Yadda Anthony Joshua ya doke Prenga a Saudiyya

    • Marubuci, Charlotte Coates
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Dan damben Birtaniya kuma dan asalin Najeriya Anthony Joshua ya sake dabbaka sunansa a fagen damben duniya a karawar da ya yi a daren ranar Asabar mai cike da takaddama da kuma sosa zuciya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake tunkarar wani mashahurin karon-batta da ake sa ran za a yi tsakanin Joshua da Tyson Fury nan gaba a wannan shekara.

Yanzu Joshua, mai shekara 36 ya kara wani kambi a cikin tarihinsa na damben boksin 30-4, sai dai ya kusa shan mamaki mafi girma a tarihin sana’ar tasa lokacin da abokin karawarsa Kristian Prenga dan kasar Albania ya kai shi kasa har sau biyu a zagaye na farko.

Sai dai Joshua ya dawo da karfinsa a zagaye na biyu, inda ya rika saukar wa Prenga munanan naushi naushi yana kai shi kasa, lamarin da ya ba shi nasara a karawar da aka yi a birnin Jiddah na kasar Saudiyya.

Sashen wasannin motsa jiki na BBC ya zabo muku wasu kayatattun hotunan damben da aka gwabza a a daren, wanda aka yi wata bakwai bayan hatsarin mota da Joshua ya yi a Najeriya, lamarin da ya kashe aminansa biyu da ke tare da shi.