Yadda masu iƙirarin jihadi suka toshe hanyoyin shiga Bamako

Wani mai mashin yana wucewa.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Mali sun ɗauki sama da shekara 10 suna yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi
    • Marubuci, Nicolas Négoce
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Bamako babban birnin Mali - fitaccen birni a Afrika ta Yamma kuma gida ga mutum sama da miliyan uku - wani ɓangarensa na cikin kullen mayaƙa masu iƙirarin jihadi, kwanaki kaɗan bayan kisan gillar da aka yi wa ministan tsaron ƙasar.

"Sojojin mu ba su da ƙarfin kare mu, ta yaya za mu koma gidajen mu?" kamar yadda wata uwa mai ƴaƴa biyu ta faɗa wa BBC, bayan kasa samun damar sake shiga Bamako bayan kai wa iyayenta ziyara a wajen gari.

Ita tare da wasu da dama sun maƙale kan babban hanyar Bamako zuwa Kéniéba, da ke wajen birnin na tsawon aƙalla kwana guda.

Hakan ya biyo bayan gargaɗin da mayaƙa daga ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) suka yi cewa "babu wanda za a sake bari ya shiga birnin".

A bara, ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun kakaba dokar hana shigar da fetur cikin birnin, abin da ya janyo ƙarancin mai da kuma ƙaruwar farashi, sai dai a yanzu sun ayyana kulle baki-ɗaya, lamarin da ya jefa mazauna birnin cikin fargaba.

Shaidu sun faɗa wa BBC cewa aƙalla uku daga cikin hanyoyi shida na shiga birnin sun kasance a ƙulle na tsawon sa'o'i kafin mayaƙan su tafi zuwa wani wuri na daban.

Bayan tafiyarsu, wasu ababen hawa sun samu nasarar shiga birnin da kyar.

An samu gagarumin hari a faɗin ƙasar a makon da ya gabata wanda ƙawayen masu iƙirarin jihadi da wani ɓangare na ƴan tawaye suka jagoranci kai wa a arewacin ƙasar - wato Azawad Liberation Front (FLA) - inda suke da niyyar kifar da gwamnatin Janar Assimi Goïta, wanda ya ƙwace iko a wani juyin mulki a 2020.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An kashe ministan tsaron ƙaar lokacin kai harin, bayan da wata mota ɗauke da bam ta tashi a gidansa da ke Bamako.

An binne shi ranar Alhamis cikin tsauraran tsaro a gaban dubban jama'a, ciki har Goïta, kamar yadda AFP suka ruwaito.

Dakarun Mali sun kasance suna aiki da sojojin karta kwana na Rasha, wato Africa Corps waɗanda suka fito daga cikin ƙungiyar Wagner, wajen yaƙar masu jihadi.

A lokacin kai harin, an tilasta wa dakarun Rashar janye wa daga arewacin birnin Kidal, wanda yanzu ke karkashin ikon ƴan tawayen FLA.

Ƴan tawayen yanzu sun ce za su shiga sauran birane da ke arewacin ƙasar kuma sun buƙaci Africa Corps su janye daga ƙasar baki ɗaya.

Wani mai magana da yawun fadar Kremlin, ya bayyana ranar Alhamis cewa dakarun Rasha za su ci gaba da zama a Mali "don daƙile tsattsaurar ra'ayi, ta'addanci da sauran abubuwa masu lahani kuma za su gaba da taimaka wa gwamnatin da ke mulki".

Wani direban babbar mota da ke koƙarin kai wa Bamako ya faɗa wa BBC cewa: "Ban taɓa ganin abu irin haka ba.

Na ɗauki tsawon shekaru ina aikin tuki.

"Na maƙale a nan kuma hakan yana da hatsari. Na gwammace in bar wajen don tsira da rayuwata maimakon faɗa kan kayan da zan kai. Ban taba tsammanin haka ba."

An kakaba ƙulle na baki ɗaya kan garin Ségou, mai kilomita kasa da 80 daga babban birnin ƙasar, abin da ya jawo tsayawar ababen hawa da dama, ciki har da manyan motoci, bas-bas da kuma ƙananan motoci.

Fasinjoji, ciki har da iyalai da ƴan kasuwa sun maƙale na tsawon kwanaki a can, inda suke wahalar samun ruwa da abinci, a cewar wani ɗanjarida a garin.

Shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Goïtaya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri kan masu ta da ƙayar-bayan, bayan wani taron gaggawa na tsaro da ya kira ranar Laraba, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.

Goïta ya kuma yi iƙirarin cewa sojoji da jami'an tsaro sun samu nasarar kashe ƴan tawaye da dama.

Taswirar Mali.

‎Alain Antil, darektan wata cibiya, ya faɗa wa BBC cewa "abin da ya faru ya nuna gwamnatin na da rauni kuma ba za ta iya dawo da tsaro ba.

Bayan wata haɗakar masu jihadi da ƴan awaren kabilar Tuareg sun shiga birnin Bamako a 2013, dakarun Faransa, haɗe da wasu daga sauran ƙasashen Afrika, sun shiga tsakani don kare babban birnin ƙasar.

Sun samu nasarar mayar da ƴan ta da ƙayar-baya, sai dai sun ci gaba da kai hare-hare kuma ƙasar ta kasance cikin rashin tabbas. Bayan ƙwace iko, Goïta ya kori Faransa daga ƙasar inda ya koma ga Rasha don neman taimako sai dai lamarin bai sauya ba, har zuwa hare-hare masu muni da aka kai karshen makon jiya.

Ƙasashe da dama - ciki har da Faransa, Canada da kuma Birtaniya - sun buƙaci ƴan ƙasashensu da su fice daga Mali, yayin da Amurka ta buƙaci nata mutanen su zauna a gida.

"Babu inda zan je," kamar yadda wata ƴar Faransa ta shaida wa BBC, "Ina son Mali".

"Ta zama jikina tun da na zo nan tun 2002. Za mu zauna da iyalina. Mun san cewa abubuwa za su yi sauki."