Ta yaya za a iya aiwatar da hukuncin ɗaurin shekara 75 kan Saleh Mamman?

...

Asalin hoton, Sale Mamman/X

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026 ne babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon ministan lantarki a Najeriya, Saleh Mamman shekara 75 a gidan yari kan almundahanar kuɗi fiye da naira biliyan 33.

Kotu ta ce ta samu Saleh da aikata laifuka 12 da hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa - EFCC - ta tuhume shi da su masu alaƙa da haɗa baki da almundahana.

To, sai dai kotun ta yanke wa Saleh hukunci ne a lokacin da ba ya nan kuma ba ya gaban kotu, lamarin da ya haifar da muhawara da tambayoyi kan ko me irin wannan hukuncin ke nufi, ta ya za a aiwatar da hukuncin kan mutumin da ba ya nan kuma idan bai dawo ba fa?

Dalilin haka ne BBC ta tuntuɓi wani lauya a Abuja, Abba Hikima Fage domin samun ƙarin haske kan wannan lamari.

Me irin wannan hukuncin ke nufi?

Lauyan ya bayyana wa BBC cewa yanke wa mutum hukunci ba ya nan ko ba ya gaban kotu na nufin kotu ta ci gaba da shari'a tare da yanke hukunci alhali wanda ake tuhuma bai halarci zaman kotun ba.

Abba Hikima ya ƙara da cewa: "A ka'ida, ba a yanke hukunci a shari'ar laifi sai mutum yana nan a gaban kotu tun daga gurfanar da shi zuwa duka wani abu da za a yi domin a tabbatar da adalci da damar kare kai," in ji lauyan.

Sai dai ya ƙara da cewa dokar na da wasu keɓaɓɓun yanayi inda ya ce; idan wani dalili ya zama wanda ake tuhuma ba ya nan, misali a ba mutum beli sai ya zama ya gudu ko kuma ba mamaki ya zama tun farko ma akwai umarnin a kamo mutum wato bai riga ya zo gaban kotu an gurfanar da shi ba, to kotu na iya ci gaba da shari'a har ta kai ga yanke hukunci ba tare da kasancewarsa ba."

Ta ya ya za a aiwatar da irin wannan hukunci?

....

Asalin hoton, Getty Images

A cewar lauyan, idan kotu ta yanke wa mutum hukunci alhali ba ya gabanta, hakan ba yana nufin an kawo ƙarshen batun ba ne ko kuma hukuncin ba zai yi aiki ba. Ya ce da zarar kotu ta gama shari'a tare da tabbatar da laifi, doka na bai wa hukumomin tsaro damar neman mutumin tare da kama shi duk inda aka gano shi domin aiwatar da hukuncin da aka yanke masa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lauyan ya bayyana cewa a shari'ar laifi, abin da ake hukuntawa shi ne mutum kansa, saboda haka idan wanda aka yanke wa hukunci ya gudu ko ya ɓuya, hukuncin zai ci gaba da kasancewa a kansa har zuwa lokacin da aka kama shi ko aka gan shi.

A cewarsa, "ko bayan shekaru masu yawa, idan aka gano inda mutumin yake, jami'an tsaro za su iya cafke shi sannan a kai shi gidan yari kai tsaye domin ya fara zaman hukuncin da kotu ta yanke."

Abba Hikima ya ce a wasu lokuta, kotu kan bayar da umarnin kama wanda ake tuhuma tun kafin a gama shari'a idan ya ƙi bayyana ko kuma aka yi zargin cewa ya tsere domin guje wa shari'a.

Ya kara da cewa doka ba ta yarda mutum ya tsallake hukunci kawai saboda ya daina zuwa kotu ba, saboda hakan zai iya zama hanyar da masu laifi za su riƙa amfani da ita wajen guje wa hukunci.

Saboda haka, idan aka kama wanda aka yanke wa hukunci lokacin da ba ya gaban kotu, ba sai an sake sabuwar shari'a ba, domin hukuncin ya riga ya tabbata tun farko, in ji lauyan.

Ya ce abin da ya rage kawai shi ne a aiwatar da abin da kotu ta umarta, ko zaman gidan yari ne ko kuma wani hukunci daban da aka ayyana a cikin hukuncin kotun.

Idan wanda aka yanke wa hukunci ba ya nan bai dawo ba fa?

Lauyan ya ce "Idan wanda aka yanke wa hukuncin da ba ya nan, bai dawo ba to ba yanda za a yi shi kenan maganar gaskiya amma sai dai komai tsawon shekaru, duk lokacin ya dawo ko aga gan shi za a iya kama shi kuma a aiwatar da wannan hukunci kamar yadda duka dokoki suke magana."

Ya kara da cewa dokar Najeriya ta bai wa jami'an tsaro damar ci gaba da neman wanda aka yanke wa hukunci, kuma duk lokacin da aka same shi, ko bayan shekaru masu yawa, ana iya kama shi domin ya fuskanci hukuncin da kotu ta riga ta yanke.

Abba Hikima ya ce wannan tsarin yana daga cikin hanyoyin da doka ke amfani da su wajen tabbatar da cewa babu wanda zai kauce wa hukunci ta hanyar guduwa ko ɓoyewa.

A cewarsa, muddin kotu ta yanke hukunci bisa ka'ida, zai ci gaba da aiki har sai an kama wanda ake nema kuma an aiwatar da abin da doka ta tanada a kansa.