Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙungiyoyin Turai 4 da suka lashe kofunan gasannin ƙasashensu
Fitattun ƴan Najeriya da masoya ƙwallon a ƙasar na ci gaba da taya ɗan wasan ƙasar, Victor Osimhen murnar jagorantar ƙungiyarsa ta Galatasaray S.K. wajen lashe kofin gasar Turkiyya.
Cikin wani saƙo da tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar, Peter Obi ya wallafa a shafinsa na X, ya taya Osimhen murlar lashe babbar gasar tamaula ta Turkiyya, bayan da ya ci ƙwallo biyu a wasan da ya bai wa ƙungiyar nasara.
''Jajircewarka da ƙoƙari da ƙwazon da kake nunawa na ci gaba da burge miliyoyin matasan Najeriya, wadnada suka yi imanin cewa aiki tuƙuru da sadaukarwa na haifar da sakamako mai kyau'', a cewar Peter Obi.
Ƙungiyar ta samu nasarar lashe kofin gasar ta bana ne yayin da ya rage sauran wasa guda a kammala gasar ta bana.
A wannan muƙala mun duba ƙungiyoyin Turai huɗu da suka lashe kofunan gasar bana, duk da rashin kammala kakar wasannin.
Barcelona
A daren jiya ne ƙungiyar Barcelona ta lashe kofin Gasar La Liga ta ƙasar Sifaniya.
Barcelona ta samu nasarar ɗaukar kofin ne a wasan hamayyar El Clasico da Real Madrid a filin wasa na Camp Nou, inda ta yi nasara ta ci 2-0.
Ƙungiyar ta ɗauki kofin ne yayin da ya rage saura wasa huɗu a kammala gasar ta bana.
Yanzu haka ƙungiyar ce ta ɗaya a kan teburin gasar da maki 95 bayan wasa, kuma ta bai wa Madrid ta biyu tazarar maki 14, yayin da ya rage wasa uku a kammala gasar ta bana.
Barcelonan ce dai ke riƙe da kofin gasar, da ta ɗauka a shekarar da ta gabata.
Bayern Munich
Tun a ranar 19 ga watan Afrilun da ya gabata ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga na bana.
Ƙungiyar ta samu nasarar lashe kofi karo na 35 kuma na 13 cikin kaka 14 a wasan da ta doke Stuttgart da ci 4-2.
Bayern ta ɗauke kofin gasar ta bana ne da tazarar maki 16 tsakaninta da Borussia Dortmund ta biyu.
Zakarun na Jamus sun ɗauki kofin ne yayin da ya rage wasa huɗu a kammala gasar.
Inter Milan
A ranar 3 ga watan Amyun da muke ciki ne ƙungiyar Inter Milan ta samu nasarar ɗaukar kofin gasar Seria A ta bana.
Ƙungiyar ta dauki kofin ne bayan doke ƙungiyar Parma da ci 2 -0.
Inter Milan ta lashe gasar ne yayin da ya rage wasa uku a kammala gasar, inda yanzu haka ta bai wa Napoli ta biyu tazarar maki 15 a kan teburin gasar.
Saura dai wasa biyu a ƙarƙare gasar ta bana.
Galatasaray S.K.
A ranar Lahadi ne Galatasaray S.K. ta samu nasarar lashe kofin babbar gasar Turkiyya bayan doke Antalyaspor da ci 4-2.
Wannan ne karo na 26 ga ƙungiyar ke lashe babbar gasar tamaula ta Turkiyya.
Galatasaray S.K. ta yi bajintar ne yayain d aya rage wasa ɗaya a kammala gasar, inda ta bai wa Fenerbahçe SK ta biyu tazarar maki huɗu.
Ya batun Gasar Premier?
Gasar Premier Ingila ta kasance ɗaya daga cikin gasannin da har yanzu ba atantance wanda zai ɗauka ba.
Yanzu haka dai Arsenal na kan teburi da maki 79 bayan wasa 36, yayin da Manchester City ke biye da ita da maki 74 bayana wasa 35.
Idan kuma aka tafi a haka dole sai a ranar ƙarshe na gasar za a iya tantancewa wanda zai lashe gasar ta bana.
Sai dai tuni aka samu ƙungiyoyi biyu da suka fice daga gasar, wato Wolverhampton Wanderers da kuma Burnley, yayin da West Ham United da Tottenham ke fafutikar faɗuwa daga gasar.