Manyan ƙalubale da ke hana matasa yin takara a Najeriya

..

Asalin hoton, NotTooYoungToRun/Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Duk da cewa tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari ya saka hannu a dokar da ta bai wa matasa damar tsayawa takara a 2018, amma har yanzu masu karancin shekaru na fuskantar tarnaƙi iri-iri a siyasa ƙasar.

A duk lokacin da zaɓe ya ƙarato a Najeriya, ana ganin matasa ne suka fi cika filayen yaƙin neman zaɓe da tarukan siyasa - su ne ke liƙa fastoci da yaɗa saƙonni a kafafen sada zumunta da kuma zagaya unguwanni suna neman ƙuri'u domin 'yan takara.

To amma idan aka duba cikin jerin masu neman kujerun siyasa, sai a tarar cewa matasa kaɗan ne ke samun damar shiga takara.

Wannan lamari ya daɗe yana jawo muhawara a tsakanin al'umma, musamman ganin cewa matasa su ne mafi rinjaye a Najeriya.

Duk da yawan kiraye-kirayen da ake yi na bai wa matasa dama a shugabanci, har yanzu da yawa daga cikinsu na kallon siyasa a matsayin wata hanya mai cike da wahala, kuɗi da kuma tasirin masu ruwa da tsaki.

Wasu matasan na da buri da hangen nesa na kawo sauyi a al'ummarsu, amma suna ganin akwai manyan ƙalubale da ke hana su taka rawar azo-a-gani a siyasa.

BBC ta tattauna da wasu matasa da kuma masana kimiyyar siyasa domin ji daga bakinsu.

'Tsadar takara ta hana ni fitowa'

Sani Musa matashi ne mai shekara 37 da ke gwagwarmayar siyasa a jihar Kano kuma ya ce ya kwashe shekara da shekaru yana bauta wa ƴan siyasar jihar ba tare da samun damar tsayawa takara ba wadda ita ce babban burinsa.

Matashin ya ce tun yana jami'a yake sha'awar shiga siyasa saboda yana ganin matasa na da rawar takawa wajen kawo cigaba.

Ya ce sau da dama yana tunanin tsayawa takarar kansila a yankinsu amma matsalar kuɗi na hana shi.

"Ko neman tikitin jam'iyya ma yana buƙatar kuɗi mai yawa, idan ka je taro, mutane suna kallon abin da za ka bayar ne kawai ba abin da za ka faɗa ba." in ji shi.

Sani ya kuma lissafa wasu ƙalubale da ya ce ƙari ne kan matsalar tsadar takara:

  • Rashin damar fitowa a Jam'iyyu: Wasu jam'iyyun siyasa ba sa bai wa matasa dama sai idan suna da kuɗi ko alaƙa da masu ruwa da tsaki.
  • Matsin lamba daga iyaye da abokai: Matashin ya ce baya ga matsalar kuɗi, wasu iyaye da abokai na ganin siyasa ba ta dace da matashi mai ƙaramin ƙarfi ko wanda bai gama kafa rayuwarsa ba, saboda haka bai kamata ya nemi tsayawa takara ba.

"Nima na fuskanci wannan ƙalubalen kuma yana da karya ƙwarin gwiwa ƙwarai da gaske," in ji Sani Musa.

'Siyasa sai da ubangida'

Ita kuma Maryam Abdullahi mai shekara 29 daga jihar Neja dake tsakiyar Najeriya ta ce ta taɓa shiga harkokin jam'iyya da niyyar tsayawa takarar kansila, amma daga baya ta ja da baya saboda yadda tsarin siyasar ke tafiya - dole sai kana da uban gida wanda ya tsaya maka.

"Na fahimci cewa ba wai ƙwarewa ko ra'ayin cigaba ake dubawa ba kawai. A wasu lokuta sai ka kasance kana da uban gida ko mutanen da za su ɗaga ka," in ji ta.

Maryam ta kuma ƙara da wasu matsalolin da ta ce a fahimtarta su ma sun zama ƙalubale ga siyasar matasa da burinsu na tsayawa takara.

  • Kasancewa mace: Maryam ta ce kasancewarta mace kuma matashiya ya ƙara sanya wasu ba sa ɗaukarta da muhimmanci.
  • Rashin wakilcin matasa a manyan muƙamai: Matsahiyar ta ce duk da cewa matasa su ne mafi yawan al'umma a Najeriya, har yanzu ba kasafai ake ganin su a manyan kujerun gwamnati ko shugabanci ba. Yawancin mukamai na siyasa na hannun manya ne da suka daɗe suna mulki.

"Karancin ganin matasa a manyan kujeru kan rage wa sauran matasa ƙwarin gwiwar shiga siyasa, domin suna ganin tsarin bai buɗe musu ƙofa sosai ba," in Maryam.

  • Tashin hankali da barazanar tsaro: A wasu lokuta, siyasa a Najeriya na tare da rikice-rikice, faɗa tsakanin magoya bayan jam'iyyu, ko barazana daga masu fada a ji. Wannan na sanya matasa da dama tsoron shiga harkar siyasa saboda gudun shiga hatsari.

"Lokutan zaɓe musamman kan kasance masu tada hankali a wasu yankuna, abin da ke sa iyaye hana 'ya'yansu shiga harkar siyasa."

  • Rashin horaswa da fahimtar siyasa: "Ba duk matasa ne ke samun damar koyon yadda siyasa da shugabanci ke aiki ba. Rashin horaswa, jagoranci da shirye-shiryen da za su taimaka musu kan rage musu damar shiga siyasa cikin ƙwarewa." in ji Maryam.
  • Tsoron fuskantar cin zarafi a kafofin sada zumunta: Maryam ta ƙara da cewa a yanzu siyasa na tafiya tare da suka da cin mutunci musamman a kafafen sada zumunta. Wasu matasa kan ji tsoron shiga siyasa saboda gudun zagi, ɓata suna ko cin mutunci daga mutane.

Me masana ke cewa?

..

Asalin hoton, NotTooYoungToRun/Facebook

Bayanan hoto, Marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammdu Buhari kenan yake saka hannu a dokar a ranar 31 ga watan Mayun 2018.

Ƙari bisa abubuwan da matasan suka lissafa, Farfesa Abubakar Umar Kari, malami a jami'ar Abuja ya shaida wa BBC cewa akwai wasu matsalolin da suke kallo a kimiyyance.

  • Manyan mutane sun mamaye jam'iyyun siyasa: Farfesa Abubakar Umar Kari ya ce wannan na daga cikin manyan matsalolin da matasa ke fuskanta musamman manyan jam'iyyu. A cewarsa, waɗannan mutane ne ke da ikon yanke shawarar wanda zai tsaya takara da wanda ba zai tsaya ba. Ya bayyana cewa hakan na hana matasa damar fitowa su fafata cikin adalci, saboda tsarin jam'iyyun ba ya bai wa kowa dama iri ɗaya.
  • Rashin dimokraɗiyya a cikin gida: Masanin ya ce rashin dimokraɗiyya a cikin gida na daga cikin abubuwan da ke hana matasa samun dama. Ya ce a maimakon a bari a yi zaɓe ko a gwabza takara cikin gaskiya, sai wasu shugabanni su riƙa ɗora mutanen da suke so. A cewarsa, galibi waɗannan mutane sukan kasance masu biyayya ga masu ruwa da tsaki, ba wai waɗanda jama'a ko matasa suke so ba.
  • Ana fifita 'yan lele a kan masu ƙwarewa: Farfesa Kari ya yi zargin cewa a wasu lokuta ba a duba ƙwarewa ko hangen nesa wajen zaɓar 'yan takara. Ya ce an fi bai wa waɗanda suke kusa da masu faɗa a ji dama, ko da kuwa akwai matasa masu ilimi da tunanin kawo sauyi. Ya ce hakan na sa matasa da dama su rasa ƙwarin gwiwar shiga siyasa.
  • Rashin amincewa da muryar matasa da murandunsu: Matashin ya ƙara da cewa wasu mutane har yanzu na kallon matasa a matsayin marasa gogewa, duk da cewa suna da sabbin tunani da kuzarin kawo sauyi.
  • Mata matasa sun fi fuskantar ƙalubale: Farfesan ya ce mata matasa sun fi fuskantar matsaloli a harkar siyasa idan aka kwatanta da maza. Ya bayyana cewa baya ga matsalar kuɗi da tsarin jam'iyya, mata kan fuskanci ƙalubalen al'ada da wariya daga al'umma. Ya ce hakan na rage yawan mata masu sha'awar tsayawa takara ko shiga manyan mukaman siyas.
  • Amfani da matasa a lokacin yaƙin neman zaɓe kawai: "A lokuta da dama ana amfani da matasa wajen yakin neman zaɓe, amma idan lokacin bada muƙami ya zo sai a ware su." in ji Farfesa Kari.

Mafita

Matasan Najeriya dai na ci gaba da nuna sha'awar ganin an samu sauyi a siyasa, amma har yanzu suna fuskantar manyan ƙalubale da ke hana su shiga siyasar gaba ɗaya.

Duk da yawan alƙawuran da ake yi na bai wa matasa dama, har yanzu suna jin kamar an bar su a baya.

Kuma a yayin da ake ƙara tunkarar kakar zaɓen 2027, masana irin su Farfesa kari na bayar da shawarar bai wa matasan dama kasancewar su ne manyan gobe. Sai dai kuma ya ce dole ne sai an samar da wasu abubuwa kamar haka:

  • Ingantacciyar dimokraɗiyyar cikin gida
  • Amincewa da muryar matasa da muradunsu
  • Fifita ƙwarewa kan kuɗi ko kusanci
  • Matasa su daina yadda ana amfani da su a ƴan barandan siyasa.