Wane ne tsohon sojan Amurkan da za a nuna zartar da kashe shi kai tsaye?

    • Marubuci, Sareen Habeshian
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta sanar da cewa za ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbin bindiga kan tsohon Manjo a rundunar sojin Amurka, lamarin da zai kasance kisan soja na farko da aka aiwatar cikin fiye da shekara 60.

An samu Nidal Hasan da laifin ya harbe tare da kashe sojojin Amurka 13 da ba su ɗauke da makami a sansanin soji na Fort Hood a shekara ta 2009, sannan ya jikkata wasu mutum 32.

Mai magana da yawun Pentagon, Sean Parnell, ya sanar a shafukan sada zumunta ranar Litinin cewa Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ne ya bayar da shawarar aiwatar da hukuncin, kuma Shugaba Donald Trump ya amince da ita.

Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka ya faɗa a ranar Talata cewa an tsara gudanar da hukuncin a sansanin Fort Hood da ke jihar Texas a ranar 3 ga watan Disamba.

Hukuncin zai kasance na farko da rundunar sojin Amurka za ta aiwatar ta hanyar harbin bindiga tun bayan ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu.

"An saka ranar yanke hukunci ga Hasan," in ji Parnell a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

Wane ne Hasan Nidal, kuma me ya aikata?

Hasan likitan ƙwaƙwalwa ne a rundunar sojin Amurka kuma ɗan asalin jihar Virginia.

A shekarar 2009 ya kashe sojoji 13 a sansanin soji da ke Texas.

Daga baya ya amsa a kotu cewa shi ne ya aikata harin, sannan ya nemi afuwa kan "duk wasu kura-kuran" da ya yi.

A lokacin shari'arsa ta kotun soja a shekarar 2013, ya ce ya yi imanin cewa yana kare Musulmi da kuma ƙungiyar Taliban a Afghanistan.

Kisan da aka yi a ranar 5 ga Nuwamban 2009 shi ne hari mafi muni da aka taɓa kai wa sansanin sojin Amurka wanda ba a lokacin yaƙi ba.

Harin ya faru ne a wani ginin lafiya da ke cike da jama'a, inda sojojin da ake shirin

Matakan aiwatar da hukuncin kisa a Amurka

Hasan na ɗaya daga cikin fursunoni huɗu da ke jiran aiwatar musu da hukuncin kisa a tsarin shari'ar rundunar sojin Amurka.

A ƙarƙashin dokokin soja na Amurka, dole ne shugaban ƙasar ya amince kafin a aiwatar da hukuncin kisa kan wani soja.

Haka kuma, dole ne a kammala duk matakan ɗaukaka ƙara tare da yanke hukunci na ƙarshe kan sahihancin hukuncin kafin a ci gaba da aiwatar da shi.

A shekarar 1983, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Rundunar Soji ta Amurka ta yanke cewa hukuncin kisa a tsarin soja ya saɓa wa kundin tsarin mulki, sai dai daga baya an dawo da shi ta hanyar umarnin shugaban ƙasa a zamanin tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan.

Bambancin hukuncin soji da na farar hula

Hukuncin kisan da rundunar soji ke aiwatarwa ya bambanta da wanda jihohi ke aiwatarwa.

Yawancin hukuncin kisa da ake aiwatarwa a Amurka jihohi ne ke gudanar da su, inda jihohi 27, da rundunar soji, da kuma gwamnatin tarayya har yanzu suke da damar amfani da hukuncin kisa a matsayin wani zaɓi da doka ta tanada.

Kisa ta hanyar harbin bindiga ba kasafai ake amfani da ita ba.

A bara, an aiwatar da irin wannan hukunci a jihar South Carolina, wanda shi ne karo na farko da aka yi hakan a jihar, kuma karo na farko a Amurka cikin shekara 15 da aka yi amfani da wannan hanya.

Wasu jihohi huɗu ma suna ba da damar amfani da harbin bindiga wajen aiwatar da hukuncin kisa, ciki har da Idaho da Mississippi da Oklahoma da Utah.

Shugaba Donald Trump ya kasance mai goyon bayan hukuncin kisa a matakin tarayya, kuma ya mayar da shi aiki ta hanyar umarnin zartarwa da ya sanya wa hannu a ranar farko ta gwamnatinsa a watan Janairun 2025.

A zamanin wanda ya gada, tsohon Shugaba Joe Biden, Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta dakatar da aiwatar da hukuncin kisa a matakin tarayya.

Umarnin zartarwar da Trump ya sanya wa hannu ya bayyana hukuncin kisa a matsayin "wani muhimmin kayan aiki na hana aikata manyan laifuka da kuma hukunta waɗanda suka aikata munanan laifuka da ayyukan tashin hankali da suka yi sanadin salwantar rayukan 'yan ƙasar Amurka."

Wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka ya shaida wa BBC cewa za a fitar da ƙarin bayanai daga baya kan yadda za a watsa aiwatar da hukuncin kisan kai tsaye.

Bayanan ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International sun nuna cewa ƙasashen da suka fi yawan aiwatar da hukuncin kisa a bara su ne China da Iran da Saudiyya da Yemen da kuma Amurka.

Shugaba Donald Trump ya soke dakatarwar aiwatar da hukuncin kisa na gwamnatin tarayya da magabacinsa Joe Biden ya kafa, bayan ya koma Fadar White House.

Wani bincike da cibiyar Pew Research ta gudanar a watan Yuli ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Amurkawa na goyon bayan aiwatar da hukuncin kisa ga masu laifin kisan kai, adadin da ya ƙaru da maki shida cikin shekaru biyar da suka gabata.

Kisan soja na ƙarshe da aka aiwatar ta hanyar harbin bindiga ya faru ne a watan Janairun shekara ta 1945, lokacin da aka harbe Eddie Slovik, wani matashin sojan Amurka da ya gudu daga aiki, a watannin ƙarshe na Yaƙin Duniya na Biyu.