'Da dala muka biya kuɗin fansa kafin a sako yaranmu'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ɗaya daga cikin iyayen matasa masu hidimar ƙasa (nysc) 20 da aka saki bayan an yi garkuwa da su a jihar Imo, Kudu maso gabashin Najeriya ya shaida wa BBC cewa masu garkuwa da yaran sun karɓi kudin fansa da dalar Amurka kafin sakin matasan.

Mutumin da bai so a faɗi sunansa ba ya yi iƙirarin cewa babu wata hukumar tsaro da ta taka rawa wajen sakin ƴaƴan nasu.

Biyan kudin fansa haramun ne a dokokin Najeriya.

Haka nan a farkon mako rundunar ƴansanda ta Najeriya ta ce ta gano wurin da ake tsare da matasan kuma tana ƙoƙarin karɓo su, duk da cewa ba za ta iya shiga dajin ba saboda bayanai sun nuna cewa an dasa nakiyoyi.

Sai dai a ranar Laraba rundunar ƴansandan ta Najeriya ta sanar da ceto matasan ƴan hidimar ƙasa guda 20 bayan abin da ta bayyana "gagarumin aikin ceto".

Sai dai wasu iyaye da suka tattauna da BBC sun ce: "Babu wani da ya sanya hannu wajen ceto ƴaƴanmu. Iyaye da da abokai ne suka harhaɗa kudi domin biyan kudin fansar da masu garkuwa da mutane suka buƙata."

Iyayen yaran da aka sace sun kuma ce jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun yi ƙoƙari wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, inda suka gayyaci iyayen domin su taimaka wajen gudanar da bincike.

Wani daga cikin iyayen ya ce DSS na da cikakken bayani kan yadda suka canza kuɗaɗen zuwa dalar Amurka ta hannun wani mai canjin kuɗi kafin su miƙa kuɗin ga masu garkuwa da mutanen.

"Kuɗin suna da yawa sosai. Ba ƙananan kuɗi ba ne."

Sai dai ya ƙi faɗin adadin kuɗin da aka biya a matsayin kuɗin fansa.

Mutanen da aka sace sun shafe kusan mako guda a hannun masu garkuwa da su kafin a sako su.

Wata uwa da ta yi magana da wani gidan jarida ta bayyana cewa ita ta biya naira miliyan shida domin a sako ɗanta bayan tattaunawa da masu garkuwa da mutanen. Amma ta jaddada cewa ba adadin kuɗin da kowane iyaye suka biya ba ne, domin

'Ɗana ba zai ci koma ba'

Iyalan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace sun ce yaronsu ba zai ci gaba da yi wa NYSC hidima ba idan har za a tilasta masa komawa jihar da aka fara tura shi.

Iyayen sun ce idan aka sauya masa wurin yi wa ƙasa hidima zuwa Jihar Oyo ko Jihar Ogun, to zai ci gaba da kammala shekarar hidimar tasa.

A ranar Laraba, rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwa inda ta bayyana cewa an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, tare daukar iƙrarin nasarar aikin ceto yaran.

'Yan sandan sun ce an ceto mambobin NYSC ɗin ne a ƙauyen Amakohia Ubi da ke Jihar Imo.

Mai magana da yawun rundunar, Ani Iniedu, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda ke da hannu a satar mutanen, yayin da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro ke gudanar da ayyukan haɗin gwiwa domin tabbatar da an gurfanar da masu laifin gaban shari'a.

Ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun gudanar da bincike bisa bayanan sirri a dazuka da wuraren da ake zargin masu garkuwa da mutane na amfani da su a matsayin mafaka.

Sai dai bai ambaci ko an biya kuɗin fansa ba ko kuma an kama wani daga cikin masu garkuwar ba.

A nasa ɓangaren, gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya yaba wa jami'an tsaro bisa abin da ya kira gaggawar ɗaukar mataki, haɗin kai da kishin ƙasa da suka nuna wajen ceto matasan 20 da ke shirin shiga NYSC ba tare da wata illa ba.

Haka kuma, fadar Olubadan, basaraken Ibadan a Jihar Oyo, inda matasan suka fito, ta tabbatar da sakin su a cikin wata sanarwa.

Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Oktoba yayin bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kan Najeriya, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan bas-bas guda biyu da ke ɗauke da sabbin waɗanda suka kammala karatu suna kan hanyarsu ta zuwa yi wa ƙasa hidima. Maharan sun yi awon gaba da da dama daga cikinsu zuwa cikin daji.

Lamarin ya faru ne a yankin Umunoha da ke kusa da birnin Owerri, babban birnin Jihar Imo. Bayan sa'o'i kaɗan da harin, 'yan sanda sun ce sun ceto mutum 10 daga cikin waɗanda aka sace.

Daga bisani, kwamishinan 'yan sanda na jihar, Audu Bosso, ya ce jami'ansa sun gano inda masu garkuwa da mutanen suke tare da waɗanda suka sace, amma sun kasa shiga yankin saboda masu laifin sun kewaye wurin da abubuwan fashewa.

Ya ce rundunar tana sake tsara dabaru tare da shirin amfani da manyan injinan tono hanya da manyan motoci domin shiga yankin da ceto sauran mutanen.

Daga baya rahotanni suka fara yawo a kafafen yaɗa labarai na cikin gida cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan waɗanda aka sace tare da neman naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum.

Bayan sanarwar ceto da 'yan sanda suka fitar a ranar Laraba, wasu 'yan Najeriya da suka mayar da martani a shafin rundunar na X sun bayyana shakku kan ko da gaske 'yan sanda ne suka ceto mutanen.

Wani mai suna Emmanuel ya rubuta:

"Kun ce kun ceto su duka ba tare da kama masu laifin ba? Kai!"

Shi kuma wani mai amfani da X mai suna @Skynet_006 ya ce:

"Ba a kashe ko ɗaya daga cikin masu garkuwar ba, ba a kama kowa ba, amma kun ce kun ceto mutum 20 daga hannun masu makamai. Yadda kuke tunanin muna da wauta gaskiya abin mamaki ne."

Wannan rukuni na matasa na cikin shirin na NYSC, wanda shiri ne na tilas na hidimar ƙasa na shekara guda ga yawancin waɗanda suka kammala jami'a a Najeriya, inda ake tura su sassa daban-daban na ƙasar domin yin hidimar.

Matasan na tafiya ne cikin bas-bas guda biyu daga Ibadan da ke Jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya zuwa sansanonin horaswar NYSC a Jihar Abia da Jihar Akwa Ibom, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai musu hari a kan babbar hanya.

Lamarin ya sake tayar da hankalin jama'a game da matsalar rashin tsaro da sace-sacen mutane a kan tituna a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Satar mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaro a Najeriya, inda ƙungiyoyin masu laifi da masu ɗauke da makamai ke shiga harkar. Har zuwa yanzu, hukumomi ba su bayyana ko su waye maharan ba.

Gwamnati ta haramta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane a wani yunƙuri na rage musu ƙwarin gwiwa da ribar aikata irin waɗannan laifuka. Sai dai duk da hakan, matakin bai yi tasirin da ake fata ba wajen dakile matsalar.