Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Iran ta so ta kashe ɗaya daga cikin ƴaƴana – Netanyahu
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Iran ta yi yunƙurin kashe ɗaya daga cikin ƴaƴansa maza, sai dai bai bayyana lokacin da abin ya faru ba.
Haka nan Netanyahu bai faɗi wanne daga cikin ƴaƴan nasa ne aka yi yunƙurin kashewar ko kuma yadda abin ya faru ba.
Wannan bayani na Netanyahu ya nuna yadda ake ci gaba da zaman ɗarɗar tun bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Amurka a watan Fabarairu, wanda ya yi sanadin kisan jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei da wasu shugabannin ƙasar ta Iran.
Firaiministan na Isra'ila wanda ƙawancen jam'iyyarsa ke fama da rashin farin jini, wata biyu gabanin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar a ranar 27 ga watan Oktoba ya yi wannan zargi ne a wata tattaunawa ta waya da gidan talabijin na Isra'ila Channel 14.
Yana mayar da martani ne kan rahotannin da ke cewa jami'an tsaron ƙasar sun ƙi bayar da kariya ga wani ɗan siyasa na adawa a ƙasar.
"Na san cewa akwai ban mamaki, game da yarana, amma haka ne. Iran ta farmaki ɗaya daga cikin ƴaƴana. Iran ta so ta kashe ɗaya daga cikin ƴaƴana," kamar yadda Netanyahu ya shaida wa gidan talabijin ɗin mai goyon bayan gwamnati.
"Saboda haka yanayin tsaron na cikin damuwa," in ji shi, ba tare da yin ƙarin haske kan yadda lamarin ya faru ba.
Babu tabbas kan ko wanne daga cikin ƴaƴan nasa yake magana a kai. Babban ɗansa Yair Netanyahu na rayuwa ne a birnin Miami na Amurka.
Ofishin jakadancin Amurka a birnin New York bai mayar da martani kan buƙatar yin ƙarin haske game da zarge-zargen ba.
Netanyahu ya kuma ce ya faɗa wa shugaban hukumar tsaro ta Shin Bet, David Zini cewa ya kamata a samar da isasshen tsaro ga duk wanda ke takarar muƙamin Firaiminista.
A baya kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito cewa Zini ya ƙi samar da tsaro ga Gadi Eisenkot, tare da shaida wa hukumar zaɓe ta ƙasar cewa babu wata barazanar tsaro a kansa.
An yi hasashen cewa jam'iyyar Eisenkot ce za ta lashe mafi rinjaye na kujerun majalisa a zaɓen da za a gudanar duk da cewa yawanci ana haɗa gwamnati a Isra'ila ne ta hanyar haɗaka a maimakon samun jam'iyya ɗaya tilo da za ta yi rinjaye.
Amurka ta sanar da jerin takunkumai a kan Iran kuma ta yi barazanar ɗaukar mataki kan ƙasashen da suka taimaka wa Iran ɗin.
Sakataren harkokin kuɗi na Amurka Scott Bessent ya bayyana matakin a matsayin "mafi munin harin tattalin arziƙi a tarihi."
Bessent wanda ya bayyana lamarin a matsayin "ƙiyamar tattalin arziƙi" ga Iran ya ce Amurka za ta katse duk wata alƙara tattalin arziƙi ta Iran, sannan ya ce duk wata ƙasa da ta yi hulɗa da Iran ita ma za a mayar da ita saniyar ware.
Sai dai ministan harkokin tattalin arziƙi na Iran Ali Madanizadeh ya ce Iran na da shirin daƙile raɗaɗin matakin na shekara biyu, kuma za a ƙara yin galaba kan Amurka.
Yaƙin ya haifar da tashin farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya. Kuma Iran ta sake yin barazanar ƙara ƙaimi wajen toshe fitar da ɗanyen man fetur daga yankin.
Haka nan Iran ɗin ta ƙara yin sabuwar barazana kan duk wani jirgin ruwan da ya so ratsawa ta Mashigar Hormuz ba tare da izininta ba.
Wane ne Benjamin Netanyahu?
Benjamin Netanyahu ya zamo shugaban ƙasa na huɗu wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta bayar da sammacin kamawa bisa zargin su da laifukan take haƙƙin bil'adama.
An haifi Benjamin Netanyahu ne a birnin Tel Aviv a shekarar 1949. A shekarar 1963 ce ƴan gidansu suka koma Amurka bayan mahaifinsa, Benzion, wanda fitaccen masanin tarihi ne kuma mai fafutikar kafa ƙasar Yahudawa zalla ya samu aikin koyarwa a can.
Yana ɗan shekara 18 ya koma Isra'ila, inda ya shiga aikin soja, ya yi shekara biyar, har ya kai muƙamin kyaftin a sashen yaƙin sunƙuru da ake kira Sayeret Matkal.
Yana cikin waɗanda suka ji rauni a wani hari da aka kai wa jirgin Belgium da wasu ƴanbindiga na Falasɗinawa suka yi, inda suka karkatar da jirgin sannan ya fafata a yaƙin gabas ta tsakiya na shekarar 1973.
A shekarar 1976, aka kashe ɗan'uwan Netanyahu, Jonathan a lokacin da yake jagorantar aikin ceto Isra'ilawa da suke cikin jirgin da aka karkatar zuwa Uganda. Kashe shi ya ɗaga martabar gidan su Netanyahu, domin sunansa ya yi amo a ƙasar baki ɗaya.
Netanyahu ya kafa cibiyar yaƙi da ta'addanci domin tunawa da ɗan'uwansa, sannan a shekarar 1982 ya zama mataimakin jakadan Isra'ila a Amurka.
Kwatsam sai Netanyahu ya zama fitacce a Isra'ila. Gwani ne wajen tsara magana da Ingilishi da irin harshen Amurka, inda ya zama fitacce a shirye-shirye talabijin na Amurka, kuma sanannen mai fafutikar kare Isra'ila.
An naɗa shi wakilin Isra'ila na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya a shekarar 1984.