Hanyoyi 5 da ake iya sa EFCC ta ƙaddamar da bincike kan mutum

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta'annati ta Najeriya (EFCC) na da ikon gayyatar duk wani mutum da take zargi da aikata laifuffukan da suka shafi almundahana da dukiya ko kuma cin hanci da rashawa.

Hukumar EFCC mai zaman kanta ce, wadda aka sha ganin tana gayyatar manyan mutane a Najeriya, kuma da dama daga cikin 'yan ƙasar na fargabar amsa gayyatarta.

To amma, waɗanne dalilai ne ke sa hukumar ta ƙaddamar da bincike kan mutum?

BBC ta tattauna da masana dokoki, inda wani lauya a Najeriya, Barista Hamza Nuhu Dantani, ya bayyana hanyoyi biyar da za su iya sa EFCC ta gayyaci mutum ko kuma ta ƙaddamar da bincike a kansa.

EFCC da kanta

EFCC na da ikon gudanar da bincike kan zargin aikata laifukan almundahana da dukiya bisa tanadin dokar da ta kafa ta.

A ƙarƙashin sashe na 6(d) na dokar, hukumar na da hurumin binciken laifukan da suka shafi zamba da sauran laifukan tattalin arziki da kuɗi.

Haka kuma, tana iya bin diddigin kadarori ko asusun da ake zargin suna da alaƙa da laifuka, tare da neman matakan doka da suka dace domin ƙwace su.

A cewar Barista Dantani, waɗannan hukumce-hukumcen na cikin ikon da EFCC ke da shi wajen gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi da aikata irin waɗannan laifuka.

Ta hanyar kai ƙorafi a rubuce

Barista Dantani ya ce sashe na 6(h) na dokar EFCC ya bai wa kowa damar kai ƙorafi ga hukumar, ta hanyar rubutu ko baki, idan yana da bayanan da ke nuna yiwuwar aikata almundahana.

Ya ce ƙungiyoyi ma za su iya amfani da wannan dama wajen gabatar da ƙorafi a rubuce, tare da bayanan da za su taimaka wa hukumar wajen gudanar da bincike.

A wasu lokutan, ƙungiyoyin da ke rajin kare dukiyar al'umma da masu sa ido kan ayyukan gwamnati kan gudanar da zanga-zanga domin neman a binciki wani mutum kan zargin almundahana.

Haka kuma, ba lallai sai wanda ya kai ƙorafin ne wanda aka zalunta ko aka yi wa wani laifi ba.

Mutum ko ƙungiya na iya kai ƙorafi idan sun samu bayanan da ke nuna yiwuwar almundahana da dukiyar jama'a.

Sai dai EFCC ce ke da alhakin tantance bayanan da aka gabatar mata da kuma yanke shawarar ko akwai dalilin buɗe bincike kan zargin.

Haɗa hannu da wata hukuma

A ƙarƙashin tanade-tanaden dokar EFCC, hukumar na iya haɗa kai da wasu hukumomin tsaro ko na gwamnati wajen gudanar da bincike kan mutum ko zargin aikata almundahana.

Barista Dantani ya ce hukumomin tsaro, irin su 'yan sanda da sojoji, ko wasu ma'aikatun gwamnati, na iya bayar da bayanan da za su taimaka wajen binciken wasu laifuka.

Sai dai Barista Dantani ya ce bai dace wata hukuma ko gwamnati ta yi amfani da ƙarfin ikonta wajen musgunawa mutum saboda saɓanin da ke tsakaninsu, ko kuma domin tozarta shi ba.

Ya ce a wasu lokutan hukumomi kan yi amfani da irin wannan dama ne kawai domin a binciki mutanen da suke adawa da su.

A cewarsa, irin wannan hali na iya rage tasiri da kuma zubar da martabar hukumar da aka yi amfani da ita.

Kwarmata bayanai

EFCC na iya fara bincike kan mutum bayan samun bayanan sirri daga wani mutum ko wata majiya da ke zargin cewa an aikata almundahana.

Ana iya kwarmata bayanai ga EFCC ba tare da bayyana sunan wanda ya bayar da su ba, domin kare sirrinsa da kuma kauce wa duk wani abin da ka iya jefa shi cikin matsala.

Sai dai Barista Dantani ya ce yana da kyau a gabatar da ƙorafi a rubuce tare da hujjoji, domin hakan zai taimaka wajen tabbatar da bayanan da kuma amfani da su a matsayin shaida idan binciken ya kai ga kotu.

Duk da haka, ya jaddada muhimmancin kare sirrin mutanen da suka bayar da bayanai, musamman idan bayyana sunayensu zai iya jefa su cikin barazana ko wata illa.

Sai dai samun irin waɗannan bayanai ba ya nufin an tabbatar da zargin, domin hukumar ce ke da alhakin tantance sahihancinsu da gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Idan mutum na kashe kuɗin da ya wuce ƙarfinsa

Idan aka lura cewa mutum na kashe kuɗaɗe fiye da yadda matsayinsa ko abin da yake samu zai iya ɗauka, hakan na iya jawo hankalin EFCC ta ƙaddamar da bincike a kansa.

Alal misali, Barista Dantani ya ce idan ƙaramin ma'aikacin gwamnati ko malamin makaranta ya fara yin waɗaka da kuɗi, tare da mallakar kadarori ko gudanar da rayuwar jin daɗi da ba ta yi daidai da abin da yake samu ba, hukumar na iya fara binciken tushen arzikinsa.

Ya bayyana cewa irin wannan bincike na iya taimaka wa hukumar wajen gano ko akwai wasu hanyoyin samun kuɗi da ba su dace ba, musamman idan aka samu alamun cewa kadarorin ko kuɗaɗen da mutum ke kashewa na iya kasancewa sakamakon almundahana ko wani laifi da ya shafi tattalin arziki.

Shin ana iya sake buɗe bincike bayan shekaru?

Barista Dantani ya ce ana iya sake buɗe bincike kan wani batu ko da bayan shekaru sun, muddin ba a kammala binciken ba ko kuma kotu ba ta yanke hukunci kan batun ba.

Ya ce idan an kammala bincike kuma kotu ta wanke wanda ake zargi, hakan na iya shafar yiwuwar sake binciken batun, gwargwadon yanayin shari'ar da kuma tanade-tanaden doka.

Saboda haka, ya bayyana cewa ana iya sake duba wani batu idan buƙatar hakan ta taso, musamman idan akwai wasu sababbin bayanai ko hujjoji da suka taso.

Ya ƙara da cewa ba lallai ba ne EFCC ta gudanar da bincike kan duk wani ƙorafi da aka gabatar mata.

Sai dai yana da muhimmanci hukumar ta tantance ƙorafe-ƙorafen da take samu kafin yanke shawarar fara bincike ko kuma kai mutum kotu.

Barista Dantani ya ce domin kare martabarta da ƙimarta a idon duniya, ya kamata EFCC ta guji zama hanyar da mutane za su riƙa amfani da ita wajen cimma muradunsu na kashin kai ta hanyar shigar da ƙorafe-ƙorafe marasa tushe.