Arsenal na zawarcin Raphinha, an yi wa Chelsea tayin Bissouma

Asalin hoton, Getty Images
An yi wa Chelsea tayintsohon ɗanwasan tsakiyarMali da Tottenham mai shekara 30, Yves Bissouma, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗanwasan Argentina mai shekara 25, Enzo Fernandez, wanda ya koma Manchester City kan £125m. (Sun)
Manchester City da Chelsea na cikin ƙungiyoyin da suka yi zawarcin ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekra 22,Adam Wharton, kafin a rufe cinikin ƴanwasa, amma Crystal Palace ta ƙi sallama shi. (Guardian)
Aston Villa da Manchester City da kuma Newcastle United na bibiyar ɗanwasan gefen Sifaniya Alex Baena amma Atletico Madrid ba ta da aniyar sayar da ɗanwasan mai shekara 25. (CaughtOffside)
Wolves ta so sayar da ɗanwasan gaban tawagar Portugal ta matasa ƴan ƙasa da shekara 21, Mateus Mane kafin rufe cinikin ƴanwasa, inda Liverpool da kuma Manchester United suka yi zawarcin ɗanwasan mai shekara 18. (Teamtalk)
Arsenal za ta gabatar da tayin £68m kan ɗanwasan gefen Barcelona da Brazil mai shekara 29 Raphinha, a watan Janairu. (Fichajes - in Spanish)
Tottenham na tunanin biyan Richarlison domin warware kwangilar ɗanwasan gaban Brazil ɗin wanda bbai samu karɓuwa ba.(Talksport)
Everton ta gabatar da tayin £40m kan ɗanwasan gaban West Ham da Argentina mai shekara 27, Taty Castellanos amma cinikin bai kammala ba. (Teamtalk)
Dagewar da Kocin Newcastle United Matthias Jaissle ya yi kan ci gaba da zaman ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 31, Jacob Murphy ta sa ƙungiyar ta ƙi amincewa da tayi biyu da Nottingham Forest ta gabatar a kan sa. (Football Insider)















