Mece ce ACF, kuma me ya janyo rikici a cikinta?

Asalin hoton, ACF/Facebookk
Rikicin da ya barke a ƙungiyar tuntuɓa ta ACF ya ɗauki wani sabon salo bayan da jami'an 'yan sanda suka rufe hedikwatar ƙungiyar da ke Kaduna.
Wannan na zuwa ne yayin da wani ɓangare na ƙungiyr ya shirya gudanar da wani taron majalisar zartarwar ƙungiyar na ƙasa.
Wannan takaddama dai ta kaure ne sakamakon zargin da kwamitin amintattu ya yi cewa kwamitin zartaswar ƙungiyar wa'adinsu ya ƙare da kuma zargin karkatar da wasu kuɗaɗe.
Mece ce ACF?
An kafa ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa ko kuma Arewa Consultative Forum da Turanci wato ACF a ranar 7 ga watan Maris na shekarar 2000, inda ofishinta yake a Kaduna, a wani taro da Sarkin Musulmi, Sultan Macciɗo ya jagoranta.
Manufar kafa ƙungiyar shi ne haɗa kan al'ummar mutanen jihohin arewacin ƙasar 19 da kuma kare muradun yankin masu alaƙa da tattalin arziƙi da dimokraɗiyya.
An naɗa tsohon sifeto janar na ƴansandan Najeriya, Alhaji Yusuf Dikko a matsayin shugaban ƙungiyar na farko, inda aka nada Mista Sunday Awoniyi a matsayin shugaban kwamitin amintattu na ACF a 2000.
Taken ƙungiyar shi ne "Arewa Ɗaya, Al'umma Ɗaya, Makoma Ɗaya"
Me yanyo rikici a ACF?
Rahotanni dai na cewa rikicin na da nasaba da taƙaddama kan shugabanci da kuma ikon da ke tsakanin kwamitin zartarwa na ƙasa da kuma kwamitin amintattu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bugu-da-ƙari akwai zarge-zargen rashin gaskiya wajen tafiyar da wasu maƙudan kuɗaɗen ƙungiyar ta ACF da ake zargin an tara bara.
Bayanai na cewa an jima ana wannan taƙaddama 'yan watanni da kammala babban taron ƙungiyar na cikarta shekara 25 da kafuwa inda wasu manyan arewacin ƙasar suka tara maƙudan kuɗaɗe don gyaran yankin.
Rikicin dai ya janyo jami'an 'yan sandan suka yi dirar mikiya tare da garƙame hedikwatar ƙungiyar da ke Kaduna a lokacin da mambobin kwamitin zartarwa na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Barrista Mamman Mike Osuman suka shirya gudanar da taron gaggawa a hedikwatar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamitin ya zargi shugaban kwamitin amintattu, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bashir Dalhatu, da yin katsalandan a harkokin da ba su shafe shi ba.
"Kwamitin amintattu aikinsu dai bayar da shawara ne su kuma kwamitin zartarwa aikinsu zartarwa. To amma sai shi shugaban kwamitin amintattu ya zama duk abin da za a yi a wannan ƙungiyar sai ya yarda sai ya saka hannu. Hatta kuɗaɗen da ƙungiya ta samu ya ɗauka ya kai bankin da shi yake so," in ji Farfesa Tukur Muhammad Baba,kakakin ƙungiyar ta ACF.
Farfesa ya kuma ƙara da zargin Alhaji Bashir Ɗalhatu da ƙoƙarin yin ƙarfa-ƙarfa dangane da sakataren ƙungiyar.
"Sannan kuma ya ce sakatare ya gama wa'adinsa saboda haka ya ba shi zuwa 15 ga wata shi ne kwamitin zartarwa ya ce na haka ake yi ba saboda zaɓen sakatare aiki ne na kwamiti da zai naɗa kuma bai naɗa ba. To shi ne ya kawo rikicin har ta kai ga an turo mana ƴansanda."
Wane martani Bashir Ɗalhatu zai yi?
BBC ta tuntubi shugaban kwamitin amintattun ƙungiyar ta ACF, Alhaji Bashir Dalhatu game da zargin da kwamitin zartarwa ya yi wa kwamitin amintattu da yake jagoranta cewa ya kanakane abubuwan ƙungiyar.
Sai dai Bashir Ɗalhatu ya shaida wa wakilin BBC cewa an shiga wani yanayin da ba zai iya yin wani ƙarin bayani ba.











