Yadda aka sace ɗalibai a jihohin Borno da Oyo a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
'Yan bindigan sun sace ɗaliban da zuwa yanzu ba a tantance yawansu ba a wasu makarantu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da kuma jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar.
A jihar Borno, bayanai sun ce gomman ɗalibai sun ɓata a wasu makarantu da ke cikin haraba guda, bayan wani hari da 'yan Boko Haram suka kai garin Mussa na ƙaramar hukumar Askira Uba wayewar garin ranar ta Juma'a.
Daya daga cikin mahaifan daliban da bayanai suka ce an sace ya yi wa BBC bayani ta waya, kan halin da suke ciki bayan lamarin ya faru, daga garin na Mussa wanda ke da nisan kimanin kilomita 40 daga hedikwatar ƙaramar hukumar ta Askira Uba.
To amma rundunar 'yansandan Najeriya a jihar ta Borno ba ta iya tabbatar da cewa ko sace dabilban aka yi ba ko kuma sun razana ne suka shiga daji a lokacin da maharam suka durfafi garin.
Wani mazaunin garin da ya buya a kan dutse a lokacin ya sheda wa BBC yadda ya ce ya hangi lokacin da maharan ke sace daliban, a kan babura: ''Sun sace yaran ne fa a kan babur sai sojojin nan suka bi inda muka tabbatar da lamarin shi ne ga takalman yaran a zuzzube a kan hanya shi ne muka zo muka bincika.''
Ya kara da cewa shi kansa akwai 'yarsa a cikin wadanda aka sace, '' yaran nan, ni mai magana ma akwai 'yata a ciki mai shekara shida tana makarantar furamaer ne aji daya. Sai kuma ta yayana ita kuma tana nazare ne mai shekara uku. Gaba daya da muka yi lissafi su 43 aka sace.''
''Huɗu daga cikinsu sun ki shekara 15 sauran daga mai shekara uku ne zuwa shida,'' in ji shi.
Sai dai hukumomin jihar Borno ba su ce komai ba har zuwa lokacin da BBC ta tattara wadannan bayanai.
Mahaifin da ya yi bayani ya ce, ya ce har zuwa marece ba su ji komai ba daga hukumomin jihar ba sai dai sojojin da suka bi maharan kawai.
''A kauyen nan namu bayan sojoji ba wasu hukumomi da suke mulki, sai soja da kuma 'yan bijilanti, wadanda suke zama suna taimakawa.''
A jihar Oyo ma wasu 'yan bindiga sun sace wasu daliban bayan sun hallaka wani malami
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumomi a jihar ta Oyo sun tabbatar cewa gungun wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu makarantu guda biyu a garin Ahoro-Esinle da safiyar Juma'a inda suka hallaka wani malami kuma suka sace ɗalibai.
Hukumar kula da harkokin kananan makarantu sun bayar da umarnin rufe makarantun da ke kusa da garuruwan da aka sace nasu daliban, har sai abin da hali ya yi.
Hukumar ta ce an yi hakan ne a matsayi wani mataki na wucin-gadi, domin gudun a sake sace wasu, domin tabbatar da kwanciyar hankali.
A sanarwar da suka fitar, sun bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali ga jihar ta Oyo, inda suka bayyana cewa sun damu matuka tare da tausayawa ga iyayen yaran da al'ummomin gaba daya.
Sun ce ba su san ainahin yawan daliban da abin ya shafa ba, yayin da jami'an tsaro suka bazama yankin don tabbatar da ainahin abin da ya faru da kuma yadda za a ceto daliban da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga al'ummomin da abin ya shafa.
Hukumomi sun tabbatar wa da iyaye cewa ba za su sarara ba har sai sun tabbatar da dawo da dukkanin yaran da aka sace
Sun ce suna ci gaba da magana da hukumomin tsaro tare da sanar da halin da ake ciki.
Rahotanni sun ce an bayar da sanarwar rufe makarantun yankin bayan kai harin. Amma kuma daga biani hukumomin jihar sun bayar da umarnin a ci gaba da karatu a makarantun ranar Litinin, bayan da aka kai karin jami'an tsaro yankin.
Lamarin hare-haren 'yan bindiga da atar mutane don nemna kudin fansa sun fi kamari ne a yankin arewacin Najeriya, inda ba kasafai aka saba ganin hakan ba a kudancin kasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.
A baya-bayan nan ita ma dai jihar ta Oyo na fuskantar matsalar tsaron daga gungun masu aikata laifi.










