Ko Mourinho zai iya gyara Real Madrid?

    • Marubuci, Guillem Balague
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport columnist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Abin da shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya yi a ranar Talata - bayan fiye da shekaru goma ba tare da taron manema labarai ba, wani sako ne cewa sai dai a tsige shi da karfin tsiya daga Bernabeu - kamar yadda yake kokarin nuna cewa shi mutum ne da ke zagaye da makiya na zahiri da kuma wadanda aka kirkira.

Sabon babi ne ake fatan budewa na kawo muhimmin canji a Real Madrid, saboda abin da ke cikin zuciyar dukkan mutanen da ke cikin zauren shi ne sanin cewa Jose Mourinho zai dawo kungiyar bayan shekara 13 da raba gari.

Ga kuma mummunan hasashen da mutane ke yi: Salon aikin Mourinho - na amfani da dabaru da yaɗa hasashe da jita-jita kan yadda kafafen yada labarai ke tsangwamar shi, wanda ya zo daidai da salon da Perez ya shafe shekaru yana amfani da shi.

Shugaban Real Madrid wanda ya yi kaurin suna wajen sukar alkalan wasa kuma wanda ya ke kokarin nuna yadda a cewar sa, kafafen yada labarai ke neman ganin bayan shi da kuma yadda yake ikirarin ana nuna goyon baya ga Barcelona a gasar La Liga, a yanzu ana iya cewa ya samu koci daidai da yadda yake so.

Abin da ya sa dawowar Mourinho za ta yi kyau

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jose Mourinho zai koma Real Madrid bayan shekara 13

Zargi da rashin yadda da ake da shi tsakanin shugabanni a Bernabeu, a yanzu zai koma bencin kungiyar tare da Mourinho - a yanzu haka ma Alvaro Arbeloa ya riga ya samar da irin wannan yanayi.

Wannan ne ya sanya komawar Mourinho ke da matukar muhimmanci, a tunanin Perez.

Kawunan dun dare a kungiyar Real Madrid. Ana ta samun rashin jituwa tsakanin ‘yan wasa.

Vinicius Jr ya cimma burinsa a lokacin da aka kori Xabi Alonso daga aikin horas da kungiyar.

An tsani Kylian Mbappe a kungiyar, ya zamo tamkar saniyar ware.

Sannan ga shi kungiyar ta kammala kakar wasa biyu a jere ba tare da lashe kofi ba.

A wannan yanayi ne wani sanannen mutum mai tsattauran ra’ayi, wanda ba ya daukar shirme zai kutso.

Wannan wata dabara ce daga shugaban kungiyar wanda ya gaza kwaba wa ‘yan wasansa, ai kuwa dole ya ga dawowar Mourinho ce mafi dacewa.

To amma bukata ba lallai ta zama cancanta ba. Kuma kafin Madrid ta fara murnar dawowar ‘Mutum na musamman’, yana da kyau a sake yin wata tambaya mai muhimmanci: shin zai sake tafka shirmen baya?

Raunin baya bai warke ba kuma kawunan magoya baya a rarrabe suke

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mourinho bai tabuka wani abin a zo a gani ba a baya-bayan nan. Bai lashe kofi ba a cikin shekara 11 da suka gabata. Sau shida ana korar shi daga aiki a baya-bayan nan.

Wani rahoto na musamman na Amazon mai taken ‘Da babu dadi gara babu baki daya’, ya kunshi bayanai masu muhimmanci.

An bayyana yadda ake cin kwakwa wajen atsiaye, ana ajiye ‘yan wasa barkatai, sannan idan aka je hutun rabin lokaci daga fada sai tsawa.

Bayan jerin rashin nasara sai ya dora wa ‘yanwasa laifi. A karshe sai da kawunan ‘yanwasa ya dare zuwa gida uku: akwai kalilan masu yi masa biyayya, sai mafi yawa wadanda ke adawa da shi, sai kuma wasu gungun ‘yan ko-oho.

Bai lashe komai ba, sannan bai bar kungiyar ba sai da ya kammala dagula lamurra.

Babban makasudin rashin nasararsa ba batun rashin dabarar wasa ba ne. Matsala ce ta rashin fahimtar dabi’ar kungiyar.

Babban nakasun Mourinho shi ne tunaninsa cewar kwarjininsa da halayyarsa ta tilastawa sun fi muhimmanci a kan tsarin da kungiya ta gina na tsawon gomman shekaru.

A lokacin da yake horas da Tottenham, abin ya kai ga cewa komai ya tarwatse.

A lokacin da yake horas da Manchester United za a iya cewa tabbas ya gano inda cutar take, amma sai ya yi kuskuren amfani da maganin wata cutar ta daban.

Real Madrid ba Tottenham ba ce, kuma ba Manchester United ko Chelsea ba, haka nan ba Roma ba ce. Kungiya ce da ke da tsarinta na asali, da aniye kowa a matsayinsa da kuma nuna isa, kuma tana da nata tunanin na daban game da abin da take kallo a matsayin samun masara.

Lokacin da Mourinho yake a kungiyar, tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013, ya bar kungiyar a matsayin wadda dangantaka a cikinta ya yi mummunan tsami, inda shi kansa a watan Janairun wannan shekara ya bayyana lamarin a matsayin “kusan tashin hankali”.

Har yanzu raunin da ya bari a kungiyar bai warke ba, inda a lokacin ya lashe La Liga daya da Copa del Rey daya. Kawunan magoya baya a rabe suke.

To amma Perez, wanda shi ne jagora ya riga ya ce musu: muna da makiya kuma zan yake su. Mourinho ja mu je.

Rikici, rarrabuwar kai da labaran kanzon kurege

Jose Mourinho tare da shugaban Real Madrid Florentino Perez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jose Mourinho tare da shugaban Real Madrid Florentino Perez

To amma mene ne zai sa dawowarsa ta yi kyau?

Bangarorin da suka kamata Mourinho ya inganta ba a boye suke ba.

Ya kamata ya fahimci cewa nasara ba ta mutum daya ne ba, kuma ba aba ce da ake tursasa wa mutane ba.

Idan aka duba zaman da ya yi a kungiyar Tottenham da Manchester United akwai waau abubuwa karara wadanda ya kamata ya watsar: kin tafiya da kowa a kungiyar, watsi da shawarwarin mutanen da ke kusa da shi, yabon kansa shi kadai idan aka samu nasara sannan da kokarin ture laifi daga kansa idan aka ci karo da rashin nasara.

Akwai kuma wani lamarin da bai tunzura mutane yadda ya kamata ba a Spain, wanda in da mutane sun mayar da hankali a kansa da ya zama babban abin cece ku ce.

Lokacin da Mourinho ya mayar da martani kan zargin cin zarafin wariyar launin fata da dan wasan Benfica Gianluca Prestianni ya yi wa Vinicius, in da Mourinho ya mayar da martani da cewa bai kamata a zargi kungiyar da ke tutiya da fitaccen danwasanta a tarihi bakar fata ne - Eusebio - da laifin nuna wariyar launin fata ba.

Abin ya so ya tayar da kura, amma sai kuma ya lafa. Har yanzu da wuya ka ji ana maganar duk da batun da ake yi na shirin komawar Mourinho Madrid, wanda hakan ke nuna halin dimuwa da ake ciki a kungiyar inda ake neman mafita ido rufe.

A Real, inda yanzu haka ake zaman ‘yan marina tsakanin Vinicius da Mbappe, sannan aka bar ‘yanwasa na yin abinda suka ga dama tsawon shekara biyu, duk wani abu da zai ta’azzara alakar da ke tsakaninsu zai iya zamewa bala’i ga kungiyar.

Akwai bukatar mayar da hankali kan tsamin dangantakar Vini da Mbappe. Masu horaswa uku - Carlo Ancelotti, Xabi Alonso da kuma Arbeola - sun gaza hada su domin su samar da sakamakon da ake so.

Haduwar wadannan ‘yanwasa biyu ya kamata ya mayar da Real kungiyar da aka fi tsoro a Turai, amma abin ya gagara.

A tarihin Mourinho, akwai kila-wa-kala kan kwarewarsa wajen hada ‘yanwasa biyu wadanda ba su cika jituwa ba, amma dai bari mu kyautata zato.

Ya mayar da Samuel Eto’o dan wasan gefen dama a Inter Milan kuma suka samu nasarar lashe kofi uku.

Ya yi kokari wajen amfani da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema a Madrid, kuma akalla sun bayar da sakamako mai kyau a tare.

Zai iya sake kwatanta irin haka. To amma fa sai idan zai yi jagoranci ta hanyar rungumar kowa da kuma sanin yadda zai sarrafa ‘yanwasa ba ta hanyar kama-karya kawai ba.

Ya riga ya bayyana bukatunsa. Yana son a rika sauraron bukatunsa wajen sayen ‘yanwasa - ba lallai takamaiman ‘yanwasa da yake so ba, amma zai iya fadin gurbin da yake so a samo.

Ya bayyana wuraren da yake ganin ana da rauni a kungiyar.

A lokacin baya da ya jagoranci Real ya bukaci ‘yanwasa irin su Luka Modric, Sami Khedira da Mesut Ozil, kuma an ga irin rawar da suka taka.

Yana kuma son mutanensa a kusa da shi, yana so a nada mutanensa a muhimman mukamai. Kungiyar kuma tana son ci gaba da aiki da masu kula da lafiyar da suke aiki da su a yanzu da kuma bangaren motsa jiki.

Amincewar Mourinho ya bi wannan tsari - wato masu horaswa mutanensa, likitoci na shugabanni - ya danganta da irin sauyin da aka samu a irin ra’ayin da aka san shi da shi.

Wani babban lamari kuma shi ne jan aikin da zai iske.

Kakar wasa biyu babu kofi da tawaga maras mayar da hankali a filin wasa, wadanda suka kammala cikin ’yan kasan na goman farko a teburin gasar Champions League - har sau biyu.

A tattaunawar da Perez ya yi da manema labarai ranar Talata bai yi magana kan ko daya daga cikin wadannan ba.

Ya yi magana ne kan kafofin yada labarai, da labaran kanzon kurege game da masu yi masa bakin ciki. A baya ba ya magana irin haka a bainar jama’a.

Tamkar dai Mourinho ne ke masa kidi shi kuma yana tika rawa. Bai yi magana ba a kan harkar kwallo.

Amma shi Mourinho yana bukatar ya yi magana a kan kwallo, ya warware matsalar da ta shafe ta, ta hanyar samun yardar wadanda zai horas. Ta hanyar martaba al’adar kungiyar a maimakon rusa ta. Ta hanyar sanin cewa kungiyar da zai je ta fi karfin wani mutum daya tilo.