Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Litinin 11/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Tinubu ya isa Kenya don halartar taron ƙoli na Afirka da Faransa

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi.

    Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami'i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare.

    Akwai kuma Ministar harkokin waje ta Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Jakadan Kenya a Najeriya, Amb. Isaac Parashina.

    Taron zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Najeriya na zurfafa alaƙa da kuma haɗin kai da sauran ƙasashen Afirka da kuma Faransa.

  2. Shugabannin Afirka na halartar babban taron ciyar da nahiyar gaba a Kenya

    Shugabanni daga sassa daban daban na Afirka na hallara a Kenya domin halartar wani gagarumin taron ƙoli da Faransa haɗin gwiwa da gwamnatin Kenya ke karɓar baƙunci.

    Taron na ciyar da Afirka gaba mai taken Africa Forward zai samu halartar shugabannin ƙasashe kusan 30 daidai lokacin da Paris ke ƙoƙarin inganta alaƙarta da nahiyar bayan koma-bayan da ta fuskanta a yammacin Afirka.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Kenya Wiiliam Ruto ne ke karɓar baƙuncin taron na yini biyu da ya haɗa shugabannin Afirka da masu hannun jari da manyan ƴan kasuwa.

    Taron zai mayar da hankali kan kasuwanci da makamashi mara gurɓata muhalli da fasaha da tsaro.

    Sai dai ana kallon taron a matsayin wata alama ta sauyi a a yadda Faransa ke tafiyar da al'amuranta a Afirka.

    Shi ne babban taro irinsa na farko tsakanin Faransa da ƙasashen Afirka da za a gudanar a ƙasar da ake magana da harshen Turanci.

    Masu sharhi sun ce Faransa na ƙoƙarin sake dasa kanta a matsayi mai kyau a Afirka ta hanyar dogaro kan ƙawancen kasuwanci da zuba jari.

  3. Sojojin Najeriya sun musanta rahoton kisan farar hula a hare-haren Neja

    Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe farar hula a wasu jerin hare-hare da aka kai ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

    A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce ta kai hare-hare ta sama kan wuraren ƴanbindiga da ke sassan jihar.

    Kakakin rundunar, Manjo Janar Micheal Onoja ya ce an kai hare-haren ne kan ƙauyukan Katema da Bokko da Kusasu da Kuduru kuma an kai samamen ne bayan bayanan sirri da aka samar.

    Ya kuma yi watsi da rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka yaɗa cewa hare-haren sun shafi farar hula.

    Janar Onoja ya ce saɓanin rahotannin da ak yaɗa, hare-haren sun shafi yankunan ƴanbindiga ne kawai inda kuma aka kashe mayaƙa 70 a Kusasu kaɗai.

    An daɗe ana zargin rundunar sojin Najeriya da kashe farar hula a samamen da take kai wa kan ƙungiyoyin ƴanbindiga da mayaƙa masu iƙirarin Jihadi duk da cewa hukumomin sun sha faɗin cewa mutuwar farar hular abu ne da ba a yi niyya.

  4. Trump ya yi watsi da martanin Iran kan buƙatar kawo ƙarshen yaƙi

    Shugaba Donald Trump ya yi watsi da martanin shawarwari ko buƙatun da Iran ta gabatar a kan na Amurka, waɗanda za a shirya tattaunawar zaman lafiya a kansu.

    A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce, '' Ba na son su - kacokan abu ne da ba za a lamunta ba''.

    Rahotanni sun ce - a ɓangarenta, Iran ta nemi a ware batun yarjejeniyar kawo ƙarshen rikici a Mashigar Hormuz, daga sauran batutuwa da suka fi sarƙaƙiya, kamar shirin nukiliyarta.

    Wasu kafofi a Iran daga bayanan da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na Tasnim - da ya ɗan jiɓanci gwamnati, sun ce - martanin Trump ɗin ko alama bai ɗaɗa hukumomin Iran ɗin da ƙasa ba kuma Iran ɗin za ta gabatar da buƙatu ne domin ƴancin kanta - ba wai don ta daɗaɗa wa Trump ba.

  5. Barka da Safiya

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa na Kai Tsaye, barka da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Kamar kodayaushe, shafin zai kawo muku labaran da suka shafi yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran da abubuwan da suka shafi Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu rahotannin da ma kallon bidiyo.