Yadda rikici ya ɓullo a jam'iyyar ADC a jihar Kaduna

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyar ADC a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta fada cikin wani rikici bayan da aka ayyana sunan mutumin da ya zo na biyar a zaben fitar da gwani na gwamna a matsayin dantakarar da ya samu nasara a karkashin jam'iyyar.

Tun da farko dai sakataren kwamitin zaben ya ayyana sunan Isah Ashiru Kudan, a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na dantakarar gwamnan, amma daga baya shugaban kwamitin daukaka karar zaben fitar da gwanin da aka tura jihar ya ba da wata sabuwar sanarwa ta daban inda ya ayyana Shu'aibu Idris-Mikati, a matsayin wanda ya yi nasara.

Isah Ashiru Kudan, dai ya samu kuri'u 86, 113, sai kuma shi Shu'aibu Idris Mikati, wanda ya samu kuri'u 10, 819.

Tuni dai matakin sanar da Mikati a matsayin wanda ya yi nasara a zaben daga baya ya haifar da martani daga bangarori daban-daban, inda sakataren kwamitin zaben fitar da gwanin Mika'ilu Ibrahim Barau, ya ce ba da yawunsa aka yi hakan ba.

Ya ce," Muna zaune kawai muka ji an ce shugaban kwamitin daukaka karar zaben fitar da gwanin ya yi sanarwar inda ya canja dan takara.

''Gaskiya wannan ba shi ne aikin da aka samu ba, aikinmu shi ne mu saurari korafi sannan mu kai wa jam'iyya ita kuma ta yi abin da ya kamata."

" A matsayinsa na shugaban kwamitin mutum uku babu abin da zai gabatar ba tare da ya tuntubi sauran mambobin kwamitin ba musamman sakatare." In ji shi.

Ya ce, " Kodayake mun samu bayanan cewa an ba shi cin hanci ne aka ce ya je ya sanar ba abin da zai faru."

A nasa bangaren, Isah Ashiru Kudan, wanda aka fara ayyanawa a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwanin ya ce abin da shugaban kwamitin ya yi cike da yake da ban mamaki.

Ya ce," Mutumin da ya zo na biyar an ce ba ni ne na ci ba shi ya ci, to na san shalkwatar jam'iyyarmu ba za ta bar wannan abu ba."

Shi kuwa shugaban kwamitin daukaka karar zaben fitar da gwanin, Dakta Mustapha Fagge, ya ce yana da takardu da bidiyo da kuma shaidun mutane, kuma duk wani mataki da ya dauka yana da madogara.

Ya ce," Mu abin da muka dauka zuwa aka yi aka yi ta rubuta sakamakon zaben domin akwai inda ma ba a yi zaben ba aka ce an yi."

" Batun da suke cewa kudi na karba shi ya sa na yi wannan sanarwar, ni babu wanda ya ba ni ko sisi." In ji shi.

Tuni dai bangaren Shu'aibu Idris-Mikati,suka ce sun amince da wannan mataki.