Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace ce Sadiya Farouq, ministar Buhari da EFCC ke nema ruwa a jallo?
A ƙarshen makon nan ne hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohuwar ministar jinƙai ta Najeriya, lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na internet, ta ce tana neman tsohuwar ministar ne bisa zarge-zarge masu alaƙa da almundahanar kuɗaɗe.
Sanarwar EFCC ta buƙaci jama'a su sanar da hukumar duk inda suka ga tsohuwar ministar domin kama ta.
Ba wannan ne karon farko da hukumomin yaƙi da cin hanci na Najeriya suka zargi tsohuwar ministar da hannu a almundahanar kuɗi ba.
A watan Janairun 2024 hukumar ta gayyaci tsohuwar ministar zuwa ofishinta domin amsa wasu tambayoyi kan zargin ɓacewar naira biliyan 37 lokacin da take jagorantar ma'aikatar.
Laifukan da EFCC ke zargin Sadiya da aikatawa
Cikin sanarwar da hukumar EFCC ta fitar a shafinta na Intanet a ƙarshen mako ta lissafo wasu laufuka uku da take zargin tsohuwar ministar jinƙan da aikatawa kamar haka:
- Haɗa baki domin aikata laifuka
- Amfani da ofishi ba bisa ƙa'ida (lokacin tana minista)
- Karkatar da kuɗaɗen gwamnati
Hukumar ta EFCC ba ta yi ƙarin haske ba game da waɗannan laifuka da ta zayyano, sai dai ta buƙaci ƴan ƙasar su sanar da ita, duk inda suka ga tsohuwar ministar.
Wace Sadiya Umar Farouq?
Sadiya Umar Farouq ta kasance ƴar siyasa da ta jima a tafiyar siyasar tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammad Buhari.
A watan Agustan 2019, marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa ta minista a sabuwar ma'aikatar jinƙai da yaƙi da bala'o'i ta ƙasar, muƙamin da ta riƙe tsawon shekara takwas.
Ta ƙasance minista mafi ƙanƙantar shekaru a ƙunshin ministocin tsohuwar gwamnatin Buhari a lokacin da aka naɗa ta.
A lokacin da take minista ta riƙa janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen tallafi.
A watan Afrilun 2020, gwamnatin Buhari ta amince da bayar da tallafin kuɗi da abinci ga ƴan ƙasar, sakamakon annobar Korona da ta janyo kulle a faɗin ƙasar, wanda aka yi ƙarƙashin ofishinta, wani abu da ya riƙa janyo mata zargi daga ƴan ƙasar.
A watan Agustan 2020 ne ta yi wasu kalamai da suka ƙara janyo mata suka a cikin ƙasar, bayan da ta ce gwamnati ƙarƙashin ofishinta ta kashe naira miliyan 500 wajen ciyar da yara ƴan makaranta abinci a lokacin kullen.
A watan Satumban 2020 ne ta auri babban hafsan sojin saman ƙasar na lokacin mulkin Buhari, Air Marshal Sadiq Baba Abubakar, a wani biki da aka yi cikin sirri.
A ƙarshen watan Satumban 2020 ɗin ne kuma tsohon shugaban hukumar ICPC mai yaƙi da almundahar kuɗi, Farfesa Bolaji Owasanoye ya yi zargin cewa an karkatar da kuɗi har naira biliyan 2.67 da aka ware domin ciyar da 'yan makaranta a lokacin kullen korana, wanda kuma ofishinta ne ya jagoranci shirin.
Sauran ministocin Buhari da EFCC ke bincike
Ba Sadiya Farouq ba ce kawai ministar tsohuwar gwamnatin Buhari da hukumar EFCC ke tuhuma da aikata almundahar kuɗi ba.
Akwai aƙalla sauran tsoffin ministocin Buhari biyar da hukumar EFCC ke tuhuma da aikata ba daidai ba.
- Saleh Mamman
A makon da ya gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta samu tsohon ministan lantarki Saleh Mamman da laifuka 12 da suka shafi halasta kuɗaɗen haram, bayan da EFCC ta gurfanar da shi gabanta.
A cikin bayanin da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar (EFCC) ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta ce an samu tsohon ministan da laifin karkatar da kuɗin da suka kai kimanin naira biliyan 33.
- Abubakar Malami
Malami ne tsohon babban lauyan gwamnati, sannan ministan shari'a a zamanin Buhari, kuma EFCC na bincikensa kan zargin ɓatan wasu kuɗaɗe.
A cewar Malami, zargin nasa ya samo asali ne daga batun dala miliyan 346 da ƙasar Switzerland ta mayar wa gwamnatin Najeriya, wanda ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha ya sace.
Kotu dai ta sha ɗauri Malami kan wannan zargi kodayake ya sha musantawa.
- Timipre Sylva
Duk da cewa Buhari ne babban ministan ma'aikatar man fetur, Mista Sylva ne ke kula da ayyukan ma'aikatar na yau da kullum, wadda ita ce hanya mafi girma ta samun kuɗin shiga ga Najeriya.
A ranar 10 ga watan Nuwamban shekarar 2025 ne EFCC ta ayyana neman Silva ruwa a jallo bisa zargin almundahar kuɗi, fiye da dala miliyan 14 - kwatankwacin naira biliyan 21.
A cewar hukumar, wata babbar kotun jihar Legas ce ta bayar da umarnin kama shi ranar 6 ga watan Nuwamba.
- Hadi Sirika
A 2025 ne EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama na ƙasar, Hadi Sirika a kotu kan wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba a lokacin da yake minista.
Hukumar ta zarge shi da amfani da ofishinsa wajen yi wa 'yarsa Fatima da mijinta Jalal Hamma alfarmomi ta hanyar ba su aikin bayar da shawarwari a kamfanin Nigeria Air, da kuma ba su kwangilar gina wani ɓangare na filin jirgi a Katsina.
- Chris Ngige
A watan Disamban 2025 ne EFCC ta tsare da tsohon ministan ƙwadagon ƙasar, zamanin gwmanatin Buhari, Dr Chris Ngige.
Sai dai a lokacin, hukumar ba ta yi cikakken bayanin zargin da take yi wa tsohon ministan ba.
Zargin tsoffin ministoci: Laifi ko siyasa?
Galibi dai tsoffin ministocin Najeriya kan fuskanci tuhume-tuhume daga hukumomin yaƙi da rashawa na ƙasar bayan sun sauka daga muƙamansu.
Hukumomin dai kan dage cewa tsoffin ministocin sun aikata laifukan da ake zargin su da yi.
To amma wasu ƴanƙasar na alaƙanta batun da siyasa, inda suke zargin cewa gwamnati na amfani da hukumomin wajen musguna wa tsoffin ministocin wataƙila saboda jam'iyyunsu.
Masu wannan zargi na cewa hukumomin ba sa kama tsoffin ministocin da suke cikin jam'iyya mai mulki sai waɗanda suka fice ko suke yunƙurin ficewa.
To sai dai a lokuta da dama hukumomin sun sha musanta waɗannan zarge-zarge.