da muke yi a wannan rana ita ce taya Manzon Allah baƙin cikin abin da ya samu jikokinsa da zuri'arsa a wannan rana'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya kuma ƙara da cewa baya ga wannan ana kuma yin "laɗamiyya" wato bugun ƙirji a hankali ana kuka, da waƙe tare da tunawa da abin da ya faru.
Mene ne matsayin yanka jiki da wuƙaƙe a ranar Ashura?
Sai dai kuma Sheikh Hussaini Lawan Kano ya ce yanka da dukan jiki domin jini ya fita wannan ba ya cikin koyarwar Shi'a Imamiyya.
''Wannan abin a hukumance ma an haramta a ƙasar Iran''.
Malamin ya ce wasu gurɓatattun ƴan Shi'a ne ke yin wannan ɗabi'a, amma baya cikin koyarwarsu.
''Kamar yadda ka sani a cikin kowace irin ɗariƙa akwai gurɓatattu, to haka mu ma a cikinmu akwai waɗanda suka wuce gona da iri'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa masu irin wannan aƙida ba mabiya Shi'a ne na aihini ba.
Imam Murtadha Gusau a tattaunawarsa da BBC a 2021 ya ce akwai wasu mabiya ɗariƙa da ake kira Nawasib waɗanda su kuma farin ciki da wannan kisan da aka yi wa Hussaini jikan Annabi suke yi.
"Za ka ga a wannan rana su 'yan Nawasib murna suke, suna yanka dabbobi saboda su saɓa wa 'yan Shi'a. Su suna murna ne da abin da 'yan Shi'a ke baƙin ciki a kansa," a cewarsa.
"Sai dai duk wanda ya yi murna ko baƙin ciki a wannan rana ya saɓa wa Shari'ar Musulunci saboda babu abin da ya inganta daga Annabi Muhammad SAW a kan hakan saɓanin azumi," in ji Sheikh Murtadha.
Bisa al'ada, al'ummar Hausawa kan kira ranar Ashura da Ranar Cika-Ciki.
Wasu ma kan kira watan na Muharram da watan cin jela.
Daga jin sunan an san cewa yana nufin farin ciki da ciye-ciye da yalwata wa iyali.
Iyalan Hausawa kan yi girke-girke na musamman a wannan rana sannan su aika wa maƙota domin sada zumunci - ko da yake dai al'adar ba a aiwatar da ita sosai yanzu a birane.