Arsenal na zawarcin Varela, Crystal Palace na son ci gaba da riƙe Ismaila Sarr

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal da Napoli da Benfica, suna nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Monza, ɗan ƙasar Portugal mai suna Gustavo Varela, mai shekara 21, wanda ke kan ganiyarsa a halin yanzu. (Gazzetta dello Sport)

Crystal Palace ba ta da niyyar sayar da ɗan wasanta na gefe ɗan ƙasar Senegal, Ismaila Sarr, mai shekara 28, a watan Janairu, musamman bayan da ta gudanar da tattaunawa kan sabon kwangila da ɗan wasan. A baya, Sarr ya nuna sha'awar komawa Liverpool a bazarar da ta gabata. (Football Insider)

Ɗan wasan baya na Brighton, Luka Vuskovic, na ƙasar Croatia mai shekara 19, ya ci gaba da ɗaukar hankalin manyan ƙungiyoyin Turai, inda Liverpool da Real Madrid, da Barcelona suka shiga sahun masu zawarcin ɗan wasan. (Teamtalk)

Liverpool na matuƙar girmama ɗan wasan tsakiya na Borussia Dortmund, Felix Nmecha, ɗan ƙasar Jamus mai shekara 26, amma ba a ɗauke shi a matsayin babban ɗan wasan da ta son ɗauka a halin yanzu ba.(Florian Plettenberg)

Tsohon kocin Newcastle, Eddie Howe, na iya dagewa kan sai ya zai zo da dukkan tawagar mataimakansa idan har Manchester United ta tuntuɓe shi domin ya zama kocinta. (Express)

Manchester United za ta buƙaci biyan Newcastle diyya mai tsoka ta fam miliyan 6 domin ɗaukar Howe, bisa sharuɗɗan da ke tattare yarjejeniyarsa ta barin St James' Park. (Telegraph)

Mamallakin Bournemouth, Bill Foley, ya amince da bayar da tayin kwantiragi mai tsoka—wanda ya karya tarihin ƙungiyar—ga ɗan wasan tsakiya na Ingila mai shekara 23, Alex Scott. A halin yanzu dai Chelsea da Liverpool, da Arsenal da Tottenham duk suna sanya ido kan yadda lamarin zai kaya. (Teamtalk)

An sanar da Manchester United cewa za ta buƙaci kashe fiye da fam miliyan 70 domin ɗaukar ɗan wasan baya na Newcastle, Lewis Hall, mai shekara 22. (Football Insider)

Ajax na son ɗaukar ɗan wasan gaba na Wolves kuma ɗan asalin Najeriya, Tolu Arokodare, a matsayin ɗan wasanta na dindindin. A yanzu haka, ɗan wasan mai shekara 25 yana buga wasa ne a ƙungiyar ta gasar Eredivisie a matsayin aro. (Sport Witness)

Idan har Crystal Palace ta yanke shawarar korar kocinta ɗan kasar Faransa, Pierre Sage, to za ta nemi naɗa wani koci wanda a halin yanzu ba shi da aiki. (Football Insider)

Tsohon kocin Brentford da Tottenham, Thomas Frank, da kuma tsohon kocin Burnley da Everton da Nottingham Forest, Sean Dyche, na daga cikin waɗanda za a iya la'akari da su idan Crystal Palace ta yanke shawarar rabuwa da Sage. (The I)