Shin za a iya samar da ciyayi a Sahara?

Vue aérienne d'un champ agricole circulaire et verdoyant bordé par le sable du désert, avec un long pipeline partant d'une petite structure blanche et s'étendant jusqu'à la zone verte.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Idan muka yi tunanin hamada, abin da ke zuwa zuci shi ne yadda ake faɗaɗa sahara.

A zahiri, hamada na da faɗi ɗauke da nau'ika na bishiyu da dabbobi da rayuwar bil adama.

Al Ƙahira, babban birnin Masar ne birni mafi girma da ke da hamada inda ake da fiye da mutane da dabbobi fiye da miliyan 23 da ke zaune a wajen.

Hamada wuri ne a bushe ninda ƙarancin ruwa ke sa yin rayuwa a wajen ta zama abu mai wahala.

Hamada na faɗaɗa. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, kowace shekara ana samun raguwar kusan fili mai girman faɗin kilomita miliyan ɗaya na ƙasa mai albarka.

Yayin da ake ci gaba da samun ƙarancin ƙasa mai albarka a doron ƙasa, akwai yiwuwar a samar da ruwa a kuma mayar da hamada zuwa wajen da shuka za ta rayu.

A sauya yanayi

Des rangées de panneaux solaires réfléchissants s'étendent à perte de vue dans un paysage désertique, installées entre des dunes de sable ondulantes sous un ciel brumeux.

Asalin hoton, VCG via Getty Images

Yan Li, wata farfesa kan ilimin kimiyyar ƙasa a jami'ar Beijing Normal da ke China, ta ce "rasa ƙasa mai albarka na nufin shuka na iya bushewa saboda ƙarancin har daga bisani waje ya koma hamada."

A 1970, masanin kimiyya Jule Charney ya gano cewa wasu ayyuka da jama'a ke yi na taka muhimmiyar rawa a wannan lamari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Idan aka samu dabbobi masu yawa, dabbobin na cin shuka, abin da ke shafar albarkar da ƙasa ke da shi,' kamar yadda Li ta yi wa shirin BBC na CrowdScience bayani.

Idan wuri na janyo zafi a maimakon shanyewa, iskar da ke sama ba ta yin zafi sosai. Hakan na nufin za a samu rashin danshi da kuma haɗuwar girgije, lamarin da zai sa wajen ya zama a bushe.

A cikin shekarun 1970s, wani masanin kimiyya Jule Charney ya gano cewa hada-hadar ɗan adam sun taka muhimmiyar rawa a wannan tsari.

Li ya bayyana wa shirin CrowdScience na BBC cewa "Lokacin da dabbobi suka yi yawa, suna cinye dukkannin ciyayi, abin da ke sa ciyawar ta koma ciki kasa har wajen ya koma yashi."

Lokacin da wannan ya faru, yanayin hange daga nesa yana canzawa, saboda yashi yana da laushi sosai shi ya sa yake ɗaukar hasken rana.

Ya yi iƙirarin cewa amfani da abubuwa masu amfani da hasken rana hanya ce mai kyau don cimma abin da ake so. Saboda suna da duhu, kuma baƙin abu yana da ɗaukar zafi, wanda ke taimakawa wajen ɗumama iska da zafi, da kuma samar da gajimare.

Tawagarsa ta ƙirƙiro wata na'uar da za ta riƙa duba abin da zai faru idan aka rufe kashi 20 na Sahara da farantan samar da lantarki daga hasken rana.

Na'urar ta yi hasashen cewa za a samu ƙaruwar ruwan sama a sahara.

Amma a yanzu tana matakin gwaji ne kawai, kuma za a iya samun ƙaruwar farantan samar da lantarki da hasken rana, inda za su mamaye kusan faɗin kilomita miliyan biyu. Kusan girman Indonesiya ko Mexico kenan.

Li ya yi bayanin cewa wannan tsarin zai yi aiki ne kawai a wuraren da suke da sahara ko kusa da teku, inda ake samun yanayi mai ɗumi.

Yawancin yankunan sahara irinsu Gobi da kuma waɗanda ke Gabas ta Tsakiya suna nesa da tekuna ne.

Giragizai

Au sommet d'une montagne se trouvent deux grandes toiles maintenues à la verticale par des poteaux en bois, avec des bacs placés en dessous ; un homme se tient debout à proximité, dos à la caméra.

Asalin hoton, MARTIN BERNETTI/AFP via Getty Images

Wani wurin da ake ganin ya fi ko ina bushewa da tsandauri a duniya shi ne Saharar Atacama da ke Chile, amma wata fasaha ta nuna cewa za a iya samun ruwa a wajen.

Virginia Carter, ƙwararriya ce a fannin ilimin ƙasa kuma mataimakiyar farfesa a jami'ar Universidad a Chile, ta yi bayanin cewa: "Girbin da ake yi ya samo asali ne a Chile kimanin shekaru 50 da suka gabata. Wato dabarar samun ruwa daga giragizai a sahara."

Ms. Carter ta ce za a iya samun aƙalla lita biyu a kowace mita a rana a arewacin Chile, inda za a iya samun sama da lita bakwai a wasu wuraren.

To ko haƙon da ake yi a zai iya sa Sahara ta koma kore shar?

Ms. Carter tana ganin abu ne mai yiwuwa. Tawagar ta yanzu haka tana wani shiri a saharar Atacama inda ake amfani da ruwan da aka haƙo domin daidaita yanayin.

Amma kuma akwai koma baya. Ruwan da za a iya samu bai kai abin da ake samu a wasu wuraren idan aka kwatanta da wasu dabarun ba.

Daga ruwan teku zuwa tsaftattacen uwa

Des rangées de tuyaux verts parallèles s'étendent depuis une plate-forme métallique surélevée jusqu'au sol pavé en contrebas ; on aperçoit la mer juste derrière.

Asalin hoton, Clea Rekhou/The Washington Post via Getty Images

Yayin da ruwan tekunan duniya ke ƙaruwa, ko hakan zai sa a iya janyo ruwa daga nan?

Yayinda janyo ruwan teku zai fi maida hankali wajen amfani da kimiyya, tsarin da ake amfani da shi na buƙatar na'urori masu ƙarfi da kuma makamashi.

Christopher Sansom, Farfesa ne a jami'ar Derby, yana ƙera wasu na'urorin da za su iya janyo ruwan ta hanyar amfani da hasken rana.

Wannan tsarin yana amfani da hasken rana, inda ya ke tafas ruwan da kuma raba shi da gishirin.

Amma kuma domin biyan buƙatun ɗan'adam da kuma samar da ciyayi a sahara, dole a bi tsarin janyo ruwa.

Za a iya amfani da kowane irin salo, amma abin da ake fata shi ne a yi amfani da tsarin da ba zai cutar da muhalli ba.

Shin za mu iya tabbatar da hakan?

Un homme portant un foulard chevauche un âne sur un étroit sentier de pierre creusé dans un canyon rocheux, bordé de part et d'autre par de abruptes parois de grès.

Asalin hoton, STR/NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Miliyoyin mutane ne ke zaune a yankunan da ke da sahara

A haka dai, za a iya maida sahara ta koma kore shar ta hanyar amfani da ruwan teku da amfani da giragizai domin samar da yanayin da sauya saharar.

Amma kuma sahara ba su da wata matsala. Sahara wuri ne da haka aka halicce shi a duniya. "Idan sahara ta daidaita, komai zai kasance lafiya. Za mu iya barin abin a haka," in ji Li.

"A madadin ƙoƙarin maida sahara kore ta hanyar janyo ruwa, ina tunanin zai fi muhimmanci mu kare rayuwar da take wurin," in ji Zinnia Gonzalez Carranza, wata ƙwararriya a fannin kimiyyar tsirrai a jami'ar Nottingham.

Ta ce ƙoƙarin maida sahara kore zai iya haifar da illa ga muhalli da mutanen da ke zaune a wurin.

"Abin da nake ganin ya kamata mu yi shi ne mu fahimci sahara, mu mutunta yanayin da wurin ke ciki, sai mu yi ƙoƙarin yin aiki da hakan," in ji ta.