Nawa ne albashin sojojin Najeriya idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Afrika?

    • Marubuci, Chukwunaeme Obiejesi
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa mai ritaya, ya yi wasu kalamai da suka haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar bayan da ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙara mafi ƙarancin albashin sojojin ƙasar zuwa naira 100,000 a wata..

Janar Musa, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ranar Laraba, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakan inganta walwalar sojoji.

"Da can sojoji suna karɓar naira 49,000 a wata ne. Mun yi ƙoƙari sosai, yanzu suna karɓar naira 100,000," in ji shi.

Sai dai bayan kalaman nasa, ƴan Najeriya da dama sun yi ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu suka ce sam albashin bai dace da irin haɗarin da sojoji ke fuskanta ba wajen yaƙi da ƴan bindiga da ƙungiyoyin ta'addanci.

Wani mai amfani da shafin X, @im_patrickekong, ya kwatanta albashin sojojin Najeriya da na Amurka, inda ya ce "sojan Amurka kan karɓi tsakanin dala 2,400 zuwa 4,200 a wata, yayin da sojan Najeriya ke karɓar kusan dala 93 kacal idan aka yi la'akari da canjin kuɗi na yanzu."

Shi ma wani Sunday Donatus, a Facebook, ya ce "ko masu aikin leburanci da gini na kan samu tsakanin naira 15,000 zuwa 20,000 a rana, kuma hakan zai iya ba su tsakanin naira 75,000 zuwa 100,000 cikin kwanaki biyar kawai".

A ranar Alhamis kuma, Shugaba Bola Tinubu ya gana da manyan hafsoshin rundunonin tsaro da shugabannin hukumomin leƙen asiri da masu ba shi shawara kan harkokin tsaro.

Sai dai ba a bayyana ko taron yana da alaƙa da muhawarar da ake yi kan albashin da walwalar sojoji ba.

Bambancin albashin sojojin Najeriya da wasu ƙasashen Afrika

A yanzu da gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an yi ƙarin albashi ga sojoji, za a iya cewa mafi ƙarancin abin da sojan Najeriya ke ɗauka shi ne naira 100,000 a wata.

Sai dai idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Afrika, musamman maƙwabta, sojojin Najeriya ne ke karɓar albashin da ya fi ƙaranci idan aka canza kuɗaɗen zuwa naira.

Duk da yake babu wasu bayanai a hukumance game da albashin jami'an soji na dukkan ƙasashen Afrika, domin ƙasashe da dama ba sa bayyana irin waɗannan bayanai a fili. Amma akwai wasu cibiyoyi masu tattara bayanan ƙididdiga da suka wallafa ƙiyasin albashin sojoji bisa bayanan da suka samu.

Wasu bayanai da cibiyar Statisense ta wallafa kan mafi ƙarancin albashin sojoji masu muƙamin kurtu (wato sabon soja da ya fara aiki), sun nuna yadda bambancin yake.

Najeriya: ₦104,000 ($64)

Ghana: Cedis 1,000 zuwa1,500 (₦157,000 – ₦235,000)

Afirka ta Kudu: Rand 8,000 zuwa R12,000 (₦704,000 – ₦1.06m)

Benin: 233,531 (₦560,474)

Kenya: KSh 18,700 (₦199,155)

Nijar: 75,000 (₦180,000)

Kamaru: 60,000 (₦144,000)

Chadi: 60,000 (₦144,000)

Statisense ta kuma ce jami'in soja mai muƙamin Manjo Janar a Najeriya na karɓar fiye da naira miliyan 1.15 a wata, yayin da takwaransa mai irin wannan muƙami a Afirka ta Kudu ke karɓar kusan Rand 120,000, wanda ya kai kusan naira miliyan 10.

Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sashihancin alƙaluman ba.

Najeriya da Afirka ta Kudu na daga cikin manyan ƙasashe biyar mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Alƙawarin da Tinubu ya yi jami'an sojin Najeriya

A ranar 7 ga Maris, 2026, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da amincewa da ƙarin albashin jami'an rundunonin sojin Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani taron buɗa-bakin azumin watan Ramadan da ya yi da manyan hafsoshin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa.

"Ya zama wajibi in gode muku a madadin ƴan Najeriya, domin mun san sau da dama kuna barin iyalanku, wasu kuma suna fuskantar hare-haren ƴan bindiga da ƴan ta'adda."

"Wannan ƙasa za ta ci gaba da gode muku game da sadaukarwar da kuke yi, kuma ba za ta tafi a banza ba. Ina tabbatar muku cewa za mu yi duk mai yiwuwa domin ganin ba ku yi nadamar hidimar da kuke yi."

"Jin daɗinku, samar muku da matsuguni da kuma wasu damarmaki ga iyalanku za su kasance cikin abubuwan da gwamnatinmu za ta bai wa fifiko," in ji shugaban.

Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun ce har yanzu ba a aiwatar da wasu daga cikin alƙawuran da shugaban ya yi ba.

A watan Afrilun bana, wani tsohon soja mai suna Sojaboy a shafukan sada zumunta ya ce a lokacin da ya bar aiki, albashinsa na ƙarshe bai wuce tsakanin naira 109,000 zuwa 111,000 a wata ba.

Ya ce an ƙara albashin ne a watan Fabrairun 2025.

"Kafin lokacin muna karɓar naira 51,000 ne, sannan akwai alawus na naira 20,000, wanda suka kama naira 71,000," in ji shi.

Sojaboy ya kuma yi iƙirarin cewa baya ga albashi, babu wasu kuɗaɗen shiga da sojoji ke samu, inda ya ca rayuwar soja na cike da ƙalubale.