Rumbun adana ƙwaƙwalen mutane mafi girma a duniya

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Rumbun adana ƙwaƙwalen mutane mafi girma a duniya
An wallafa

Wannan cibiya ce da ke ƙunshe da ƙwaƙwalwar mutane kimanin dubu goma, wadda aka kafa ta tun shekarar 1945.

Kimanin ƙwaƙwale 10,000 ne aka tattaro daga 1945 zuwa farko-farkon shekarun 1980.

Jami'ar South Denmark ta tattaro ƙwaƙwale 9,479, waɗanda aka ciro daga gawarwakin mutane masu taɓin hankali.

Muhimmin abin da suka yi a wancan lokacin shi ne, da zarar an kammala bincike a kan gawa sai su adana ƙwaƙwalwar tare da ajiye abin da suka yi bincike a kai.