Dakarun Amurka sun fara horas da na Najeriya a Bauchi
Dakarun Amurka sun fara horas da twakwarorinsu na Najeriya kan yadda ake sarrafa jirage marasa matuƙa da kuma kula da sojojin da suka samu rauni a lokacin yaƙi a wani ɓangare na alaƙar tsaro da ƙasashen biyu suka ƙulla.
A wani bayani da rundunar tsaron Amurka da ke da mazauni a Afirka ta wallafa a shafinta, Africom ta ce horon wanda ke gudana a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya na mayar da hankali ne wajen tabbatar da cewa dakarun Najeriya sun laƙanci kasancewa cikin yanayin ko-ta-kwana da kuma bunƙasa yadda suke aiki.
Rahoton na Africom ya ce horon ya mayar da hankali kan sarrafa jirage marasa matuƙa, sarrafa makamai, cire bama-bamai, kula da waɗanda suka ji rauni da kuma dabarun yaƙi ga ƙaramar tawagar soji.
"Amurka da Najeriya na gudanar da aikin bayar da horo a sansanin horon soji da ke a Bauchi, Najeriya, bisa manufar musayar ƙwarewa, ƙarfafa abokan hulɗa da kuma yauƙaƙa alaƙa tsakanin ɓangarorin biyu," a cewar bayanin.
Horon na zuwa ne bayan a watan Yuli Amurka ta sanar da janye akasarin dakarunta da ta tura Najeriya domin wani aikin yaƙi da ta'addanci na musamman, yayin da ƙasashen biyu suka ci gaba da shirinsu na musayar bayanan sirri da tsaro.
A ƙarshen shekarar 2025 ne ƙasashen biyu suka ƙulla wata alaƙa ta tsaro bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana gallaza wa Kiristoci a Najeriya tare da matsa wa hukumomin Najeriyar lamba kan su magance matsalar tsaro.