Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashe 7 da ma'aurata suka fi samun gamsuwa
Bincike ya nuna cewa manya da matasa a Birtaniya na yin jima'i ƙasa da yadda aka saba a baya
Wani sabon bincike da aka gudanar a ƙasar ya nuna cewa manya na yin jima'i sau kaɗan idan aka kwatanta da shekarun baya, inda matasa ke cikin rukunin da wannan sauyi ya fi shafa.
Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet ya nuna cewa mutanen da shekarunsu ba su kai 45 ba, a yanzu suna yin jima'i sau biyu a wata ne kacal, idan aka kwatanta da sau huɗu a wata a tsakanin shekarar 1990 zuwa 1991.
A cikin matasa masu shekaru 16 zuwa 24, mutum ɗaya cikin uku bai taɓa yin jima'i ba.
A binciken da aka gudanar tsakanin shekarar 1990 da 2010, adadin ya kasance kusan mutum ɗaya cikin biyar.
Sai dai yawan yin jima'i ba lallai ne ya nuna cewa mutum ya fi gamsuwa da rayuwarsa ta soyayya da jima'i ba.
Wani bincike na ƙasashe daban-daban da cibiyar binciken ra'ayin jama'a ta Ipsos ta gudanar ya nuna cewa akwai babban bambanci tsakanin ƙasashe dangane da yawan mutanen da suka gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Binciken, wanda ya ƙunshi mutane 23,765 daga ƙasashe 30, an gudanar da shi tsakanin watan Disamban 2024 da Janairun 2025.
An tambayi waɗanda suka bayar da gudummuwa a binciken game da yadda suka gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Sakamakon binciken ya bayyana ƙasashe bakwai da suka fi samun kaso mafi yawa na mutanen da suka gamsu da rayuwarsu ta wannan fuskar, inda aka fara da ƙasashe uku da suka zo matsayi na biyar tare.
7. Malaysia
Malaysia na cikin ƙasashe uku da suka zo matsayi na biyar tare, inda kashi 67 cikin 100 na waɗanda suka shiga binciken suka ce sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
A cikin wannan kaso, kashi 30 sun ce sun gamsu matuƙa, yayin da kashi 37 suka ce sun gamsu kaɗan. A gefe guda kuma, kashi 15 ba su gamsu sosai ba, yayin da kashi takwas ba su gamsu ko kaɗan ba.
Wannan sakamako ya sanya Malaysia cikin ƙasashen Asiya da suka samu babban kaso na mutanen da suka gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i a wannan bincike, duk da bambancin matakin gamsuwar da aka samu tsakanin mahalarta.
6. Peru
Ƙasar Peru ma ta zo matsayi na biyar tare da wasu ƙasashe, inda kashi 67 cikin 100 na wadanda suka bayar da gudummuwa a binciken suka bayyana cewa sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Binciken ya nuna cewa kashi 37 cikin 100 na mutane a ƙasar sun ce suna samun gamsuwa matuƙa, yayin da kashi 30 suka ce gamsuwar ta su ƙalilan ce.
Wannan na nuna cewa mafi yawan mahalarta binciken na da kyakkyawan ra'ayi game da rayuwarsu ta jima'i.
Peru na cikin ƙasashen Latin Amurka da suka samu babban kaso na mutanen da suka gamsu da rayuwarsu, inda ta kasance tare da wasu ƙasashen yankin da suka zo kan-kan-kan
5. Chile
Chile ma na cikin jerin ƙasashen da suka zo matsayi na biyar tare, inda kashi 67 cikin 100 na mutanenta suka ce sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Ba kamar Malaysia da Peru ba, Chile ta samu kaso mafi yawa na mutanen da suka ce sun gamsu matuƙa, inda suka kai kashi 43 cikin 100. Sauran kashi 24 sun ce sun gamsu kaɗan.
A yankin Latin Amurka, wannan sakamako ya sanya Chile cikin ƙasashen da suka samu babban kaso na mutanen da suka gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i, sai dai Colombia da Mexico sun fi ta matsayi a jerin.
4. Indonesia
Indonesia ta zo matsayi na huɗu, inda kashi 70 cikin 100 na waɗanda suka shiga binciken suka bayyana cewa sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Wannan sakamako ya sanya ta cikin ƙasashen Asiya da suka samu babban kaso na mutanen da suka gamsu a binciken.
Bisa ga ƙididdigar binciken, kashi 32 cikin 100 na mahalarta sun ce sun gamsu matuƙa, yayin da kashi 38 suka ce sun gamsu kaɗan.
Hakan na nuna cewa mafi yawan mahalarta sun faɗa cikin waɗannan rukunan biyu.
Indonesia ta samu kaso mafi girma idan aka kwatanta da matsakaicin kaso na dukkan ƙasashe 30 da suka shiga binciken, wanda ya kasance kashi 59 cikin 100.
Wannan na nuna bambancin matakin gamsuwa tsakanin mahalarta daga Indonesia da matsakaicin sakamakon binciken baki ɗaya.
3. Thailand
Thailand ta samu matsayi na biyu a bayan Mexico, inda kashi 72 cikin 100 na mahalarta binciken suka ce sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da kuma jima'i.
Binciken ya nuna cewa kashi 24 sun ce sun gamsu matuƙa, yayin da kashi 48 suka ce sun gamsu zuwa wani mataki.
Wannan na nuni da cewa mafi yawan waɗanda suka gamsu sun kasance cikin rukunin masu gamsuwa zuwa wani mataki, maimakon waɗanda suka gamsu sosai.
Thailand ta kuma samu sakamako mai kyau a ɓangaren gamsuwa da abokan soyayya ko ma'aurata.
Daga cikin mahalarta binciken da ke cikin alaƙar soyayya, kashi 44 sun ce sun gamsu matuƙa da abokan zamansu, yayin da kashi 48 suka ce sun gamsu zuwa wani mataki.
2. Mexico
Ƙasar Mexico ta zo matsayi na biyu tare da Thailand, inda kashi 72 cikin 100 na mahalarta binciken suka bayyana cewa sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Ba kamar Thailand ba, Mexico ta samu kaso mafi yawa na mutanen da suka ce sun gamsu matuƙa, inda suka kai kashi 42 cikin 100. Sauran kashi 30 sun ce sun gamsu kaɗan.
Haka kuma, Mexico na cikin ƙasashen da suka fi samun kaso mai yawa na mutanen da suka ce suna jin ana ƙaunarsu, inda kashi 86 cikin 100 na mahalarta binciken suka bayyana cewa suna jin ana ƙaunarsu.
Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da cibiyar Ipsos ta bincika a yayin tantance matakin gamsuwar mutane da rayuwarsu ta soyayya.
1. Colombia
Ƙasar Colombia ce ta zo ta farko, inda kashi 74 cikin 100 na mahalarta binciken suka bayyana cewa sun gamsu da rayuwarsu ta soyayya da jima'i.
Wannan shi ne kaso mafi girma a tsakanin ƙasashe 30 da suka shiga binciken.
A cikin wannan kaso, kashi 48 cikin 100 sun ce sun gamsu matuƙa, yayin da kashi 26 suka ce sun gamsu kaɗan.
Hakan na nuna cewa kusan rabin mahalarta binciken a ƙasar sun nuna gamsuwa sosai da rayuwarsu ta jima'i.
Colombia ta kuma zo ta farko wajen gamsuwa da dangantakar soyayya.
Daga cikin mahalarta binciken da ke cikin alaƙar soyayya, kashi 65 cikin 100 sun ce sun gamsu matuƙa da abokan zamansu, yayin da kashi 24 suka ce sun gamsu kaɗan.