Juventus na nazari kan Jackson, ƙungiyoyi da dama na rububin Bowen

Nicolas Jackson

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Juventus na tunanin ɗaukar aron dan wasan gaban Chelsea Nicolas Jackson. Ɗan wasan na Senegal, mai shekara 24, yana zaman aro ne a Bayern Munich amma ba zai ci gaba da zama da zakarun Jamus a kakar wasa mai zuwa ba. (Bild)

Ƙungiyoyin Premier uku da suka haɗa da Liverpool da Newcastle, da Everton sun nuna sha'awa kan ɗan wasan gaban Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 29, ko da kuwa West Ham ta kauce wa faɗawa matakin gasar Championship. (Mail)

Liverpool na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Monaco Magnes Akliouche, mai shekara 24, inda ɗan wasan na Faransa ke da farashin kusan fam miliyan 50. Shi ma abokin wasansa Lamine Camara yana jan hankalin ƙungiyar ta Anfield, amma za ta iya fuskantar hamayya daga Newcastle kan ɗan wasan tsakiyar Senegal mai shekara 22. (L'Equipe).

Da alama Real Madrid za ta buƙaci sayar da ƴan wasa kafin ta kawo wasu sabbin fuskoki, inda ake ganin ɗan wasan tsakiyar Sifaniya Dani Ceballos, mai shekara 29, zai iya shiga cikin waɗanda za ta yi ƙoƙarin sallama a bazara mai zuwa. (The Athletic)

West Ham ta sanya farashin £84m kan ɗan wasan tsakiya na Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21, wanda ke jan hankalin manyan ƙungiyoyi kamar su Manchester United da Paris St-Germain. (Football Insider)

Manchester United na tunanin zawarcin ɗan wasan Atalanta da Brazil Ederson, mai shekara 26, wanda za'a iya siyan shi a kan farashin kusan fam miliyan 40. (Manchester Evening News).

Kocin Barcelona Hansi Flick ya amince da sabon kwantiragin da zai ci gaba har zuwa 2028, tare da zaɗin tsawaitawa na tsawon shekara guda. (Mundo Deportivo)

Ana sa ran Manchester United za ta yi hidima a kasuwar musayar ƴan wasa yayin da take zawarcin ƴan wasa aƙalla biyar da suka haɗa da ƴan wasan tsakiya uku da na baya na gefen hagu da kuma ɗan wasan gaba. (Sun)

Masu tsaron gida biyu na gasar Ligue 1 sun tabbata a matsayin waɗanda za su iya maye gurbin Emi Martinez, inda Aston Villa ta ke nazari kan ɗan wasan Lens Robin Risser da Guillaume Restes na Toulouse - dukansu matasan Faransa ne masu shekara 21. (Foot Mercato)

Ɗan wasan tsakiya na Sporting da Portugal Francisco Trincao, mai shekara 26, yana jan hankalin Liverpool da Chelsea. (Caught Offside)

Ɗan wasan Sunderland da DR Congo Noah Sadiki, mai shekara 21, bai yanke hukuncin barin filin wasan Stadioum of Light ba a bana. (Voetbal Nieuws)