Manchester United na son ɗaukar Valverde, PSG na harin Alvarez

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na duba yiwuwar zawarcin ɗan wasan tsakiyar Real Madrid ɗan ƙasar Uruguay Federico Valverde, mai shekara 27. (Star)

Paris St-Germain ta sanya ɗan wasan gaban Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, a cikin jerin sunayen ƴan wasan da za ta yi zawarci a bazara mai zuwa. (ESPN)

Manchester United ta ƙara ƙaimi wurin zawarcin ɗan wasan Atalanta dan ƙasar Brazil Ederson, mai shekara 26, da kuma dan wasan tsakiyar West Ham da Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21. (Sky Sports)

Ben White na iya watsi da tayin Everton a bazara idan ɗan wasan , mai shekara 28, ya samu tabbacin ci gaba da taka leda a Arsenal. (Football Insider)

Real Madrid ba ta da tabbacin ko za ta fara batun sayen ɗan wasan bayan Como da Sifaniya Jacobo Ramon a bazara, don haka Chelsea za ta iya samun damar sayen ɗan wasan mai shekara 21. (Sun)

Ɗan wasan Belgium Youri Tielemans, mai shekara 29, zai iya barin Aston Villa a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Football Insider)

Ɗan wasan gaba na Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 29, zai iya ci gaba da zama a West Ham ko da kuwa ƙungiyar ta faɗo daga gasar Premier. (Teamtalk)

Porto na da sha'awar ɗaukar Robert Lewandowski a kan cinikin kyauta a wannan bazarar amma har yanzu akwai yiwuwar ɗan wasan na Poland mai shekara 37 zai iya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Barcelona. (Florian Plettenberg)

Duk da cewa ya taimaka wa Nottingham Forest wurin guje wa faɗawa gasar Championship, akwai yiwuwar ƙungiyar za ta iya sallamar koci Vitor Pereira ta kuma maye gurbinsa da kocin Fulham Marco Silva a bazara. (Teamtalk)

Kocin Bournemouth Andoni Iraola ya fice daga cikin masu takarar karɓar ragamar Manchester United yayin da a ke daf da naɗa Michael Carrick a matsayin koci na din-din-din a Old Trafford, wanda hakan ya sa Iraola ya samu damar tattauna guraben aiki a Crystal Palace da Chelsea.(Mail)

Chelsea ta fara tattaunawa da tsohon kocin Real Madrid Xabi Alonso, kuma ta tuntuɓi Andoni Iraola da Marco Silva. (Times)