Abin da muka sani kan harin jirgin sojin Najeriya a Neja

Asalin hoton, Nigerian Airforce
Bayanai daga jihar Neja da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya na nuna cewa wani jirgin sojin saman Najeriya ya yi luguden wuta kan al'ummar garin Guradnayi da ke kusa da Kusasu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.
Rahotanni sun ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 13 da suka haɗa da mata da ƙananan yara.
Bayanai dai sun nuna cewa garin na Guradnayi maɓoyar ƴan ta'adda ne.
To sai dai kuma hedikwatar tsaron Najeriya, a wata sanarwa da ta fitar, ta musanta kai wa fararen hula hari, inda ta ce ta kai wa ƴan ta'adda hari ne.
Me ya faru?
BBC ta tattauna da wasu mazauna garin da al'amarin ya faru waɗanda kuma suka shaida mana cewa al'amarin ya fara faruwa ne tun ranar Asabar da maraice amma kuma jirgin ya saki bam ɗin ne ranar Lahadi.
"Ƴanbindiga sun kwana suna wucewa shi ne mutanen garinmu na Guradnayi suka gudu suka ɓuya a wani wuri a garin Kusasu saboda tsoron harin ƴanbindiga. To da safe kuma suna kwance a ɓoye sai kawai suka ji bam daga sama. Kuma yawancin waɗanda suke a kwancen yara ne. Suna barci kafin ma su tashi. Wasu ma na fitsari," in ji wani mazaunin garin Guradnayi.
Ya kuma ƙara da cewa mutum 13 ne harin ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
"Kamar da misalin ƙarfe 5 zuwa 6 na safe ne jirgin ya jefo bam ɗin. Kuma kamar mutum 13 ne suka mutu. Waɗanda suka ji ciwo kuma su shida ne," in ji mazaunin garin na Guradnayi.
Martanin sojoji
Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe farar hula a wasu jerin hare-hare da aka kai ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.
A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce ta kai hare-hare ta sama kan wuraren ƴanbindiga da ke sassan jihar.
Kakakin rundunar, Manjo Janar Micheal Onoja ya ce an kai hare-haren ne kan ƙauyukan Katema da Bokko da Kusasu da Kuduru kuma an kai samamen ne bayan bayanan sirri da aka samar.
Ya kuma yi watsi da rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka yaɗa cewa hare-haren sun shafi farar hula.
Janar Onoja ya ce saɓanin rahotannin da aka yaɗa, hare-haren sun shafi yankunan ƴanbindiga ne kawai inda kuma aka kashe mayaƙa 70 a Kusasu kaɗai.
Yadda ƴan ta'adda matsa wa al'ummar Kusassu
Kamar yadda hedkwatar tsaron ta sojojin Najeriya ta ce garin na Kusasu matattara ce ta ƴan ta'adda, shi ma mazaunin garin ya tabbatar da hakan.
"Mutane na zama ne kawai saboda su ƴan ta'adda suna wucewa su yi ƙwace ko su sace mutane sannan wani lokaci kuma suna wucewa su tafi wani gari. Babu irin barazanar da ba sa yi wa mutanenmu. Kawai dai ana zama ne domin a yi noma a samu a ci abinci," in ji wanda ɗan uwansa ya samu rauni.
Ya kuma ƙara da yin kira ga hukumomi da su samar wa da garin nasu tsaro domin kawar musu da ƴan ta'adda abin da zai ba su damar zaman lafiya da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
"Da muna zuwa kasuwa ba tare da matsala ba amma yanzu duk su ƴan bindigar sun rufe hanya. Idan mutum zai yi tafiya sai dai ya yi ta addu'ar Allah ya sauke shi lafiya."
Hare-haren 'kuskure' na sojojin Najeriya
Idan dai ta tabbata cewa jirgin sojin Najeriyar ya kai harin kan fararen hula bisa kuskure, to wannan zai zama karo na 14 da jiragen yaƙin sojin Najeriyar ke kai wa fararen hula hari bisa kuskure a ƙoƙarinsu na bibiyar ƴan ta'adda.
Ko da a baya-bayan nan sai da aka samu irin wannan taƙaddama tsakanin al'ummar gari da suka yi zargin sojojin sun kai musu hari a kasuwar Jalli da ke jihar Borno, da sojoji da suka musanta.









