Arsenal na zawarcin Rodrygo, Shaw zai iya barin Man United

Rodrygo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na sa ido kan yadda Rodrygo ɗan wasan gefe na Real Madrid mai shekara 25, ke murmurewa daga raunin da ya ke fama da shi, inda a baya ta nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan na Brazil a bazarar da ta gabata. (Teamtalk)

Luke Shaw na iya barin Manchester United a bazara mai zuwa, yayin da alamu ke nuna cewa babu wani batun sabunta kwantiragi tsakanin ƙungiyar da ɗan wasan bayan na Ingila mai shekaru 31 a halin yanzu.

Ƙungiyar Luton Town ta gasar League One ta tuntuɓi Arsenal a lokuta da dama game da ƙulla yarjejeniyar aro kan ɗan wasan gaba ɗan ƙasar Ingila mai shekara 16, Max Dowman. (Talksport)

Ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Jamus mai shekara 17, Noah Ajayi, na gab da sanya hannu kan kwantiraginsa na farko a matsayin ƙwararre tare da ƙungiyar Manchester United. (Sky Sports)

Liverpool na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Monaco da Senegal, Lamine Camara mai shekara 22, a watan Janairu, bayan da ya rasa damar komawa Chelsea a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar ƴan wasa. (Football Insider)

Tottenham ce ƙungiya ta baya-bayan nan da ake alaƙantawa da ɗan wasan gaba na Argentina, Mauro Icardi; ɗan wasan mai shekara 33 yana nan a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa bayan ya bar Galatasaray a watan Yuli. (Calciomercato)

Ɗan wasan gaba na Ingila, Vincent Joseph, ya tabbatar da barin ƙungiyar Liverpool, inda ake sa ran ɗan wasan mai shekaru 16 zai koma Arsenal. (Standard)

Ƙungiyar Leeds United ba za ta yi gaggawar mayar da yarjejeniyar aro ta ɗan wasan gaban Eintracht Frankfurt, Jean-Matteo Bahoya, zuwa ta dindindin ba. Suna da damar sayen ɗan wasan na Faransa mai shekara 21 kan kudi £19.7m. (Football Insider)

Ana sa ran tsohon ɗan wasan gaban Manchester United da tawagar Faransa, Anthony Martial, mai shekara 30, zai koma ƙungiyar Malaga ta gasar La Liga a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa. (Footmercato)

Ƙungiyoyin Arsenal da Brighton, da Aston Villa duk suna sa ido kan ɗan wasan tsakiya dan ƙasar Austria mai shekaru 17, Luca Weinhandl, wanda za a iya samunsa daga ƙungiyar Sturm Graz kan kuɗi kimanin fam miliyan 17. (CaughtOffside)