Yadda iyaye ke sayar da yaransu domin samun abin ci a Afganistan

Abdul Rashid Azimi zaune da ƴaƴansa

Asalin hoton, Imogen Anderson/BBC

Bayanan hoto, Abdul Rashid Azimi ya ce a shirye yake ya sayar da ɗaya daga cikin yaransa mata domin ciyar da sauran iyalinsa
    • Marubuci, Yogita Limaye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, South Asia and Afghanistan correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Da asuba ta fara bayyana, ɗaruruwan maza na taruwa a wani fili mai ƙura a Chaghcharan, babban birnin lardin Ghor a Afghanistan.

Suna tsayawa a gefen hanya da gajiyayyun fuskoki, suna jiran ko wani zai zo yana neman ma'aikata domin aikin rana. Aikin ne zai tantance ko iyalansu za su samu abin da za su ci a wannan rana.

Sai dai damar samun aikin tana da ƙanƙanta sosai.

Juma Khan, mai shekaru 45, ya samu aiki kwana uku kacal cikin makonni shida da suka wuce, inda ake biyansa tsakanin kuɗin Afghani 150 zuwa 200 kimanin dala 2.35 zuwa dala 3.13 kenan a kowace rana.

"Ƴaƴana sun kwana da yunwa har na kwana uku a jere. Matata tana kuka, haka ma yara. Sai na je na roƙi makwabcina ya ba ni bashi domin in sayi garin fulawa," in ji shi.

"Ina rayuwa cikin tsoro cewa ƴaƴana za su iya mutuwa saboda yunwa."

Labarinsa ba shi da bambanci da na wasu da dama.

Gargaɗi: wannan rahoto na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali.

A halin yanzu a Afghanistan, kusan mutum uku cikin huɗu ba sa iya biyan buƙatunsu na yau da kullum, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya. Rashin aikin yi ya yi ƙamari sosai, tsarin kiwon lafiya ya taɓarɓare, sannan agajin da ake dogara da shi a baya ya ragu sosai fiye da yadda yake a da.

Bayanan bidiyo, Yogita Limaye ta BBC ta tattauna da wasu iyaye maza a Afghanistan da talauci ya tilasta musu yanke shawarar da ke da matuƙar wahala, inda suke fuskantar zaɓi tsakanin rayuwar iyalansu da rashin abin yi.

Ƙasar na fuskantar matakin yunwa mafi muni da aka taɓa gani, inda ake ƙiyasta cewa mutane miliyan 4.7 wato fiye da kashi ɗaya cikin goma na al'ummar Afghanistan suna dab da shiga matsananciyar yunwa.

Lardin Ghor na daga cikin wuraren da abin ya fi shafa sosai.

Maza a wannan yankin suna cikin wani hali na tsananin damuwa da rashin tabbas.

Rabani ya ce: "Na samu kira cewa 'ya'yana ba su ci abinci ba har kwana biyu." Muryarsa na rawa yayin da yake magana.

"Na sha tunanin kashe kaina. Amma sai na yi tunanin, ta yaya hakan zai taimaki iyalina? Don haka na zo nan ina neman aiki."

....

Asalin hoton, Imogen Anderson/BBC

Bayanan hoto, Juma Khan mai shekara 45, ya samu aikin kwana uku bayan shafa sati shida yana neman aiki
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafin Khwaja Ahmad ya kammala magana sai hawaye suka kwaranyo masa. Ya ce suna cikin matsananciyar yunwa, har wasu daga cikin manyan ƴaƴansa sun riga sun rasu. Yanzu kuma saboda tsufa, babu wanda yake son ba shi aiki duk da buƙatarsa ta neman abin ciyar da iyalinsa.

A lokacin da aka buɗe wani gidan burodi kusa da filin, mai gidan ya raba gurasar da ta rage ga jama'a. Nan take mutane suka ruɗe, kowa na ƙoƙarin samun ko da ɗan gutsure ne na burodin lamarin da ya haifar da turereniya.

Bayan mintuna kaɗan, wani mutum a babur ya zo neman ɗan aikin ɗaukar bulo. Nan da nan maza da dama suka yi masa kawanya, kowanne yana ƙoƙarin samun damar aikin. Cikin awanni biyu, mutane uku kacal suka samu aiki.

A kauyukan da ke kusa, inda gidaje ke warwatse a kan tsaunuka marasa ciyawa, talauci da rashin aikin ya addabe su.

Abdul Rashid Azimi ya kai mu gidansa, inda ya nuna mana 'yan tagwayensa 'yan shekara bakwai, Roqia da Rohila. Cikin kuka, ya bayyana irin wahalar da yake ciki, yana cewa "ina iya sayar da ƴaƴana mata saboda tsananin talauci da bashi."

Ya ce idan ya sayar da ɗaya, zai iya ciyar da sauran iyalinsa na tsawon shekaru huɗu. Duk da haka, ya rungumi ɗiyarsa yana kuka, yana nuna yadda zuciyarsa ke karyewa, amma yana ganin hakan ne kawai hanyar da ta rage masa.

...

Asalin hoton, Imogen Anderson/BBC

Bayanan hoto, Ma'aikata masu aikin hannu kan taru tun da sassafe domin neman ɗan aikin da zai samu.

Kayhan, mahaifiyar yaran, ta ce abin da suke ci kawai shi ne burodi da ruwan zafi, babu ma shayi ba.

A Afghanistan, iyaye kan fi yanke shawarar sayar da ƴaƴa mata maimakon maza saboda al'ada na kallon maza a matsayin waɗanda za su riƙa ciyar da iyali nan gaba. Hakan ya ƙara tsananta bayan dokokin Taliban da suka hana mata da ƴan mata ilimi da aiki.

Haka kuma akwai al'adar bayar da kuɗin aure daga ɓangaren ango zuwa iyayen amarya.

Wasu daga cikin 'ya'yan Abdul suna aikin goge takalma a gari, yayin da wani ke tara shara da mahaifiyarsu ke amfani da ita wajen girki.

Saeed Ahmad kuma ya ce talauci ya tilasta masa sayar da 'yarsa Shaiqa mai shekara biyar bayan ta kamu da cutar appendix da wata matsala a hanta. Ya ce bai da kuɗin jinyarta, don haka ya sayar da ita ga wani ɗan'uwansa.

An yi wa Shaiqa tiyata cikin nasara ta hanyar kuɗin da aka biya saboda yarjejeniyar aurenta. Sai dai Saeed ya ce ya amshi wani ɓangare ne kawai na kuɗin yanzu, yayin da aka shirya cewa bayan shekara biyar za a kai yarinyar gidan mutumin domin ta auri ɗansa.

Duk da cewa Shaiqa tana da matuƙar kusanci da mahaifinta, ana sa ran za ta bar gidansu tana da shekara 10 kacal. Saeed ya ce in da yana da hali, da bai taɓa tunanin ɗaukar irin wannan mataki ba, amma ya ji aƙalla hakan zai ceci rayuwarta.

Auren yara ƙanana dai na ci gaba da yawaita a Afghanistan, musamman bayan hana 'yan mata zuwa makaranta da gwamnatin Taliban ta yi.

Saeed Ahmad szaune da ƴaƴansa

Asalin hoton, Imogen Anderson/BBC

Bayanan hoto, Saeed Ahmad ya ce ya sayar da ƴar sa Shaiqa ƴar shekara biyar.

Shekaru biyu da suka gabata, Saeed da iyalinsa suna samun tallafin abinci kamar yadda miliyoyin 'yan Afghanistan ke samu. Ana ba su garin fulawa da man girki da wake da kayan ƙarin gina jiki ga yara.

Sai dai rage tallafin ƙasashen duniya cikin 'yan shekarun nan ya jefa mutane da dama cikin matsanancin hali. Amurka, wadda ta kasance babbar mai bai wa Afghanistan tallafi, ta rage kusan dukkan taimakonta a bara. Sauran ƙasashe masu bayar da tallafi, har da Birtaniya, sun rage gudummawarsu. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tallafin da aka samu a bana ya ragu da kashi 70 cikin ɗari idan aka kwatanta da 2025.

Haka kuma fari mai tsanani da ya shafi fiye da rabin lardunan ƙasar na ƙara jefa mutane cikin wahala. Wani mazaunin ƙauyen mai suna Abdul Malik ya ce ba gwamnati ko ƙungiyoyin agaji da suka taimaka musu.

Gwamnatin Taliban ta ɗora alhakin matsalolin kan tsohuwar gwamnatin Afghanistan da kuma shekarun yaƙi, tana cewa tattalin arzikin ƙasar ya ta'allaka ne kan kuɗaɗen da ƙasashen waje ke shigowa da su. Sai dai wasu na ganin dokokin Taliban, musamman hana mata ilimi da aiki, suna daga cikin dalilan da suka sa masu bayar da tallafi suka ja baya. Taliban kuwa ta ce bai kamata a siyasantar da agajin jin ƙai ba.

A yayin da Taliban ke magana kan shirye-shiryen samar da ayyuka da rage talauci ta hanyar manyan ayyukan tattalin arziki, miliyoyin mutane na buƙatar taimakon gaggawa domin rayuwa.

Mohammad Hashem ya ce jaririyarsa ƴar wata 14 ta mutu saboda yunwa da rashin magani. Wani dattijo a yankin ya ce mutuwar yara, musamman saboda rashin abinci mai gina jiki, ta ƙaru sosai cikin shekaru biyu da suka gabata.

A yankin babu cikakken rajistar mace-mace, amma maƙabarta ce kaɗai ke nuna yadda mutuwar yara ta ƙaru. An lura cewa ƙananan kaburbura na yara sun ninka kaburburan manya kusan sau biyu.

...

Asalin hoton, Imogen Anderson/BBC

Bayanan hoto, An haifi tagwayen kafin su kai watan haihuwa, bakwaini kuma suna fuskantar ƙalubale wajen numfashi

A babban asibitin lardin Chaghcharan, sashen kula da jarirai ne ya fi cunkoso. Duk gadaje sun cika, wasu ma ana kwantar da jarirai biyu a gado ɗaya. Yawancinsu ba su da nauyin da ya dace kuma suna fama da wahalar numfashi.

An kawo wasu 'yan tagwaye mata da aka haifa watanni biyu kafin lokaci. Ɗaya tana da kilo 2, ɗayar kuma kilo 1 kacal. Nan take aka saka musu iskar oxygen saboda halin da suke ciki ya yi tsanani.

Kakar jariran ta ce mahaifiyarsu Shakila ba ta samun isasshen abinci yayin cikin, sai burodi da shayi kawai. Bayan 'yan sa'o'i kaɗan da barin asibitin, ɗaya daga cikin jariran ta rasu kafin ma a sa mata suna. Kakarsu ta ce ta naɗe gawarta ta kai gida, kuma mahaifiyar ta suma da jin labarin mutuwar jaririyar. Yanzu suna addu'ar ɗayar ta tsira.

....

Asalin hoton, Imogen Anderson/BBC

Bayanan hoto, Ma'aikaciyar jinya Fatima Husseini ta ce mutuwar ta fara zama tamkar abu na yau da kullum a gare su.

Ma'aikaciyar jinya Fatima Husseini ta ce akwai ranakun da jarirai uku kan mutu a rana guda saboda tsananin rashin lafiya da talauci. Ta ce da farko mutuwar yara tana damunta sosai, amma yanzu ta fara zama tamkar abu na yau da kullum a gare su.

Likitan sashen kula da jarirai, Dr Muhammad Mosa Oldat, ya ce yawan mutuwar jarirai ya kai kusan kashi 10 cikin 100, kuma hakan ba abu ne mai kyau ba. Ya bayyana cewa talauci da rashin kayan aiki na ƙara jefa jariran cikin haɗari.

A wani sashe kuma, wani jariri mai suna Zameer na fama da cutar sanƙarau da ciwon huhu, amma asibitin ba shi da kayan aikin da ake bukata domin duba lafiyarsa yadda ya kamata. Haka kuma yawancin marasa lafiya sai sun sayi magunguna da kansu daga wajen asibiti.

Saboda rashin kuɗi, iyalai da dama suna ɗaukar marasa lafiya zuwa gida tun kafin su warke. Haka aka yi wa jaririyar Gulbadan da kuma Zameer, inda iyalansu suka ɗauke su zuwa gida saboda sun kasa biyan kuɗin jinya, duk da cewa har yanzu suna buƙatar kulawa sosai.